Sashe 190
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune take akan kujera mai zaman mutun biyu idanun ta na kan wayar ta ne tana dubawa.
Sallamar da yayin ma ko 'dagowa batayi ba a hakan ta amsa shi.
Gaban ta ya 'karaso ya zauna tare da kwantar da kansa bisa 'kafar ta, haka kawai sai yaji kuka ya kubce masa na tausayin kansa da yake yi.
Ammi barin abinda take yi tayi ta zuba masa idanu da alamun mamaki.
Daga bisa ni baya tayi ta jingina tana duban suman kansa har zuwa fuskar sa gaba 'daya.
Yanda duk suka yi wani iri da su, basu samun gyara yanzu sosai kamar baya, tamkar ba Mu'een ta ba 'dan 'kwalisan nan wanda akoda yaushe zaka ga kansa na 'kyal'kyali da sheki fuskar fayau gwanin birgewa, gashi da son barin gashi akansa ya tara shi ba'ki'kirin...a hankali ta maida idanun ta wajen wuyan sa duban farko idan kayi masa zaka fahimci uwar ramar da yayi musamman idan ya kasance ka sanshi watanni biyar da suka gabata.
Har cikin zuciyar ta take jin tausayin sa amma ta danne bata nuna ba..she have to purnish him saboda yasan ba haka kawai suka haife shi suka barwa duniya shi ba, so take yasan illa da aibun rayuwar da yata aikatawa.
Alhaji ya riga ya sanar da ita batun takaddar Noor da ya kai masa bata ji da'di ba kam amma ta wani 6angaren tana ganin shine dai-dai...hankalin ta be tashi bane ma ganin cewa saki 'daya ya rubuta mata, har yanzu akwai possibilityn da Noor zata koma masa amma sai ta tabbatar da daidaiton hankalin sa tukunna...duk dama taga Alhajin kamar shi baya da wannan ra'ayin kuma.
Cikin kukan ya fara fa'din" Ammi yanzu..kwata-kwata kin daina sona, Ammi baki 'kauna ta kamar baya, nayi kuskure kuma na gane kure na amma Ammi kin kasa fahimta ta balle ki ce kin yafe ni, 'karshe sai kika ce sai na rabu da matata kafin zaki yafe min.
Ammi yau gashi na rabu da Noor, ba matsayin iyali na take ba Ammi na sakar miki 'yar ki da kika fi kauna kamar yadda kika bu'ka ta, a yanzu na fahimci soyayyar da kike min koka'dan bata kama 'kafar wanda kike wa Noor ba tunda kika za6i raba ni da ita bayan kinsan itace rayuwa ta, raba ni da ita tamkar raba ni da farin ciki na ne Ammi, bazan iya cigaba da walwala ba matu'kar Noor bata tare dani....nasan nayi mata laifi Ammi amma me yasa baku barni na wanke mata ba'kin cikin da na jima ina sanya ta ciki ba...wallahi ina so in wanke laifi na Ammi..ina so in dawo da farin cikin Noor da ta rasa abaya..amma kun hanani wannan damar Ammi..."
Ammi bata san lokacin da ta kai hannu kansa ba saboda tsananin tausayin sa da taji.
A hankali ta furta" Kar ka ga laifi na Mu'een komai da ya faru laifin ka ne...kuma ko yanzun ma laifin ka ne, da kanka kasan bazai ta6a yiyuwa na nuna 'kiyayya ga 'dan da ni na haifi abu na ba, 'kiyayya ta ga halin kane, basu yi ba, kuma bazan ta6a goyon bayan ka kan sa6on Allah ba ka sani, Mu'een aure fa? Ace duk daraja irin ta aure amma ka rasa matar da zaka nema sai me aure wallahi wannan yafi komai yi min ciwo sai inga kamar ba dan dama na haifa ba, 'karin takaici ma kuma har gidan daka tabbatar matar ka na zama agidan kake kawo.mata wannan wani irin 'karamin tunanin ne Mu'een?"
