Sashe 169
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Safwan kam cire rai yayi da tunanin yana cikin motar har ya juya ya fara tafiya inda yake 'daga 'kafar tasa da 'kyar.
Jasmine ce ta fa'do ransa sai yayi saurin yun'kurawa ya kaiwan hannu da fatan zai samu jin da'd'dan labari daga bakin Safwan game da iyalan sa.
A hankali ya bu'de motar wanda yayi dai-dai da waigowan Safwan sai yayi arba da shi yana duban sa da lumsassun idanu, kallo 'daya zaka yi masa ka tabbatar ba lafiya yake ba.
Wani ajiyan zuciya Safwan ya sau'ke cike da farin ciki ya dawo baya yana furta _Alhamdulillah_ a fili, gaban sa yazo ya tsaya yana duban sa yace" Haba Mu'een me yasa kake haka ne wai? Baka tunanin halin da iyalanka.zasu shiga saboda rashin ka? wallahi ka tashi hankalin mu sosai babu inda ban nemeka ba amma na rasa ka har gidan ka naje..ga can su Alhaji ma sunzo Ammi duk damu kasa tana can tana ta kuka a banza..."
Jin sunan iyayen sa cikin maganganun Safwan 'din ne ya sashi saurin sako 'kafafun sa waje ya fito tare da kulle motar.
Bai jira Safwan ba kawai yayi gaba yana tafiyar sa cikin natsuwa, 'karfi da yaji ya danne ciwon da yake ji dan kar suyi tunanin kwantar da shi suce a duba shi.
A baya Safwan ya bisa har bakin ward 'din da Baby take kwance...yana tafiyar yana yi masa mitan 6acewan da yayi.
Har a lokacin kuwa Yah Deen bai furta masa komai ba har suka isa.
Yana fara hango su Ammi sai yaji 'kafafun sa sunyi masa nauyi a hankali ya 'karasa kusa da su wanda Alhaji Baba ma da hango shi ya yi saurin isa gaban sa suka rungume juna.
Kuka Mu'een ya sanya masa yana fa'din" Dan Allah Alhaji ka yafe min, bansan haka rayuwa ta zata juye min ba..."
Alhaji Baba zaton shi ko duk kan rashin lafiyan Babyn ne dan haka sai ya ringa kwanatr masa da hankali amma Yah Deen ya'ki yin shiru..fa'di yake" Noor tace nine sanadin komai, ni ne na jawa Baby duk abinda ya same ta kuma na yarda nima Alhaji, wallahi nayi nadamar rayuwa ta na zalunci Baby na 6ata mata future in ta tun kafin zuwan ta duniya batare da na farga da hakan ba...".
Saurin cire shi Alhaji Baba yayi daga jikin sa yana duban sa cike da mamakin kalaman sa, yayin da Ammi da ta matso da farin cikin ganin sa ita ma ta kafe shi da idanu tana duban sa cike da tausawa.
Hawayen dake zubo masa Alhaji Baba ya fara share shi masa, duk tunanin bai ja shi wani wuri ba, yayi zaton ko duk zafin so da tausayin Jasmine ya sa shi furta wa'dannan kalaman.
Ganin Ammi gefen sa ne ya sanya shi waigowa ya tafi gaban ta itama ya rungume ta tana bubbuga bayan sa cike da tausayawa.
Zaiyi magana ta dakatar da shi da fa'din" Shi...ya isa haka nan Mu'een kar jinyan yarinyacya zautar min da kai..ka manta cewar Allah ne ya 'dora mata ko?".
Murmushi yayi tare da cire jikin sa daga jikin Ammin, hannun sa 'daya yasa ya share hawayen fuskar sa, cak idanun sa suka sau'ka kan Noor suka ha'da idanu, itama hawaye ne kan fuskar ta sha6e-sha6e, take kuwa tayi saurin kawar da kanta gefe ta daina kallon sa, bai damu ba sai ya dawo da kallon sa wurin Ammi.
Dur'kuswa yayi ya zuba gwiwoyin sa a 'kasa, sannan ya kamo hannun Ammi yace" Ammi..ku iyaye na ne masu matu'kar 'kauna ta, kun bani tarbiya kun bani ilimi, kun bani farin ciki da gatan rayuwa, kunyi 'ko'kari sosai wajen ganin kun bani duk wani abu da yake hakkin ku, kuka 'kaunace ni kuka koya min son Allah da mazon sa, kuka koya min bauta da kuma bautawa Ubangiji na, kun nuna min haramci da duk abubuwan halal dake cikin rayuwa amma nayi watsi da shi.
Ammi ku yafe min dan Allah, badan hali na, ban ta6a sanin cewa da gaske halayya ta kan iya dawowa ga ahali na ba sai yanzu Ammi, ace da ciwo, na 'dauki abin.wasa ne shiyasa duk na mance da hakan sai gashi yanzu ya faru akan yarinya ta..."
Ammi saurin fizge hannun sa tayi daga nata ta wani zuba masa idanu cikinbalamar tambaya kan batun da yayi, yayin da Alhaji Baba ma daga inda yake tsayen yake duban sa duk alamun tambayoyi ne kan fuskokin su.
Noor kam kuka ta sanya tare da kwantar da kanta bisa cinyoyin ta, koda wasa bata son taji ana sake maimaita wannan batun..'konabmata zuciya yake yi sosai.
Mummyn Safwan ne tayi saurin 'karasawa kusa da ita ta fara rarrashin ta amma ina, kukan ya riga ya zauna cikin zuciyar ta bazata iya daina shi ba.
" Alhaji..Ammi ku yafe min, amma a yau shirya sanar da ku ko way ni, a yau zan bayyana muku 'dayan 6angare na da bakowa me ya sanshi ba..."
