← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 211

Sashe 90

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata samu damar kammala gyaran gidan ba har sai kusan sallar Maghrib saboda ba laifi gidan nada 'dan girma sosai, amma sosai tayi 'ko'kari cuz cikin lokaci 'kan'kani gidan ya dawo fes da shi yana walwali tamkar ba shi ne yayi futu-futu 'dazun ba...harda burner ta kunna a palourn ta saka musu turare mai da'din 'kamshi saboda kawai ta sanyaya ransa, cuz ta san shi da son 'kamshi.

Shi kam tun da ya fita sallar Maghrib bai dawo ba har sai da akayi sallar Isha'i sannan ya dawo gidan da ledan take-away da ya musu a hannun sa.

Husnah hutun Sallah take yi dan haka a palour ya same ta kishingi'de tana amsa waya daga mahaifiyar ta.

Ledan ya ajiye tare da zama facing da inda take ya tsura mata idanu yana jiran ta kammala wayar ji yake tamkar yaje ya rungumeta ya bayyana mara irin kewar ta da yayi.

Amma deep down his heart yake tsana ta na taso masa ka'dan, maganar aure ka'dai da akace mahaifin sa na shirin yi masa ya sanya tsanar yin tsiri cikin zuciyar sa inaga kuma ance auren akayi gaba 'daya..kunga ai sai cin mutunci da hantara ne zai biyo baya ko.
_'Kalubalen mu 'yaya mata, darajar ki, itace kimar ki, mutuncin ki, gadarar ki, alfaharin ki, har ma da kwanciyar hankalin ki a ko ina, mu daure mu kula da kare mutuncin mu ko dan gudun abinda kan iya zuwa ya dawo, babban ma shine tsoron Allah...Ubangiji Allah ka 'kara tsare mana kawunan mu ka raba mu da sharrin masu sharri...AM33N._

Ai kuwa tana gama amsa wayar ta juyo gare shi tana murmushi tace" Ka dawo?"
Da" Umm" kawai ya amsa ta a takaice tare da 'dago ledan da ya shigo da shi ya ciri abinda yaga zai iya ci sannan ya tura mata sauran batare da ya furta mata komai ba.

Shima 'din yunwa yake ji sosai shiyasa bai ko saurari Husnah sun ci tare ba kamar yanda suka saba kawai ya fara aikawa cikin hanjin sa.

Murmushi Husnah tayi tana kallon sa tace" ba zaka jira ko plate na 'dauko maka ba yau 'din?"

" Barshi kawai".
Yace bayan ya taune chips 'din dake bakin sa.

Husnah murmushi tayi tare da mi'kewa ta je ta 'dakko plate ta zuba iya abinda zata iya ci ta koma gefe ta fara ci, shiru 'dakin ya 'dauka kowa na cin abincin sa jifa-jifa ta kan 'dan saci kallon sa yayin da shi kuwa baya ko kallon inda take tamkar ma ya manta da kasancewar ta cikin 'dakin illah Television da yake kallo lokaci zuwa lokaci a haka har suka 'kare cin abincin baki 'daya.

Husnah ce ta ta shi ta tattare komai harda wanda yayi amfani da shi duk ta fitar zuwa kitchen sannan ta dawo palourn, sai dai bata zauna ba kawai ta tunkari 'kofar da zai sada ta da 'dakin ta tana mai shafo kyawawan siraran kitson da ke kwance a fatar kanta.

Daf da zata shige taji muryar sa ya 'kira sunan ta" Husnah"! Cikin dakiya da mugun hali.

Waigowa tayi batare da ta yi niyyar tahowa ba cuz zuwa lokacin 'dan iskan banzan halin nasa ya fara isanta itama, ganin babu wani abinda ya ha'da su amma sai faman share ta yake yi, tun zuwan ta gidan zuwa yanzu in bata manta ba bai fi sau biyu kacal magana ta shiga tsakanin su ba.

