← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 211

Sashe 187

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun rasuwar Baby Jas gidan bai 'kara zama dai-dai ba, sai dai takamammai idan za'a yi masa tambaya bazai iya fa'di ga dalilin da ya kawo rushewar farin cikin gidan ba.
Amma abin na damun sa sosai...ko ranar da suka yi bankwana da Sani ma sai da yayi 'kwallah saboda tausayin sa, ganin yanda rayuwa duk ta juya mai cikin kwanaki kalilan.

*****
Sosai likitoci suka fara bashi taimako wanda kamar jira yake da shigar su asbitin ta fara tari mai azabtar wa, yi yake yi Safwan na goge masa bakin sa, idon sa guda ne ke hawaye saboda azaba, daka ganshi zaka san cikin matsanancib hali yake kuma har a lokacin hannun sa na dafe da 'kirjin sa ne.

Yana tarin idanun sa suka fara kakkafewa nan take ya yi 'dif komai ya tsaya masa.

Safwan kam rikicewa yayi sosai take ya 'daga wa likitocin hankali kan su ceto rayuwar sa dan Allah.

Sai da ya tabbatar an bashi taimakon da ta dace kafin ya nutsu ya fita daga 'dakin yana share gumi a goshin sa.

Da fitar sa sai ya ciro wayar sa sai a lokacin ma ya ci karo da tarin missedcalls in da Ishaq yayi masa, Alhaji Baba ya fara 'kira yau in yana kuka yake bawa Alhaji ha'kuri akan ya taimaka ba dan halin sa ba ya yafe masa
Yace wallahi Mu'een na matu'kar bu'katan taimako, yace ba fata ba amma a irin halin nan da yake ciki gab yake da ya rasa rayuwar sa, to me zeje ya gayawa ubangijin sa idan ya koma gare shi yana 'dauke da fushin iyayen sa, Alhaji u need to see his condition bai ta6a irin hakan ba..dan..Allah kuzo ku duba shi Alhaji..kuyi masa albishir in..kun yafe masa...".

Alhaji Baba kam sai da ya gama jin bayanan Safwan sannan ya bashi amsa da fa'din" Bani da lokacin zuwa ko'ina Safwan, abubuwa da yawa ne akai na...."
" Innalillahi wa inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, haba Alhaji, 'dan ka ne fa..? Wallahi Mu'een yayi nadama Alhaji, na tabbata bazai sake kwatanta waccen rayuwar ba..dan Allah Alhaji ka yafe masa...".
Murmushin takaici Alhaji Baba yayi sannan yace" In dai ka biyewa Mu'een kunya zai baka Safwan, kawai ka share shi, bana masa fatan abu mummuna a rayuwar sa amma sam ban ga alamun nadama tattare da shi ba".
" Alhaji ni na tabbata yayi kuma daka ga halin da yake ciki a yanzun kaima zaka fahimta da kanka...dan Allah ku tausaya masa Alhaji..nasan bazai sake kuskuren maimaita irin hakan ba".
" To ka bari zanyi tunani akai, ka kwanatr da hankalin ka kaji".
" Owk Allah bada iko..godiya muke Alhaji Ubangiji Allah ya 'kara girma".

Sai bayan gama wayar sa da Alhaji Baba kafin ya 'kira Ishaq, ha'kuri ya bashi game da rashin 'daga wayar sa da be yi ba.
Ishaq kam wannan be dame sa ba fiye da 'kaguwa da yayi yaji halin da Mu'een ke ciki.
Nan kuwa Safwan yayi masa bayani a takaice cikin nuna tsananin tausayawar sa.
Fatan samun sau'ki yayi masa sannan suka yi sallama.

Washegari Ishaq ya kama hanya, sai da ya tsaya a Shuwarin wurin iyayen Mu'een ya 'kara basu hakuri cikin lafazi mai sanyi kafin ya wuce garin Bauchi.

