Sashe 27
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Noor da ta rasa mai zata ce da Hafsat sai kawai taci gaba da kukan ta.
girgiza kai Hafsat tayi cike da damuwa gaba 'daya zuciyar ta ta karye.....'dago kan da zatayi sai idanun ta suka sau'ka kan Deen da tsayuwar sa kenan a wurin.
bayan sa wata Nurse ce dake 'ko'karin shigowa itama "....excuse me".
Tace dashi amma ko motsi bai ba.
koda ta sake excusing 'din nasa ma still kamat bai ji ba dan haka sai ta tsaya jiran ya matsa kawai kafin ta shigo.
Yayin da ya tsurawa iyalan nasa idanu yana kallo da sauraren sautin kukan Nureee da ke ratsa masa har zuciya yana sake illata shi ta ciki.
Hafsat ne tace
"...ah ah Doc..tor!
Tayi maganar da rawar murya gami da 'dan jin natsuwan zai taimaka mata wajen kwantar wa Noor 'din hankali.
" k'araso mana" ta sake fa'di a take gami da mi'kewa tsaye.
Cak kukan Noor ya tsaya da jin sunan da Hafsat ta fa'di duk da tasan likitoci nada yawa musamman da ya kasance cikin asbiti suke, amma tasan da irin sunan Hafsat ke 'kiran Deen.
Tsaye itama ta mi'ke tana jefa masa wani mugun kallo da shi ka'dai ya san ma'anar sa.
'Bangaren Saif kuw batare da ya tsaya sake bi ta kan Noor 'din ba kawai ya doka wa 'dan uwan sa dake can ABU Zaria 'kira inda yana 'dagawa ko sallamar da yake yi bai amsa ba kawai yace "......Ni kunyi magana da Yah Deen ne?
Zaid take yace " ah ah gaskiya bamuyi magana ba...."
" Antyn mu fah?"
" itan ma bamu yi waya ba gaskiya....wani abin ne ya faru?"
Zaid ya 'karashe da tambaya sai Said yace "....ina zargin haka gaskiya....cuz recently ta 'kirani tana kuka amma ban fahimci inda ta dosa ba....bari dai in gwada 'kiran Alhaji inji ko sun 'kirashi..."
" ok ni kuma bari na gwada Yayan inji"
Da haka kowa ya yanke wayar.
'Bangaren Deen kuwa ganin kallon da Noor ke jifan sa da shi ne ya sanya shi 'karasowa ciki a hankali kuma har a yanzun hannun sa dafe yake da saman 'kirjin sa.
Shigowar tasa ne ya bawa Nurse daman 'karasowa ciki ta ajiye abin hannun ta 'dan madaidai cin tea flask ne da wani leda.
Sannu kawai tayi musu bata kuwa wani damu ba duk da bata samu amsar kowa daga cikin su ba.
Cigaba tayi da abinda ya kawo ta wato duba Jasmine.
A fusace Noor ta juyo gareta dan zaton ta ko tafiyar su 'daya da Deen ne dan haka rai 6ace tace da ita " da izinin waye kike 'ko'karin ta6a min jikin 'yata?"
Kallon Jas Nurse 'din tayi sannan ta sake kallon Noor tace "...da iznin Dr. Safwan".
Nurse d'in ta bata amsa a takaice.
Nuna Deen tayi da yaja ya tsaya daga kofa yana kallon ikon Allah, batare da ta kalle shi ba tace " wannan kuma fa....?"
Nurse da mamaki ta kalle shi sannan ta kallo Noor tace
" Dr Mu'een wai?...i think familyn sa ne ku 'din"
Cikin d'an hargagi Noor tace
" Ba wannan na tambaye ki ba madam"
Da yatsa ta nuna ta sannan tace" idan har kinsan shine ya kawo ki ward d'in nan to wallahi tun wuri ki bani waje kafin in 6ata ranki anan....bani son salon makirci......".
