Sashe 140
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana daga tsayen ya furzo da iskan bakin sa sannan ya ta6e baki gami da buga min wata harara da ban ta mecece ba.
Kawar da kaina gefe nayi ina tunanin me kuma ya kawo shi, me yake nema.
'Ko'karin fita na fara daga 'dakin inda na tunkari hanyar fita.
Sai ji nayi ya ri'ko hannu na gami da fa'din" Zonan".
Take na waigo a 'dan firgice na kalle inda ya ri'ke hannu na kafin na ankara sai ji nayi ya janyo jikin sa kusa da shi sosai ya ha'da bayana da jikin sa still yana ri'ke da hannaye na, cikin kunne ya ra'da min" Kin raina ni ko?"
Sai nayi saurin girgiza kaina.
Yah Deen sai yace
" Erh mana kin raina ni..yau ma ko gaida ni ma 'kin yi kika yi".
" mancewa nayi".
Yace" Me yasa to kullum kike wa Ammi gardamar zuwa gidan can?"
Shiru nayi na nayi narai-narai da idanu kamar zan yi kuka.
Jin nayi shiru ya sanya shi juyo da ni na fuskance shi take nayi 'kasa da idanu na sai ga hawaye ya gangaro saman kuncina.
Kaina ya 'dago da hannayen sa amma ban iya duban sa ba.." Har yanzu baki mance wancen abin ba ko?"
Shiru nayi sai ma nayi 'ko'karin cire kaina daga hannun sa amma bai sake ni ba sai ya maida min kannawa saman 'kirjin sa ya rungume ni...ni kam sai na cigaba da kuka na.
Bayan kamar sakan sha biyar sai naji yana fa'din suna na" Noor!"
Ya fa'di cikin sanyin murya mai hankali.
Ban amsa shi ba illah hawaye na da na cagaba da gogewa.
" Kina jin kishi na dama sosai har haka ne?"
Girgiza kai nayi da sauri alamar" a a.."
" To menene yake damun ki ki gaya min kinji?"
" Ni bakomai kawai ban son zuwa ne".
" Kin tabbatar bakomai?"
Nace" Umm".
'Kasan ma'koshi.
Sai yace" Zan tafi Bauchi yanzu kimin addu'ah..."
" Allah ya tsare hanya".
"Murmushi yayi sanna yace" Ameen"
A takaice.
Cire ni yayi daga jikin sa amma bai saki hannu na 'daya daya ri'ke ba yace" Barin je sai na dawo ko?"
" Uhumm".
Na bashi amsa da shi
Daga haka ya sake min hannu yayi waje.
Ko bayan fitar sa ma kuka na nasha na na 'koshi sannan nayi shiru.
Lokacin da Ammi ta dawo kuwa bacci nake yi ban ma sani ba sai da na farka kusan Azahar sannan na ganta.
Washe gari Yah Deen ya dawo Bauchin ko damuwa da kamarin sa ma banyi ba, shima 'din kuma bai damu da shiga sabga ta ba.
Bayan kwana biyu kuwa sai ya kasance gidan Ummah ta zan yini da sunan wai muyi sallama da su, Yah Deen ma Ammi tasa ya sau'ke ni, haka kuwa tunda ya 'dauko ni har ya sau'ke ni babu wata kalmar da ta shiga tsakani na da shi domin haushin sa yanzu nake ji sosai, musamman saboda tafiyar nan, baya ga haka ma gashi jiya ya 'kara tunatar dani batun sa da Husnah sai haushin sa ya 'karu sosai cikin zuciya ta.
Har na fita cikin motar na rufo ta bance da shi 'kala ba kawai na juya na yi cikin gida, da shiga ta na cire mayafi na na shige 'dakin Ummah ta na kwanta na cigaba da zubda hawaye na.
Ummah ta data ga yanda na shiga sai bata kula ni ba ta cigaba da sabgogin gaban ta domin ba yau tasan da batun tafiyar ba kuma tasan babu mamaki akai ne nake kukan.
Ina daga cikin 'daki kamar daga sama najiyo sallamar sa, Ummah ce ta amsa shi tare da yi masa iso sannan ta umarci Ummie da ta shinfi'da masa abin zama..inda ta 'kara da fa'din" Ke kuma Hudah kinsan bake ka'dai bace shine kuma kika wucewar ki ciki dan shegantaka ko?"
Ina daga inda nake kwancen nake gungunin" Ni nasan zai shigo ne, mutun kullum yanayin sa daban-daban ina zan gane masa"
Bazan manta masifar da ya zabga min lokacin da naje Darazau ba...amma ji shi kamar ba shi ba a 'yan kwanakin nan, sai daga baya ma nayi mamakin me yasa be tada zancen ba musamman yanda naga ya 'dauki zafi a lokacin har tsoro ya sani.
Murmushi kawai Yah Deen yayi da jin furucin Ummah ta..haka ya zuna fuskar sa wasai tamkar wanda dama can yayi sabo da gidan sosai...in kinji yadda ya nutsar da murya yake gaida Ummah ta bazaki ta6a zaton yana da wani hali daban ba.
Da kansa ya 'kara yi mata bayanin tafiyar ayanda tazo Ummah tace" Ai bakomai Allah ubangiji ya tsare ya bada sa'a"
Yace" Ameen-Ameen".