Shi kansa Alhaji Baban bayan tafiyar sa ya jima yana tuananin, sosai ya yaba da hankalin Ishaq, sai ma yake kara gode Allah da ya hada Mu'een abota da irin su ba dan hakan da be san inda zai javrayuwar sa ba, cuz abokai na da matukar tasiri a rayuwar mutum.
Maganganun Ishaq ne ke tayi masa yawo akan sa ya kasa manata su, shi kadai sai yayi murmushi dan sosai Ishaq ya karya masa zuciya har ma yasa shi bayyana sirrin.dake ransa game da Mu'een batare da ya farga ba wanda yasan bakomai.ne yasa hakan ba face kamalar da Ishaq ke da ita, mutun ne shi da ganin sa na farko idan.kayi zaka fahimci nutsuwar da ke tattare da shi.
Murmyshi ya sake yi cike da tsananin jin da'di yake tuno kalaman Ishaq in...." Alhaji Baba ka dube ni matsayin 'dan ka daka haifa karka yi min duba irin na abokin 'dan ka, wallahi har cikin zuciya ta nake jin ka Alhaji, ka yi min duba irin duban da kake yiwa Saif da Zaidullahi..yau ina gaban ka ne matsayin dan ka Alhaji, da wannan matsayin nake barar alfarma ta farko a wurin ka kayi ha'kuri alfarmar Annabi Muhammad (SAW) ka yafewa 'dan uwa na, kar ka dubi girman kuskuren sa Alhaji..falalar yafiya kawai zaka duba, wallahi bana samun natsuwa a duk lokacin da na tuna halin da Mu'een ke ciki, bana jin da'di, ni ban tashi da mahaifiya da mahaifi ba amma ina jin ciwon hakan har yanzu, sai dai da yake nasan ikon Allah ne shiyasa bana damuwa sosai, duk da yake naso in taso tare da su amma Allah ya riga ya kar6i rayukan su tun kafin girma na dan ya fini son su, hakan ya sa na tsani inga ko 'karamin sa6ani ya faru tsakanin 'da da iyayen sa, balle Mu'een da nake jin sa tamkar 6arin jiki na, Alhaji idan kana fushi da Mu'een tamkar da mu duka kake yi domin duk rashin walwala ke ziyartar mu, ka ji 'kan mu Alhaji ka yafe mana ko farin cikin mu zai cigaba da wanzuwa, da kanka nasan bazaka ji da'di ba ace duk yaran ka na cikin 'kunci dalilin mutum 'daya tak...
da kaina nasan Mu'een yayi kuksure amma Alhaji dogon fushin nan sake 6ata lamari zaiyi ba ze gyara ba, Alhaji idan har ka yadda cewa nima 'da nake a wurin ka dan Allah a karon farko ka yi min wannan alfarman ka yafewa 'dan uwa na laifukan da yai maka, hakan ka'dai ya ishe ni yadda cewa mahifina nanan a raye bai mutu ba...".
Idanu Alhaji Baba ya lumshe sannan ya bu'de su akan fuskar Ishaq, tausayin sa ne sosai ya kama shi, ha'ki'ka maraici abu ne mai ciwo sosai, bai ta6a sanin Ishaq maraya bane ba sai yau da ya furta masa.
Yana cikin tunanin yaji Ishaq na sake fa'din" Dan Allah Alhaji kayi ha'kuri kace ka yafewa Mu'een..nayi maka al'kawarin bazai sake maimaita irin wancan kuskuren ba, idan ma ya sake faruwa ka tuhume ni..."
Ajiyan numfashi Alhaji Baba ya sau'ke yana jin wani sanyi da farin ciki na ratsa masa zuciya..duban Ishaq ya tsaya yi na tsawon sakanni sannan yace da shi" Matso nan Ishaq zo kusa da ni".
Matsawa Ishaq yayi kamar yadda Alhaji Baba ya umarce shi.

Kansa Alhaji ya shafa yana jin 'kaunar sa na ratsa masa zuciya.

