← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 211

Sashe 57

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Karfe biyar da rabi suka baro lambun shida Alhaji, da 'kafa suke tafiya suna 'dan ta6a hira anan Alhaji Baba yake 'kara yi masa Nasiha game da rayuwar mu ta yanzu, inda ya ringa buga mai misalai da dama musamman ma irin wancan abinda ya ta6a faruwa da shi har ajiyayyen ciwon sa ya tashi masa......Alhaji yace " ina fa'da maka hakane dan nasan ba kowani lokaci bane zangan ka har in gaya maka hakan, saboda bama tare da kai, yanzun ma nasan da kasamu makarantar akan lokaci nasan da zai yi wuya mu ganka...."
Sai yace
" Haba Alhaji Baba..ai da da yanzu ba 'daya bane, zan dinga zuwa akan lokaci insha Allahu....ni dama zanyi aure na anan garin ai kaga babu batun rabuwa da ku ko?"
Ya 'karashe maganar da tsokana.

Murmushi Alhaji Baba yayi tare da fa'din " aure a garin nan....?"

Kai ya 'daga masa sama yana murumshi tamkar wani yaro...sai Alhaji yace " a ina kaganta dan nasan ka ga wacce tayi maka ne shiyasa ka fa'di haka".

" Ai kaman kasani Alhaji...dama inaso in baka amanar ta kafin in tafi..."
"Da yake ni kakan kane ko...?"
" ah ah ni dai dan Allah Alhaji Baba kar kabari a aurar da ita ma wani, ina kammala karatuna zan dawo ka nema min auran ta ".

" Baka da kunya Muhammad, ni ne zan yi ma gadin wacce kake so?"

Shagwa6e fuska yayi tare da rausayar da kansa gefe yace " please....please Alhaji... in ba haka ba kuma to kawai ka tanadi likkafani ka ajiye tun yanzu!".

" Ja'irin yaro...mu ai namu shan gumba ne kawai".
" um-um dai Alhaji gara asha biki da gumban nan, ai nasan kaima baka so in mutu tun yanzu ko ba haka ba?"
Alhaji 'yar dariya yayi sannan ya sake fa'din
" idan tazo na isa in hana ne Muhammad?"

" Allah yasa mu dace...amma ni dai please Alhaji na baka amana idan ka'ki kuma zanje in bawa Ammi na kawai".

" Da yafi maka"
Alhaji ya fa'di cikin nuna halin ko in kula....Zabura Mu'een yayi yace " haba Alhaji wai da gaske kake yi ne....ni fa gaskiya kai nake so saboda kai zaka fi kulamin da kyau...kaga idan kaji za'a min sakiyar da ba ruwa sai ka shigar da magana ta kawai amma Ammi ai kullum tana gida ina zata san meke faruwa".

Shi kam Alhaji Baba sosai yake mamakin jin wannan zancen daga bakin Muhammad 'din sa....dan ya tsokane shi sai yace " to ka bari sai munyi magana Ja'afar".

" Subhanallah "
ya furta da sauri har da kame bakinsa " Uncle Ja'afar dai?
Cikin shagwa6e murya ya 'kara fa'din" Haba Alhaji Baba kanason in sha masifa ne hala, ai kasan halin Uncle Ja'afar ba sau'ki kuma wannan fa sirrine tsakanin mu dan Allah be serious mana".
Ya 'karashe maganar kamar zaiyi kuka.
Alhaji sassautawa yayi ganin dagske fa yake sai ya tambaye shi
"...to wace yarinya ce?"
Cike da farin ciki yace " yess...." harda watsa hannayen sa.
Da sauri Alhaji Baba ya kalle shi sai yace " to na fasa"
Tuni ya nutsu yace
" ah ah no yi ha'kuri Alhaji......sunan ta Amina amma anace mata Nanne...mahaifin ta kuma wai sunan sa Malam Mamman, gidan su na can 'kasan...ya 'karashe da yiwa Alhaji kwatancen gidan mu.

