← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 211

Sashe 146

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da kansa da asubah yake tambaya ta wai a ina na samu turare mai 'kamshi haka, 'kamshin ya masa da'di"
Ban 6oye ba na fa'da masa cewa sistern Abokin sa ce ta bani.
Sai yace to ince mata ta kawo zai siya min".

Da yake na fahimci 'kamshin ne ya ja ra'ayin sa har jiya ya takura ni sosai shiyasa take na juya kaina 'dayan 6angaren sannan nace ai ya 'kare na wajen tan".

Yace
" To bari zamu nemo ba'a akwai aurin ki ba?"
Girgiza kaina nayi sannan cike da 'kosawa nace" Ni a a, babu dama ba yawa kuma san min tayi a wani kwalba 'karami".
Nayi.maganar ne ina tura baki na, baya kallon idanu na amma daga yanda nayi maganar yasan 'dayan biyu ne, inma raina baya son maganar da yake min 'din ne ko kuma zancen turaren ne ban so.

Hakan yasa yayi shiru bai sake yi min zancen ba.

Ni kuwa gari na wayewa bayan na bashi.breakfast sai na koma cikin 'daki, turaren na 'dauka na tsiyanye shi a bayi na kora ruwa, kwalbar kuma na jefa a dustbin ina ta6e baki cikin raina nace" Bazan mutu akaron banza ba ni kam". 

Ban kuma komawa gidan ba da yake biki ya 'kare so a waya ta tambaye ni batun turaren sai nace mata ai nayi amfani da shi har ma ya 'kare.. Sai tace min" Ya to kina son 'kari?"
Da sauri na girgiza kaina sannan na nace a a please Anty Fiddausi ba irin shi ba ni kam".

Dariya ta sanya sannan tace" Matsoraciya...kafin in koma ai zaki zo muyi sallama ko?"
Nace" Erh zanzo".
" Ok shikenan.."
Tace daga haka kuwa ta yanke 'kiran tana min dariya.

Shi da kansa Yah Deen da aka kwana biyu bai kuma jin 'kamshin ba sai da ya tambaye ni amma ban bashi amsar komai ba...hakan yasa bai kuma tambaya ta ba.

Abinda baki sani ba Hafsat ko a bikin ku sai da Yah Deen yayi wata budurwa mai suna Yusrah inajin 'yar sistern Mummy ce mahaifiyar Dr Safwan.

Yah Deen da kansa ya nemi ha'da ala'ka da ita batare da sanin Safwan ba har suka 'kulla soyayya, ko bayan bikin ku sun 'dan da'de suna tare da shi, har ala'kar tasu ta juye ta koma wani abu daban kamar yanda ya saba.

(" Yah Deen kenan, inajin mantawa yayi da girman al'kawarin da ya 'daukan ma kansa na cewar ya daina neman wasu matan saboda Huda, musamman saboda girman abinda ta aikata masa na rufa masa asirin da tayi ban fa'dawa kowa sirrin sa ba, da kansa yayi al'kawarin yanzu kuma hala har ya mance...ka'dan kenan daga halayyar 'dan Adam...shine saurin mantuwa musamman ma abinda ya dace).

Ni dai gani kawai nayi ya daina yawan nemana a shimfi'dar sa, duk da yake ma nasan ko ada 'din ba kullum yake ra6ar jiki ba amma na yanzun sai yayi yawa, ya kan shafe kwanaki bai nemi ha'da shimfi'da da ni ba, ban kuma san dalilin ba a lokacin, amma koka'dan bai canza min fuska ba da yake ya iya takun sa, ni kuwa hakan dama bai dame ni ba, ban damu ya nemi hakkin sa ko a a ba balle in sa abin cikin raina har in kuma kawo wani tunani daban.

Da idanu kuma na nasha cin karo da 'kiran mace cikin wayar sa, na kanga suna Yusrah ta 'kira shi kamar yadda yayi saving.

Dan a duk lokacin data ga dama 'kiran sa 'kira take yi 'kilan bai sanar da ita yana da mata bane oho, sassafe wataran zaki ga 'kiran ta, wani lokaci kuma yana wanka in ta 'kira idan na duba sai in ga sunan ta ko da yazo yagani kuwa baya ta6a 'kiran ta acikin gidan sai ya fita, cikin dare kuwa idan ta 'kirasa kashe wayar yake yi gaba 'daya yayi baccin sa, duk hakan da ke faruwa ina lura da shi ni kam sai dai in ta6e baki na kawai domin bani da damar da zan tunkare shi da maganar shiyasa na zuba idanu kawai ina ganin sarautar Allah.