Ganin ta tsaya batare da ta taho zuwa inda yake ba ya sanya shi ha'de gira yana sake fa'din" Magana nake so muyi please".

Baki ta ta6e sannan ta taho a hankali ta zauna kan kujerar da ke nesa ka'dan da shi.

Sai da ya saki numfashi kafin ya ha'de hannayen sa wuri guda yana duban ta yace" Husnah me kika ji yake shirin faruwa tsakani na da ke?"

Da mamaki tace da shi" Ni kuma me zanji Mu'een babu abinda naji ni"
Tayi maganar tana kallon fuskar sa.

Sai ya 'dage gira 'daya tare da zuba mata idanu a hankali ya furta" Mahaifina ya san ala'kar da ke tsakani na dake, akanki Husnah har mari mahaifina yai min da tun haihuwa ta har girma na hakan bai ta6a faruwa tsakani na da shi ba..kin san kenan ransa ya 6aci sosai kenan ko?"
Ya 'karashe yana duban ta sannan ya koma ya zauna da kyau still yana kallon ta da itama 'din shi take kallo...Cigaba yayi da fa'din" Ina jin tsoron hukuncin da zai yanke akan hakan ne shiyasa nake tamabayar ki".

Husnah sai tace" Babu komai, ni banji komai ba gaskiya".
Yace" Kin tabbatar ko Husnah?"
" Me yasa kake tunanin zan maka 'karya to".
"Hmm"
ya saki ajiyar zuciya afili yana jin 'dan natsuwa ka'dan na shigan sa.
Baya ya koma ya jinginu sosai da jikin kujerar yana lumshe idanu.

" To ni ka 'daure min kai sam ban fahimci inda maganar taka ta dosa ba, me kake nufi da wannan tambayar? Me yasa kake tunanin hukuncin da za'ayi maka zai shafe bacin ko sani na bai yi ba ni".

Idanun sa a lumshe yana shafa saman 'kirjin sa da left hand 'din sa ya bata amsa da fa'din
" Bazaki gane bane Husnah abar zancen kawai...fata na dai kawai shine Allah yasa abinda kika fa'da min ya zam iya gaskiyar kenan, kuma ya sanya iyakar abinda zai iya faruwa tsakani na dake ya kasance iya nan...."

Husnah kam ido kawai ta tsura masa cike da matu'kar mamakin kalaman nasa, sosai ya 'daure mata kai ya sa ta cikin tunanin manufar hakan da ya furta mata.

Yayin da cikin ransa yake ayyana cewa matu'kar Husnah tayi kuskuren da har ta bari aure ya kasance tsakanin sa da ita..." Hmm"
Kawai ya furta illah bayyana murmushin sa da yayi a fili still idanun sa a rufe.

Husnah kam zuciyar ta cike fal da tunani ta tashi ta shige 'dakin da ya kasance mallakin ta ne a gidan, sosai take so ta san me maganganun nasa ke nufi amma sanin da tayi cewa matu'kar ba ra'ayin kansa yayi ba to ko hauka zata yi bazata ta6a jin yanda take so daga bakin sa ba.

Ranar haka kowa ya kwana 6angaren sa babu wanda ya nemi 'dan uwan sa, Husnah kam 'kullin dake cikin maganar sa ne ya dame zuciyar ta..kwana tayi tana tunanin tambayar da yayi mata, to me yake tunanin zai faru tsakani na da shi wanda yake tsammanin zan ji shi a gidan mu?
Tambayar da take yawan yiwa kanta kenan abin ya dame ta sosai har hakan yasa ta 'kagara gari ya waye ta 'kira mahaifiyar ta taji, tsoron ta kar dai ahalin ta sun san da batun 'kazamar tarayyar da ke tsakanin ta da shine suke ganin ta da abin kawai...yayin da Yah Deen yayi baccin sa cikin kwanciyar hankali jin cewa babu wani labari daga 6angaren Husnah.