_Comment,Vote nd Share please_ 👏🏻

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *29*

Cikin muryar kuka Hafsat tace " wallahi jinayi tamkar yanzu ne abin ya faru....ha'ki'ka mutuwa aya ce....Allah yaji 'kan Nanne..Allah haskaka 'kabarin ta...Allah ubangijin ka kyautata namu 'karshen"

" Amin yah rabbal Alameen".....Nuree tace gami da juyawa ta kallo 6angaren da Jas ke kwance.......Sannan a hankali ta cigaba da fa'din.
" Allah sarki Rayuwa....ban ta6a sanin na sha'ku da Nannen mu ba har sai da na daina ganin ta, zazza6i me zafi ne ya kamani.....ga sunbatun sunan Nanne da ya kasa barin baki na....ban kuma fasa kuka ba.

     Har akayi sati uku da rasuwar Nanne ban samu natsuwa ba, na kan yawaita tambayar Ummahn mu cewa " dagaske Ummah bazan kara ganin Nannen mu ba?....babu ranar da bana yin irin wannan tambayar tamkar kullum ba amsa iri daya ake bani ba amma gani nakeyi kamar watarana maganar bakin su zata canza...acemin zata dawo.

Nafi jin kewar ta idan na saka abinci a gaba na domin ada tare muke cin abinci ni da ita....muyi fa'da muyi da'di.

*****
Akwai watarana bayan rasuwar Nanne da kusan sati shida.... dan har an fara mantawa ma da rasuwar, tuntuni gida yayi shiru mun koma rayuwa mu ukun mu, Baban mu sai ni sai Ummah ta, to shi Baban mu ba yini yake agida ba sai yamma yake dawowa wataran ma har sai anyi maghrib, ni da Ummah ta ka'dai muke yini tare.....haka kuma tun rasuwar Nanne Ummah bata 'kara yin sana'a ba har yau....bama ta da niyyar 'karayi.

Lokacin da hantsi ne ina zaune 'kar'kashin bishiyar mango da ke cikin tsakiyar gidan mu.... Ummah ta naga ta fito daga cikin 'daki hannun ta ri'ke da wasu kayan sawan Nannen mu.

Kamar da gaske nace da ita " Umnah ina za'a kai kayan?"
Sai tace zan bayar ne Hudah babu amfanin ajiyar su ai ko?"
Tayi maganar tana 'ko'karin cusawa a leda.

Kuka kawai na sanya gami da tasowa na iso inda take....ina kuka ina fa'din " Ina zata kai min kayan Nanne, nace ta ajiye mata abin ta...in ta kyautar to in Nannen ta dawo ita me zata saka?".

Kuka nakeyi sosai wanda sai da na saka Ummah ma kuka, 'daki ta kona ta barni da kayan a waje na tattarasu gabana ina kukan da ambatan Nanne.

Ummah bata ta6a barmin koda 'dan kwalin bane da sunan inyi amfani dashi dan gudun rigima ta amma duk da haka bata tsira ba.

  Sallamar Ammi naji a tsakar kaina ban kula ba sai na cigaba da rera kukana " Subhanallah me kuma ya faru?"
Ammi tace tare da hanzarin isowa inda nake.

Bu'dan baki na sai nace " Nanne"
Salati Ammi ta sanya gami da tallafo ni haba " Hudah wmhar sai yaushe zaki bar wannan abin dan Allah?"
Ban kulata ba inata kukana sai ta sake fa'din " bakowa a gidan ne"
?"

Ummah dake tsaye daga cikin 'daki ne ta fito ta faman kakkauda kanta, tayi 'ko'karin tsaida kukan ta ne tun sanda taji shigowar Ammi, amma duk da haka kallo 'daya zakayi mata ka fahimci cewa tayi kuka.

Tabarma ta 'dauko ta shimfi'da wa Ammi sannan a hankali tace " barka da zuwa".

Kallon ta Ammi  tayi gami da fa'din " yauwa".