Hatta gidan Safwan ma da 'kyar yazo ya samu lokaci muka je bayan da Safwan yai ta masa gorin cewa kamata yayi ace shine ba'ko na farko da zai fara ziyar tar gidan sa  amma sai gashi ya nuna masa halin ko inkula, ko ranar da muka je 'din ma Safwan sai da ya maimaita hakan aka maida shi wasa, bai sani ba ashe Yah Deen kam wata ce ke 'dauke masa hankali da ya tashi daga aiki bashi da wani cikakken lokacin kansa sai nata.

Ni dai ban sa cikin raina cewar akwai irin wancan ala'kar tsakanin su ba duk da yawan ganin 'kiran ta da nake yi, ina dai tsintan zuciya ta wani sa'in da matsanancin jin haushin 'kiran nata.

Tsawon wata guda hakan na faruwa tsakanin su, acikin wata gudan kuwa kaf bai fi sau biyu ya nemi kusantata ba, duk hakan bai wani dame ni ba dayake yanayin rayuwar mu bata canza daga yanda take farko ba, duk wani da yasan zan bu'kata tun.kafin in nema yake kawo min shi, abu 'daya ne kawai nasan ya ishe ni shine yawan ganin 'kiran Yusrah da nake yi cikin wayar sa.

Ranar ma lokacin bayan Isha'i yana zaune kan dinning ina serving masa abinci sai wayar shi ta fara ringing, wayar kuma tana can kan center table dake tsakiyar parlourn mu.
" 'Dauko min wayar".
Yace yana me kar6an serving spoon dake hannu na.

Zuwa nayi na 'dakko masa wayar nan naga sunan mayyar nan" Yusrah.
Nan take naji wani 'kululun ba'kin ciki ya taso min har zuciya na canza salon harbawan ta.
Baki na ta6e ina mai 'karfafawa zuciya ta gwiwa da fa'din" Ina ruwan ki ke kuma Hudah?"
Wata zuciyar tace dani" Ai mijin ki ne ba nata ba".
Cikin raina nace" Jarababbiya kawai".

Zuwa nayi na mi'ka masa still ina jin yanayin yanda heat beat 'dina ke saurin harbawa.
Cikin idamun sa nake kallo domin inga reaction 'din sa amma ban ga komai ba.
Kar6an wayar sa kawai yayi dai-dai lokacin da 'kiran ya yanke sai ya danna flight mode ya ajiye ta, sai a lokacin kuma ya kalle ni muka ha'da idanu.

Saurin kawar da kaina nayi jiki na sanyi 'kalau na bar inda yake da yake dama batare muka saba cin abinci ba shima sai bai kula ni ba kawai ya bini da idanu.
A fili ya fahimci kishin da ya taso min, shi da kansa bai ji da'din faruwar hakan ba har cikin ransa amma sai yaji ya kasa tantance abinda ya kamata ya aikata, tunanin sa ya kasa bashi abinda ya kamata ya aikata.

Hakan yasa ya sunkuyar da kansa kawai ya fara cin abincin sa.

Sati 'guda bayan faruwar hakan naje gidan mahaifiyar Safwan domin yin sallama da Anty Fiddausi zata koma Katsina garin da take aure, nan na samu ma har Mimah tazo 'karamar 'kanwar su dake aure a nan cikin garin Bauchi, itace ma na samu duk ranta a 6ace sai naji wani iri, lokaci-lokaci takan saki tsaki, har bayan zuwa na muka gaisa still naga fuskan ta bai canza ba, na samu Mummy bata nan tana wurin aikin ta suka ka'dai a gida dana tambaye su ita ne shine Anty Fiddausi ta gaya min.

Na kan lura da su idan Mimah tayi wani 'dan reaction ko kuma tayi tsaki sai kiga Anty Fiddausi ta harare ta ni kuma muna hirar mu da ita cikin kwanciyar hankali.
Chapter 146 · 0% Book details