Bai wani da'de ba ya tashi ya fita bayan ya ajiyewa Ummah ta ku'di, duk yanda tayi da shi ya tafi da ku'din nan 'ki yayi, da yake shima yasan ba fitowa zan yi ba yasa da fitowar sa yaja motar sa yayi gaba abin sa.
Ina daga cikin 'daki nake mita da zagin sa cikin raina..mutun sai munafurci da fuska biyu, idan ka ganshi bazaka ta6a zaton zai iya aikata abinda yake aikatawa ba, kuma Allah sai ya sakawa Ma'u kashe ta da kayi..tuno Husnah da nayi yasa ni fa'din 'yan iskan banza kawai".
Cikin 'dacin rai nake tuno duk 6oyayyun halin nasa na ina kuma jin ciwon su cikin zuciya ta.
Ummah ko ka'dan bata yi niyyan tanka ni ba har sai da na gama zaman 'dakin da kaina na fito sannan gani na haka a hargitse ya sa ta tambaya ta abinda ya same ni, take kuwa na bata labarin tafiyar tare da nuna mata rashin amincewa ta ina fa'da ina kuka, dan ni harga Allah bana son inbisa wani gari mutun cikin garin iyayen sa ma bai ji shakkan kawo mata gidan sa ba inaga inya ke6e gefe kuma?" Cikin zuciya ta na 'karasa wannan tunanin ni ka'dai.
Ummah kam shiru tayi ta gama saurara ta sai da na dasa aya sannan tace" Yanzu Uwata akan wannan tafiyar kike faman 'daga hankalin ki har haka? Miye abin damuwa aciki to?"
Shiru nayi mata bance da ita 'kala ba...cikin zuciya ta na ayyana" Ai Ummah bazaki ta6a ganewa ba, 'kilan nima sai an kawo miki gawata ya kashe nima kafin zaki fahimci abinda ke damu na a lokaci na da kuma dalilin 'kin binsa da naso yi".
Ummah kam tsura min idanu tayi tamkar mai tunani daga 'karshe tashi tayi ta barni a wurin,m zaune, da kaina na gaji da kukan na watsar da batun na cigaba da harkoki na.
Sai can har bayan azahar ma da taga na nutsu sannan ta zaunar da ni tayi min Nasiha, garga'di, ban ha'kuri da kuma jan kunne game da aure na, sosai ta nuna min cewa irin nawa auren natsuwa yake bu'kata dole in bada hankali na, in kula da hakkokin aure na kar inje inbiye wa shirme har wata 6araka ta sake 6ullowa, tace" kowa da kike gani a duniyan nan Hudah da aure ya ginu, aure ne nasarar kowa, da yawan mutane kuma auren na riskan su ne cikin rashin amincewar su amma sai suka yi ha'kuri gagarumar nasara kuma ta cimma su sanadin ha'kurin su, dalilin hakan ma sai kiga sun dace ranar gobe alkiyama, kema ina miki kwa'dayin wannan nasara matsayina na mahaifiyar ki Uwata, ko kukan da kike yi a yanzu da kanki kinsan ba amfani ne da shi ba, domin ba tun yau aka 'daura auren ki ba, bani da ikon sawa ko hanawa a yanzu kinsan yanzu ke mallakin su ce, su ke da iko akanki bani ba, ni kuma bazan ta6a saki ki bijirewa auren ki ba har abada sai dai in wani abin na nagani wanda ya sa6awa shari'a sannan, amma yanzu kam sai dai ince kiyi ha'kuri ki bi mijin ki, kuma ki sani yanzu ne rayuwar aure na sali ya tunkaro ki ba shirmen da kika kusan shekara kina yi ba, domin zaki jene inda babu kowa naki sai ke sai Allahn ki sannan mijin ki abu na uku da zai kasance tare da ke shine halayyar ki, dan haka ki yi 'ko'kari ki tsarkake zuciyar ki ki zauna da kowa lafiya ki yiwa mijin ki biyayya ki kuma ri'ke sirrin ki, mijin ki ka'dai ne abokin hirar sirrin ki da ya shafi auren ki, Hudah har yanzu nasan da sauran ki amma watarana da kanki zaki fahimci cewa ba 'kinki muke yiba inma kinsa hakan cikin zuciyar ki, sannan ki daure ki koyawa zuciyar ki kar6an 'kaddara kowace iri ce kinji? ki cigaba da yiwa mijin ki addu'ah Allah ya nutsar da hankalin sa wuri guda insha Allahu watarana komai zai zam tarihi kamar ba'a yi ba, abinda kuma ya riga ya faru ya wuce kar ki yadda ki barshi cikin zuciyar ki balle ya dame ki, domin Allah shi ka'dai yasan dalilin ha'da auren ku, tace bazan 6oye miki ba Hudah ni kaina raina ba son wannan auren yake yi ba amma ba yadda zanyi dan ban isa inja da yin Allah ba, sai dai fatan Allah ya baku zaman lafiya mai 'dorewa, idan ancutar dake Allah yana gani kuma zai miki sakayya amma dan Allah kiyi min al'kawari bazaki ta6a cutar da kowa ba".
" Insha Allahu Ummah na"
Na yi maganar siraran hawaye na gangaro min.
Ta sake fa'din" Kiyi min al'kawarin zaki zauna da mijin ki lafiya kiyi masa biyayya da ha'kuri cikin ko wani irin hali".
Wannan karan ina share hawaye nace" Insha Allahu Ummah na".