Sashe 177
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanu Ammi ta lumshe cike da 'dacin zuciya, sosai take son Mu'een take ji da shi, take kuma 'kaunar ganin farin cikin sa akoda yaushe har a zuciyan ta take jin da'di a duk lokacin da ta fahimci yana tare da walwala, amma babu yadda zata yi halayyar sa yasa dole ne tayi abinda ya dace da shi ko da hakan na nufin tashin hankalin sa ne, ko tilasta shi ne dole tayi ko dan gudun 'daukan alhaki ma.
Fes ta bu'de idanun ta akansa suka ha'da idanu a hankali cikin muryar natsuwa tace da shi"...Ina fatan da kanka ka shiryawa wannan ranar Mu'een? hope ka riga kasan mai zai biyo bayan cin amanar da ka jima kana yi mana...?"
Kallon Ammi yayi kawai yana mai jin nauyin abubuwan da suka ta yaudaran sa wurin mata har ya kasa tsaida hankalin sa wuri guda, ya kasa tsaida zuciyar sa da gangan jikin sa wurin matar da Allah da kansa ya za6a masa isa batare da wayo ko dabarar sa ba, sai dai har yanzu bai fahimci me Ammi take nufi da dam'ka masa littafi da al'kalami ba, bai san me zai yi da su ba sam.
Sannan shi bai shiryawa faruwar komai ba hasali ma shi bai ta6a kawo faruwar wani abu makamancin hakan da ya riga ya faru cikin ahalin sa ba...sai dai maganganun Ammi sun masa karan tsaye, sosai hankalin sa ya kasu kashi-kashi ya shiga nemo ma'anar su, kuma har lokacin batun saki sam bai zo kansa ba...illah zuciyar sa dake faman lugude na tashin hankali.
Yanzu kam bai ga wani alamar sulhu da yake tunanin Ammi zata yi tsakanin sa da Noor ba...
A hankali ya sau'ke idanun sa kan littafin dake ri'ke a hannun sa yayin da Ammi ta cigaba da fa'din"...'Kauna da mutuntaka yasa aka 'dauki auren Hudah aka baka kasani Mu'een ba wai dan ka isa ba, amma kayi watsi da komai, ka bi son zuciyar ka baka damu da halin da na kusa da kai zai iya tsintan kansa ciki saboda damuwar ka ba, musamman ma iyalin ka, bansani ba ko dan kana ganin baka sha wahala kafin ka same ta bane shiyasa oho..cuz na tabbata da da kanka ka nemi auren ta bazaka dinga yi mata hakan ba, if zan tuna lokacin da ka fara jin.soyayyar Amina a zuciayr ka a lokacin kusan zaucewa kayi, ba mamaki da itama Noor in ka wahala wajen neman auren ta da bazaka yi mata irin wannan cin zarafin ba...sai dai ka sani idan baka son ta ni ina son kaya na, Mahaifiyar ta da dangin ta duk na son ta ba zai yiwu mu zuba maka idanu kana azabtar mana da zuciyar ta ba while tana da gatan ta, dubi yanda duk ta lalace kuma na tabbata duk damuwar ka ce ba komai ba, ni kaina nasan yarinyar nan tayi ha'kuri da kai matu'ka, tunda kuwa har aka zo wannan gandun nasani mai iya zama da kai sai yayi ha'kurin ya kai a buga misali da shi, a kulumm idan na tambayi yarinyar nuna min take babu matsalar komqi duk wai dan ta rufa maka asiri, ba'kin halin ka da rashin wayo bai sa ka fahimci rashin walwala da yarinyar nan ke ciki ba saboda ka 'dauki hankalin ka gaba 'daya ka dam'ka a hannun matan banza, da aure ka ce zaka yi Mu'een wallahi ko ni bazan hana ka ba, amma madadin.hakan bige da biye-biyen mata sai kace wani.bunsuru, kai ko.kunyar Allah ma baka ji? yarinyar nan koda wasa bata ta6a kawo min 'karar ka ba bata ta6a nuna min ko alama cewa bata jin da'din zama da kai ba, ta rufa maka asiri Mu'een wanda ko mu iyayen ka da muka haife ka iya ka rufin asirin da zamu iya yi maka kenan a wannan duniyan, amma duk ka san hakan ka kuma yi watsi da shi ka cigaba da cutar da ita saboda son zuciyar ka.
Bazan hanaka ba, rayuwar ka ce, iya ka ta da kai a kullum in nuna maka cewa sa6on Allah kake yi ba bakomai ba, sai dai ko yanzun nasan ka fahimci cewa ba'a aikata Zina ya kuma tafi abanza, kayi ne kaina ka jira ranar faruwan naka..ai kaga misali 'daya, idan kuwa kace ba zaka bar 6ata yaran mutane ba haka kaina.zaka yi ta haifa ana lalatawa...".
Da sauri ya 'dago ya dubi Ammi zuciyar sa cike da rauni...a ganin sa bai kamata Ammi ta fa'di hakan ba saboda ita Uwa ce agare shi...me yasa bazata banbance tuban sa na da da na yanzu ba, ji yake da ana iya bu'de zuciya da ya bu'de mysu yanda yake game da rayuwar sa na baya, sosai yayi nadama ta gaskiya baya jin akwai ranar da zai sake komawa wancan rayuwar har abada..yana cikin tunanin ya fara jin hawaye na tauruwa masa kuma still bai daina kallon Ammi..gani yake kamar zata iya karantar zuciyar sa a fuskar sa.