Ishaq 'kasa yayi da kansa cikin girmamawa, Addu'a yake a zuciya Allah yasa Alhaji Baba kar ya 'ki amincewa.
Yana cikin wannan tunanin yaji Alhajin na ce da shi" Kasa naji da'di sosai Ishaq, ka dasa min sabon hpoe a zuciya ta, yanzu ina jin kaina ne matsayin mahaifin 'ya'ya har guda biyar...rabon da naji ni cikin irin wannan farin cikin har na manta, Allah yai maka albarka Ishaq, Allah ya ji 'kan mahaifan ka.
Naji da'di sosai da ya kasance kana daga cikin makusantan Mu'een kasancewar ka abin ayaba a kuma yi alfahari da shi, hakan ka'dai ma baiwa ce..kuma ngd wa Allah kan hakan..."
" ko ban fa'da ba nasan kaima kasan laifin da Mu'een ya aikata ko?"
" nasa ni Alhaji, babban laifi ne ko a wurin Allah Zina na da 'dumbin zunubi..amma please ka yafe masa insha Allahu bazai sake aikata irin wannan laifin ba".
Murmushi Alhaji Baba yayi sannan yace
" Ni ban ri'ke shi a zuciya ba, laifin sa tsakanin sa da ubangijin sa ne ni ba ruwa na, na riga na sau'ke nawa hakkin, tun abaya nata nuna masa rashin dacewar hakan, na kawo masa misalai da ayoyin qur'ani kala-kala hoping that zai ji tsoron Allah ya canza halayyar sa amma Mu'een ya watsar da batu na, bana fushi da 'dan uwan ka amma bazan 6oye maka ba cutarwa da yayi wa Noor shine abinda yafi tsaya min, buri na kawai ya sakam min ita ne yaje can da rayuwar sa ina so zan aura mata wanda zai bata farin cikin rayuwa, someone that ll lead her to jannah ba irin shi da ke sata cikin 'kunci ba, da ya bata takadda shikenan ba wani fushi tsakani na da shi...ka daina damun kanka kaji ko?"
" To Alhaji..thank u so much...Ubangiji Allah ya 'kara nisan kwana".
Kai Alhaji Baba ya jinjina masa yana murmushi mai 'kayatarwa.

Bai da'de tare da shi ba yayi masa sallama yace zai je gida wurin Ammi daga nan zai wuce dan yana kan hanya ne.
Alhaji Baba yace bakomai duk lokacin da yake son ganin sa zai sanar da shi.
Sallama suka yi bayan ya ciro ku'di masu 'dan nawi ya mi'ka mai.
Ishaq 'kin amsa yayi sai da yaga ran Alhaji Baba na shirin 6aci kafin yasa hannu ya amsa yana godiya ya tafi gida wurin Ammi.

Itan ma Ammi duk batun ta kusan 'daya ne da Alhaji Baba burin su kawai wai ya saki Noor.

Shi kam Ishaq sam bai ga laifin su ba, amma sai yake jin fargaban tunkaran Mu'een da wannan zancen.

Haka dai itama yayi mata godiya ya kama hanyar garin Bauchi, bai isa da wuri ba kuwa sai da yayi dare sosai a hanya, ko da yaje ma bai samu ganin Mu'een ba sai washegari.

Kwanan sa biyar tare da shi kafin ya koma Borno ganin kamar jikin da 'dan sau'ki amma har ya tafin ya kasa sanar da shi batun da suka tattauna da iyayen sa.

Gani yake kamar abin zai 'kara sashi cikin mawuyacin hali ne shiyasa yayi shiru kawai.

Da kansa yayi ta neman layin Noor da tunanin bata baki akan tayi ha'kuri ta ce da su Alhaji kar su raba su amma ya kasa samun ta sam, dole ya ha'kura da 'kiran nata ya sake tunanin wata mafitar.

Tausayin Mu'een kuwa daram ya dasu a zuciyar sa, dan kullum idan ya bu'di baki zancen iyayen sa zai yi maka, sai su Uncle Ja'afar da Noor matar sa.
Chapter 187 · 0% Book details