Hafsat ne tayi saurin dakatar da ita da fa'din " Haba Noor...kar zafin ciwon Baby ya sanya ki zaucewa mana....likita ce fa ita, kuma aikin ta tazo yi me yasa zaki yi haka....ina jin ita ce ke taimaka wa Safwan..ki kwantar da hankalin ki please ki barta tayi abinda ya kawo ta".
Nurse kam bata ko ko second biyar bama ta juya ta fice abinta batare da ta kara fa'din komai ba.
Wanda fitan nata ne ya bawa Jas daman ganin mahaifin ta dake tsaye tun d'azun.
Tana ganin sa kuwa take sai ta 'dan saki fuska da fara'ar ta tace " Daddy!"
Har tsakan kansa yaji sunan da ta 'kira shin dashi amma girman laifin da yake ga yake dashi agare ta bazai bar shi ya amsa wannan babban matsayin ba, gani yake bai cancanci kar6an wannan matsayin ba daga Jas.
A hankali ya 'karaso bakin gadon da Jasmine ke kai Noor na tsaye tana kallon sa ta wani yi kicin-kicin da idanu.
Hannu ya mi'ka da niyyar kama hannun Jasmine sai Noor tayi saurin shiga tsakanin su ta janye hannun yarinyar gami da fa'din " malam me ya faru?
Deen bai tankata ba illah hannun nasa da yabi da kallo sannan ya kalli Jasmine dake kwance " Baby... " ya furta saman la66an sa tare da lumshe idanu sai ga hawaye masu sanyi sun subo masa.
"....karka sake tunanin kusanto inda muke dan banaso ka kaini bango.....daga ni har baby bama bu'katar sake ganin ka ko rayuwa da kai har abada....ai kayi naka...ba burin ka ya cika ba?....sai ka kama gaban ka kaje ka cigaba da rayuwar ka son ranka...baza mu sake shiga rayuwar ka ba balle mu takura ka... please muma ka bar mu hakan nan....".
Ta 'karashe maganan cikin kuka gwanin ban tausayi.
A hankali ya bu'de idanun nasa dake cike taf da hawaye ya sau'ke su akan fuskar Noor da ke faman ruzgan kuka mai tsuma zuciya a hankali ta dur'kushe 'kasa taci gaba da kukan.
Ilahirin jikin sa kaf babu inda sautin muryar tata baya ratsa shi....sosai yake jin zafin hakan sai dai a zahiri sam bai nuna ya damu ba karo na farko cikin rayuwar sa da ya iya jure jin kukan ta batare da ya lallashe ta ba, saboda yasan yayi mata laifuka masu girma a yau 'din da bai isa ya iya hanata kokawa ba, idan ma yayi hakan kamar ya so kanshi ne, gara tayi kukan ko zata 'dan ji sassauci cikin zuciyar ta bisa ga abinda take ji.
.....Kan Jasmine ya maida duban sa da ta turo baki tana kallon sa har ranta take jin fushin bai zo inda take baga kuma kukan da mahaifiyar ta keyi a gefe.
Suna ha'da idanu da ita take ya gane abinda ke cikin ranta musamman ma da yaga yanayin fuskar ta, cuz sosai ya san halin 'yar sa ya kuma san damuwar ta.
Baya ka'dan yaja sannan ya durk'ushe 'kasa a hankali gaban gadon still yana zubda hawaye.
Kai Hafsat ta jijjiga gami da 'daukan Afrah suka bar 'dakin dan ganin kamar ahalin suna bu'katan privacy na musamman.
Babu ma wanda ya bi ta kan ta har ta idasa barin 'dakin ga dukkan alamu ma basu san da faruwar hakan ba.
Jas ne tace " Daddy kaima kana kuka irin na Mummy ko?
Idan kana kuka zan gaya ka da Baba Alhaji idan naje wurin sa".