Idanun su sar'ke da juna Ammi ta cigaba da fa'din" Yes..i mean it..fa'dar Allah ce ba ni ba, kuma ko yanzun sai dai ince Alhamdulillah cuz i know zuwa yanzun da kanka kasani ba sai an sake maimaita maka ba, in da akwai dattako ma kai ne ya kamata ka zaunar da mutane kana yi musu nasiha akan irin hakan amma tunda ka za6i rayuwar jind'adi fiye da tsoron Allahn ka shikenan, kaje kayi tayi, ni nasan akwai ranar nadama tana tafe, domin ina da ya'kinin cewa har yanzun baka 'dauki darasi cikin abubuwan da suka faru ba, yau gashi kana ji kana gani babu Baby ta koma ga Ubangijin ta inda ta tafi da mummunan tabon da halayyar ka ya ja mata...akan hakan ka'dai ma bana jin har abada zan iya yafe maka Mu'een sam naji ka fice min arai na...nd bazan iya barin yarinya ta ta mutu da ciwon zuciya ta sanadin ka ba...ha'kurin ta ya riga ya kai ma'kura ta yanda ko ita da kanta ta nemi sake zama da kai ma bazan amince ba bazan barta tana gida zaman bautar aure kaje can gantalin ka ka kwaso mata wata cutar ba....i just want u to open this book now ka rubuta min sakin 'ya ta...".
Wani ras yaji a dukkan ilahirin jikin sa ya amsa, lumshe idanu yayi da 'karfi hawayen sa suka gangaro a fili ya furta Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un... tunda Ammi ta fara magana sai yanzun hawayen sa ya gangaro.
Idanun sa ya bu'de ya zuba akan fuskar Ammi suka ha'da idanu...wanda ganin hawayen nasan bai sa ta fasa niyyar ta ba sai ma cigaba da tayi da fa'din" Ka sakar min.'yata sai ka je kayi ta jin da'din.rayuwar ka kai ka'dai, duk ranar ka tabbatar nadama ta shige ta gaskiya sai ka zo ka tabbatar min in gani.may be a lokacin zan iya yafe maka...but for now banda case da kai da kai bama na jin ka matsayin 'dan da ni na haifa..."
Zaro idanun sa yayi da kayu yana duban Ammi, harshen sa yaji yayi masa nauyi sosai, wai shi Ammi ke wa irirn wa'dannan mugun kalaman?
Ga Noor ya maida kallon sa sai yaga kanta ma kife yake kan cinyoyin ta kuka take yi sosai har da sheshshe'ka....
Yun'kuri yayi da niyyan tashi ya isa gare ta sai Ammi ta dakatar da shi a tsawace.
Kallon fuskar ta yayi yana girgiza kansa wasu siraran hawaye na bin kuncin sa yayin da hannun sa 'daya ke dafe kan 'kirjin sa da yake jin tamkar zuciyar san fa'dowa zata yi bisa hannun sa.
Bai san me ze ce da Ammi ta yadda da shi ba, Noir ce ka'dai yake da tabbacin zata fahimce shi but yaga itama tana kuka.
Kallon Ammi ya sake yi 'kwalla na zubo masa masu zafi sosai...a hankali ya fara takawa ya 'karasa wurin ta wannan karon Ammi bata hana shi ba.
Kafa'dar ta yayi niyyan kamawa da niyyan ro'kon ta ta taya shi yiwa Ammi bayani ko zata fahimce shi da kyau fatan sa Allah yasa itama ta yafe masa su sake shimfi'da sabuwar rayuwa..." Cikin zuciyar sa yake wannan tunanin but bakin sa ya kasa furta komai..ji yake tamkar an tokare shine daga 'kirjin sa numfashin sa ma da 'kyar yake fita.
Ga mamakin sa sai yaga yana ta6a jikin Noor ta firgita tamkar an tsikare ta ta mike tsaye tana banka masa hararan ta6a mata jiki da yayi.
Murmushi Ammi tayi domin ba'karamin birge ta Noor tayi ba dama tasan hakan na iyq faruwa tunda ita ce da kanta ta nemi rabuwa da shi, shiyasa ma Ammi ta barshi ya isa garetan dan ya tabbatar wa kansa da kansa.
Shi kam cikin zuciyar sa yake furta" Ki yadda dani Nuree wallahi ni mai 'kaunar ki ne, bazan ta6a ha'da ki da wata cuta ba, soyayyar ki daban take a zuciya ta, ban ta kwatanta 'kaunar da nake yi miki da wata macen daban ba kuma har abada bana jin zan iya ha'da ki da wata, Deen 'din ki ne Yayan ki dan Allah ki bu'di ki wakilce ni wurin Ammi ki fahimtar da ita cewa nadamar gaskiya nayi, tayi ha'kuri kar ta raba ni dake na rasa Baby bana so.kema in rasa ki Nuree, ki ce min ta yafe min laifuka na Insha Allahu bazan sake 6ata mata rai ba har 'karshen rayuwa ta..."
He wish a fili ya iya furat hakan amma harshen ya kasa yi mai motsi duban ta kawai yake da idanu zafin zuciyar sa na 'karuwa.
..Gaban sa Ammi ta tako ta tsay nesa ka'dan da shi, hannun Noor ta ru'ko cikin nata ganin kallon da yake yiwa Noir ne ya sa Ammi nuna shi da 'dayan hannun tan sannan ta nuna inda littafin ke ajiye tace" Kai nake sauraro...".