"..Kiyi hakuri Ammi na ni da kina nasan ban kyauta ba...".
" Ni na ha'kura kar ka damu amma ka nemi gafarar mahallici dan shi ka yiwa laifi.."
" Ina yi kuma Insha Allahu zan 'kara neman gafara a wurin sa.."
"..Gud...ka 6ata raina sosai Mu'een, ka zalunci matar ka ka maida ita tamkar bata san abinda take yi ba kawai dan kaga tana hakurin zama da kai ko?"
" Ba haka bane Ammi...ni dai ki yafe min dan Allah".
Ajiyan zuciya ta sau'ke sannan ta ce
"... komai ya wuce..sai dai kuma nadamar ka tazo ne a 'kurarren lokaci, na riga na yanke shawara so kaga saboda ni na haife ka bazai yiwu in shiga hakkin wata ba, baya ga haka ma ga shi Alhaji ne ya fara jagorantan rabuwar ta ku, ita kanta ma ta bu'kaci sakin ta tun kafin mu baro Bauchi, kaga kenan ita ma da kanta taji bazata iya sake rayuwa da kai kamar yanda tayi abay ba, finally yanzu ka sake ta kuma naji da'din hakan dalilin ma kenan da ya sani cika al'kawarin dana 'daukam maka na cewa zan yafe ma da zarar ka bani takaddar Noor..Alhamdulillah yanzu babu nawin kowa akaina, kaima sai kaje ka huta wa ranka domin baka da daman gyara kuskuren da ke tsakanin ka da ita cuz ta fita daga cikin igiyoyin auren ka..sai dai kawai ka tsaya ka gyara tsakanin ka da ubangijin ka...6angare na kuwa baka da matsala komai ya wuce buri na shine ka tabbatar min da cewa ka rabu da wancan rayuwar ne rabuwa ta har abada....".
"..Insha Allah Ammi I promise u ban sake wa har abada....".
Murmushi Ammi tayi tana duban sa tace" Not this way, cikin actions din ka nake so na fahimta".
Zai yi magana Ammi tayi saurin dakatar da shi da fa'din" ya isa hakan nan...ga breakfast can je ka sanyawa cikin ka wani abin idan basu yi maka ba let me know sai in sama maka wani".
Mi'kewa kawai yayi batare da ya sake duban table in ba kawai ya nufi 6angaren sa.
Har jin kansa yake yi babu nawi saboda tsabar rashin sukuni, dagaske kenan yanzu komai ya 'kare tsakanin sa da Noor, bai san me yasa ma yake jin sabuwar 'kaunar ta na sake ratsa shi ba...ina take? Cikin wani hali take? Duk bai sani ba.
Burin sa kawai shine ya ganta ko da sau 'daya ne amma ya rasa ta ina hakan zai faru...yana so ya ganta ya bata ha'kurin abinda ya faru da Baby amma da alamu tayi masa nisa.
Da kansa ya 'kira Ishaq da Safwan yayi musu albishir 'din yafiyar da iyayen sa suka yi masa bayan sakin Noor da yayi, inda ya 'kara da yi musu godiya sosai akan jajircewa da suka yi akan sa, ha'ki'ka sun kasance mutane da bazai ta6a iya mantawa da suba cikin rayuwar sa.
Su Ishaq basu 6oye masa farin cikin da suka shiga ba da jin wannan labari...a yanzu duk hankalin su ya kwanta nan suka yi mai nasiha akan rabuwar sa da Noor 'din, suka ce kar ya damu haka Allah ke ikon sa, idan da rabon zama watarana zata dawo masa da iznin Allah...idan kuma babu Allah ya musanya masa da wata mafi Alkhairi..
Kai ya girgiza yace" Bana tunanin akwai wata Ishaq, babu wacce zata kai min Noor".