Gari na wayewa da yake ba sallah zata yi ba, tana watsowa jikin ta ruwa ko gama kimtsawa bata bari tayi ba kawai ta rarumo wayar ta, sosai ta 'kagara taji abinda ke faruwa cuz ba 'karamin duhu Mu'een ya shimfi'da cikin tunanin ta ba.

" Hello Mummy"!
Husnah ta fa'di jin an 'daga wayar da ta 'kira 'din.
" Haba Husnah...sau nawa wai zan miki kashedi akan wannan Hello 'din da kike yi a waya, sallamar ce da wahala ko kuwa menene?"
Mahaifiyar Husnah ce ta furta hakan tana mai jin 'daci har cikin ranta na rashin jin maganar ta da Husnah bata yi.

" Sorry Mummy na daina...Fatan an tashi lafiya?"
Husnah ta fa'di tana mai zama bakin gadon ta yayin da ta folding left hand 'din ta a 'kirjin ta tana mai cigaba da sauraran wayar tare da bada dukkan hankalin ta akai.

Mahaifiyar ta sai tace" Lafiya lau Alhamdulillah...ya makarantar?"

" Qalau Mummy gamu nan duk ma ba'a dawo sosai ba ba wani da'di school 'din".

Tayi maganar tana wani yatsina fuska kamar gaske.

Mummyn sai tace" Zasu dawo ai ba abin damuwa bane may be ma duk yau ku gansu".
" Hakane Mummy".
Husnah tace tana 'dan sosa tsakankanin kitson dake kanta.
Bu'dan baki tayi kamar zata fa'di abinda ke cikin ranta
"..umm Mummy"
Sai kuma tayi shiru.
Da kulawa Mummyn tace" Me ke faruwa ne Husnah sanar da ni mana".

Sai da ta sanya dauriya cikin maganar ta kafin ta iya furta" Mummy dama tambayar ki zanyi"
" Ina jinki, me yafaru?"
" Mummy akwai abinda ya faru ne bayan tahowa ta?"
" Wani abu kamar me kenan?"
" Wai nace ko kinji wani abin, amma shikenan kawai ya wuce".

A masifance Mummyn Husnah tace" Kamar ya shikenan ya wuce, ni 'din sa'ar ki ce ko kuwa 'kawar ki ce da zaki sa ni gaba da guntayen magana ko kuwa tsabar kin raina ni?"

Cikin shagwa6a tace
" Afuwan..ba haka bane fa Mummy, dama nayi tunanin ko kin sami labari ne amma shikenan ya wuce".

" Husnah...ban son iskanci fa..."
Saurin taran ta tayi da fa'din" Allah Mummy ba komai in akwai ai kin san zan sanar dake".

" Kin tabbatar?"
" Erh Mummy"
" To shikenan ayi karatu banda wasa ko".
" Uhmm".
Daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar.

Sai dai wannan wayar da Husnah ta 'kira 'din sosai ya 'daga hankalin mahaifiyar ta, tayi saurin nuna mata ta saki ranta ne dan tana so ta binciko dalilin da yasa Husnah yi mata wannan tambayar.

Yayin da 6angaren Husnah abin ya sake 'daure mata kai, ta tabbata kalaman da Mu'een yai mata jiyan nan da akwai dalilin yin su, sai dai kuma tana tunanin maganar daga 6angaren sa ta taso bai shafe ta ba....to ko dalilin kenan da yasa shi 'dauke min wuta tun isowa ta garib nan?"
Ta tambayi kanta, take kuma ta bawa kanta tabbacin erh hakan ne ma.

To in kuwa hakane ya zam dole ta nemo dalilin daga wajen sa, batare da 6ata lokaci ba ta ci alwashin hakan cikin zuciyar ta...dole ne tasan abinda yake 'ko'karin 6oye mata.

Sai dai ga mamakin ta tun a safiyar ranar Mu'een ya dawo mata a yanda ta saba ganin sa, wannan ba'kin halin duk ya kau, yazo mata ne a asalin masoyin ta Mu'inuddeen.
Chapter 90 · 0% Book details