Cikin kukan Deen yayi 'ko'karin dai-dai ta muryar sa batare da ya goge hawayen ba yace" Baby ki yafe min dan Allah kinji.....ke da Mummyn ki ku yafe min....nasan bazan ta6a goge laifukana a gareku ba amma dan Allah ku yafe min ko Allah zaiji 'kaina".
" Daddy ka daina kuka kar little Afrah tayi maka dariya kai da mummy...na yafe maka kaji ka daina kuka, malam Hashim yace Allah yana son bayin sa masu yafiya....mummy ma ta yafe ma ka kuma kaga ta daina kukan.... idan kai kanayi kuma bazamu je Makkah da Madina da kai ba mu da Mummy ka'dai zamu tafi abin mu".
Murmushin 'karfin hali Deen yayi mata sannan yace " Allah albarkaci rayuwar ki...ya sanya haske ya kasance abokin tafiyar ki....Allah ya tashi kafa'dun ki mama na insha Allahu cikin shekaran nan sai kinje makkah koda kuwa ni bazan samu zuwa ba insha Allahu sai na cika miki burin ki kinji".
Koka'dan bai yi yun'kurin ta6a jikin ta ba dan Noor ta hana shi aikatan hakan ba kuma ya son ya sake 6ata ranta shiyasa ya tsaya iya magana.
Tambayar sa Jas ta sake yi da fa'din
"....Daddy nima ka yafe min?"
Lumshe idanu yayi yana murmushi da hawaye ya 'daga mata kai gami da fa'din " har abada bazaki ta6a yin laifi a wurina ba Baby....na yafe miki koma menene...na yafe miki uwata fatana albarkar Allah ya kasance tare da ke har karshen rayuwar ki".
Noor da ta zuba musu idanu tana kallon su ita kanta taji dadin addu'ar tasa har cikin ranta....sai dai duk da haka bata jin zata iya yafe masa abinda ya aikata mata.
Muryar Jas da taji tana fa'din " Daddy saura Mummy ma kace ka yafe mata".
" bata yi min laifi ba Baby....in ma tayi na yafe mata ".
Juyaea tayi ta kalli Noor tace " Mummy ki yafewa Daddy na kinga yana kuka".
'Ko'karin share hawayen sa ya fara sannan ya ya kalle ta da niyyar ro'kon ta gami da bata ha'kuri sai tayi saurin dakatar da shi da hannun ta gami da saurin fa'din " adana tuban ka malam, ni banda bu'kata....burina ka fita daga cikin rayuwar mu ka bar mu mu huta....wallahi Yah Deen da kasan yanda nake ji cikin raina idan na ganka ko da bazaka sake gigin kusanto inda nake ba....i hate to see u by my side....."
Hanyar waje ta nuna masa sannan ta cigaba da fa'din " barin ka ward din nan zai fiye min sassauci fiye da ganinka a gabana....dan Allah ga hanya nan zaka iya tafiya"
Kalaman tan sun masa ciwo sosai amma haka ya daure ransa bai sake zubda hawaye ba.
'Ko'karin tashi ya fara yi sai tari ya sar'ke shi harma yaci 'karfin sa matu'ka, 'kirjin sa ya dafe da yake jin tamkar zai tsage biyu inda ya rin'ka jera tarin kusan sau hu'du har sai da ya dangana kansa da bakin gadon da Jasmine take kai.
Da ya 'karayi kuwa sai ga jini a bakin sa.
kaf a idanun Noor hakan ya faru dan kokadan bata kawar da kai daga kallon sa ba, ganin jinin ne ya sanya ta saurin rintse idanu ta kawar da kanta gefe, ita kanta tasan me hakan ke nufi, amma sam bata son tausayin sa ya kamata ballantana har soyayyar shi ta rinjaye ta duk kuwa da tanajin ra'da'di cikin ranta tana kuma jin tamkar ta taimaka masa amma haka ta basar ta kawar da idanun ta tamkar bata san cewa shine a gabanta ba.