Dukkan su kallon shi suke yi suna jiran jin abinda zai fa'da musu, tun farkon maganar tasa suka fahimci cewa akwai lauje cikin na'di, a fili suka fahimci cewa wani mummunan lamari ne ya faru da Jasmine, domin ko su idan ance su fa'di wani hali Mu'een halayya 'daya zasu iya fa'da wanda yake da munin da zai iya illata wa mutun zuri'ah.."
Ammi idanu ta lumshe bata fatan taji wani makamancin hakan ga Baby, ahse dama haka ne ko da mutun ya tuba ya koma ga Allah fa'dar sa sai ya faru ga nakan.ahse dagaske ne?
Abinda tun farko Alhaji Baba yayi ta masa gudu kenan amma ya 'ke'kashe idanun sa ya yi kamar bai san da hakan ba.
Yah Deen bai damu da irin kallon da suke masa ba a hankali ya bu'di baki kaf ya basu labarin halin sa wanda suka sani da wanda ma basu san da shi ba..wanda ya jima yana 6oye musu da wanda Noor ma ta rufa masa asiri, hatta cikin da ya zubarwa Husnah bai 6oye musu ba...dan ganin sa ba bu'katan wani rufin asiri kuma yanzu bai cancanci hakan ba sam...a hankali har ya gangaro kan abinda ya sami Baby, yanda tuncfarko Noor tayi ta nuna masa rashin dacewar Sani amma ya yi banza da ita, ko ka'dan jinin ta bai 'dauki na Sani ba, da sonta ne da tuni Sani ya bar gidan su amma yayi banza da ita, Allah ya kawar da zuciyar sa ya toshe masa tunanin sa akan komai, hatta 'karan Sani da Baby take yawan kawo masa da yanda take fa'din yana cinye mata baki duk ya tuna su, kuma sai yanzu yasan manufar su wanda abaya bai ta6a fahimtar mai Baby take nufi ba, dayke Allah yaso kama shi, shiyasa ya rufe masa idanu yasa masa yadda da aminta da Sani, jinsa yake tamkar su Saif ne shiyasa bai ta6a ko gwada yi masa fa'da akan wani abu ba, ko zai yi ma sai dai suyi maganar kamar da wasa ta a wuce hakan...bai sani ashe Sani na tafe ne da mummunan 'kaddarar sa da Allah ya tamadar masa, wanda da ace ya sani da tun farko ma ko magana ba zai yadda ta ha'da shi da Sani ba babble har ya bashi masau'ki cikin gidan sa...ayu nayi danasanin rayuwa ta Amma, nayi nadamar komai dana aikata, dan Allah ku yafe min Ammi....Alhaji..."
Sai kuka yaci 'karfin sa ya kasa 'karasa abinda yayi niyyan fa'da.
Alhaji Baba kam kansa ya dafe cikin tsananin tashin hankali, ashe duk yanda ya 'dauki abin Mu'een 'din abin ya zarta hakan sosai, bai ta6a zaton yayi nisa har haka fiye da tunanin sa ba, da Husnah ka'dai ya sanshi kuma bai yi tunanin cewa muhallin su 'daya a makaranta ba, ashe har da zubar da ciki yayi, banda wanda ya 'dirkawa 'yar gidan Malam Barau hallau yazo ya dinag bibiyan Husanh bayan yasan da aure akanta...Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Yah Allah me na haifa?
Ada yayi zaton ko tunda yayi aure shikenan da yake bai sake ji ko ganin wani abu makamancin wancan da yafaru abaya ba ashe yaudaran kansa yayi da wannan tunanin, ko bayan.auren sa ma Hudah ta kamashi da Husnah kuma ta rufa masa asiri..bazai ta6a mantawa da lokacin da ta dawo gida ta'ki komawa ba wanda 'karshe dole sai.kayanta aka kawo mata ta cigaba da zama agida, ashe duk saboda banzan halin sa ne, a lokacin baya zurfafa bincike akansa dayake yana tunanin komai ya wuce..Mu'een Allah ya wadaran rayuwar ka wallahi, banda tarin abin kunyar daka 'kunsa min a Shuwarin, mutun mai mutunci amma ka ha'da ni da shi ka ha'da 'yar sa da kayan cikin 'karshe ma ta rasa rayuwar ta Mu'een ashe wannan ma bai ishe ka ba,.har gobe tsananin kunya da nauyin Malam bai barshi ba banda ma jama'ar gari kawai dannewa yake yana mu'amalar sa dan kar aga fuskan da za'a gaya masa magana amma shi ka'dai yasan yanda yake ji cikin zuciyar sa.
...Alhaji Baba jiri ya fara ji na 'diban sa Safwan ne yayi saurin tare shi suka zauna kan kujerar dake wurin yana bashi ha'kuri.
Sam Safwan bai yi mamakin jin labarin Mu'een ba cuz da kansa ma ya sanar da shi a lokacin giyan son Nuree na 'diban sa so bai 6oye masa komai ba illah batun Jiddah da ya faru daga baya, shiyasa ko yanzun ma bai yi wani mamaki ba.
Ammi kam tsaye ta mi'ke ta wafce hannun ta daga cikin nashi, babban abinda ya 'daga mata hankali shine jin asalin abinda aka yiwa Jasmine ga haushin Noor na rufa masa siri da tayi tun abaya har ta cigaba da zama da shi, wanda da tasan hakan da ko hauka take yi bazata ta6a barin ta ta zauna da shi ba, wajen ta tayi niyyan zuwa ta sau'ke mata 6acin ranta amma sai taji Yah Deen ya sake ri'ke hannun ta yana ro'kon.ta yafe masa yayi al'kawarin ba zai sake ba...