" Kar kace haka man, ai duniya nada fa'di Allah ka'dai yasan iyakar abin alkhairi dake cikin ta mu ne dai bamu san hakan ba balle mu san ta inda alkhairin zai zo mana...samu da rashi ma duk na Allah ne, dan ka rasa Noor kuma ba yana nufin ka rasa farin ciki bane...may be wani tanadin yayi maka wanda yafi wannan 'din...yace nima ba gashi ba lastweek mahaifin yarinyar da zan aura yazo daga Niger ya tafi da 'yar sa, kasan dama wurin mahaifiyar ra take mijin mahaifiyar shi ya bada auren ta, anyi mai batun auren ta da ya kusa ma sai cewa yayi wai a janye batun kawai shi bazai aurar da ita anan ba haka yasa yarinyar agaba suka tafi tana kuka..kaga shikenan batun ya tashi, so na isa in cewa Allah meyasa ne?
Ina jin son yarinyar amma dole na hakura na barwa Allah komai..sau tari abinda ka sawa ranka sai kaga ba shine alkhairin rayuwar ka ba".
" Hakane Ishaq, Ubangiji Allah yasa mu dace, Allah ya ka wata wacce tafi wancan..."
" Ameen Mu'een tare da kaima".
Cewar Ishaq yana murmushi, shima 'din Murmushin yayi kawai batare da ya furta komai ba.
Duk yanda yaso ya 'dauki hankalin sa da tunanin Noor kasawa yayi, sosai yake zurfafawa zuciyar sa wajen hasko inda Noor in sa take har yanzu ya kasa ganowa.
Alhamdulillah yanzu kaso mafi rinjaye daga cikin damuwar sa sun kau domin iyayen sa sun yafe shi duk kansu suna amsa gaisuwar sa duk dama babu wani sakin fuska sosai amma da sau'ki...damuwar sa a yanzu kashi biyu ne kacal, rashin kulashi da Uncle Ja'afar basuyi sai kuma tsananin tunanin Noor da ya addabe shi.
A kullum ji yake tamkar 'kara masa wutan 'kaunar ta ake yi cikin zuciyar sa shiyasa takasa barin ransa, a kullum tunanin sa ita ne ka'dai...sai Jasmine da yake yawan tuna memories 'din ta.
Wa'dannan abubuwan ne ka'dai yanzu damuwar sa kuma su suka hana shi sukuni.
Tsakanin sa da Uncle Ja'afar kam ya riga ya shirya yanda zai yi, jira kawai yake ya 'dan 'kara 'karfin ala'kar sa da iyayen sa ya kuma sake samun karfin jiki kfin ya tafi, ya yanke shawara can Taraban kawai zai je su sasanta da su in yaso ma sai ya 'dan huta can kafin ya dawo.
Hakan yasa ya 'dan saki ransa cuz yasan idan yaje gare su kamar anyi an gama ne..d fact that ya saki matar sa ka'dai ne ke damun sa yanzu.
Idan ya gaji da zaman gida har gidan gona yake bin Alhaji Baba ya taya shi ayyuka, kuma fitan na 'debe masa kewa sosai yake rage masa yawan tunani.
Abinda yasa shi ya daina fita 'din shine watarana da ya fita da yake yana tafiyar sa ne da 'kafa kullum idan zashi, ranar ma haka ya fito jikin sa dogon wandon jeans ne, sai farar singlate daga ciki, longslip riga ya sanya ja mai ratsin ba'ki-ba'ki, bottles na 'kasan rigar kawai ya sanya saman 'kirjin sa abu'de kana iya hango farar singlate in nasa.
Tafiya yake iskan hantsi na hura shi, tafiyar sa yake cikin natsuwa tamkar wanda ake irga takun sa, ji yake kamar iskan zai tafi da shi saboda rashin 'karfin jiki, rama sosai yayi wanda duban farko idan kayi masa zaka tabbatar da cewa cikin tsananin damuwa yake.