Bata 'kara ce da Ummah ta komai ba kawai ta dawo da hankalin ta gareni.

" Saurare ni please".
Tace dani....gami da gyara min zamana...." kalli nan"
Ta fa'da bayan ta nuna Ummah " waye wannan?"
Ta ce da ni tana kallon idanuna...cikin kuka nace " Ummah ta"
Banji ba ni share hawayen ki tsaida kuka ki fa'da da kyau inji.

Kamar yanda ta fa'da haka nayi ganin kamar yanayin ta ya canza zuwa 6acin rai.

Sake tambaya Ammi tayi kamar yanda tayi da farko nima sai nace " Ummah ta ce"

" Kin fison kullum ki ringa sanyata kuka ko?"
Sai na jijjiga kaina.
" Toh me yasa kullum kike 'daga hankalin ta? Da wanne kike so taji, da alhinin rashin 'yar uwar ki ko kuma da fitinar ki?...Hudah ke ko tausayin ta ma bakiji...dubi fa duk yanda ta lalace saboda tsaban fitinar ki, in dai mutuwa ce ai kema wataran zaki mutu a daina ganin ki...kanki aka fara ne?"

Masifa Ammi ke min sosai yayin da Ummah ke 'kara share hawaye...abin nawa duk ya isheta, ko ita da ta haifi Nanne iyaka damuwar ta ta tsaya ne tun bayan sati guda da rasuwar amma saboda ni har yau mutuwar ta kasa barin zuciyar ta....

Ni kuwa gani nake kamar fa'dan da mukayi ne ya sanya ta yin fishi dani ta tafi abinta shiyasa kullun nake ganin kamar 'karya sukeyi Nannen mu zata dawo watarana...duk kuwa da cewa kowa bai bani assurance 'din dawowar tan amma na kasa gane cewa idan an mutu ba'a dawowa har abada an rabu kenan.

Kuka na fara da jin masifar Ammin ga kuma Ummah ma da ta ke share hawaye a gefe.

'Dan 'karamin tsaki Ammi taja sannan ta kalli Ummah tace " yarinyan nan fa abin nata gaba yake  yi...ba kuma barin ki zatayi ki nutsu ba  a gidan nan...barin tafi da ita ta 'dan kwana biyu a wurina may be zata 'dan warware in bata ganin ku...."

Ummah bata ce da Ammi komai ba....amma haka kawai sai taji wani iri abin yayi mata gatsau, cuz bata zaci jin hakan ba, ya zatayi da zaman gidan ita ka'dai kafin Hudahn ta dawo"
Ummah ta tambayi kanta.

Ammi kuwa tsaye ta mi'ke hannu na cikin nata, bata ko nemi yardar Ummah ba kawai tace " idan mahaifin ta ya dawo ki sanar da shi cewa tana wurina dan Allah".
" Toh"
Kawai Ummah ta iya cewa daga nan Ammi ta jani 'kofar 'daki na saka takalmana 'dan kwali ne kawai a kaina sai doguwar riga a hakan muka nufi 'kofa " sai anjima" Ammi tace da Ummah yayin da Ummah ta amsa
" uhmmn" daga nan muka fice.

Ko bayan fitar mu Ummah bata tashi a wurin da wuri ba, tunani kawai takeyi, tana ga kamar ka'dai cin zai mata yawa, ita kanta halin da nake matan ya isheta amma sam bata ta6a kawo rabuwar mu face addu'ar data 'dauri aniyar yimin koda yaushe.

A hankali ta mi'ke gami da fa'din "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi".

Koda Baban mu ya dawo ta fa'da masa ma bai ce komai....irin kslmar da Ummah ta fa'din nan shima ita ya fa'da daga nan suka cigaba da harkokin gaban su.

Washegari aka kawowa Ummah ta Ummi 'yar gidan Addah ta ta fari....dan ta ringa 'debe mata kewa kafin in dawo.
Chapter 57 · 0% Book details