Sashe 42
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai ce da ita komai ba kawai ya mi'ka mata takaddar ta.
Kar6a tayi gami da fa'din " Thanks" tare da hanzarin barin ajin yayin da ilahirin mazan ajin suka bi ta da idanu dan sosai kalar shagwa6ar ta ta birge su sa6anin Mu'een da ko akan sa ma bai sa hakan ba.
Wani dake seat 'din gaban Mu'een ne ya waigo yana murmushi yace dashi " Amma sister n kan nan da gani rigimammiya ce ko?"
" indeed".
Yace dashi a takaice shima 'din yana murmushi kamar gaske.
Tun daga lokacin sha'kuwa mai tsanani ya shiga tsakanin Mu'inuddeen da Rahma, tun Mu'een na kaucewa har yazo ya saki jikin sa da ita dan ita komai zatayi sai ta neme shi haka kuma duk abinda ya dameta gurin sa take zuwa, sosai take girmama shi matsayin yayan ta.
Tsananin sha'kuwar ta sun ne ya sanya shi fahimtar komai game da ita a haka ya fahimci cewa itan ba sosai suke zama gida 'daya da yayanta Hayat ba.
Ta kan zauna gidan kakar ta wani sa'in, yayin da wani lokaci take zama gidan Antyn ta wato babbar yar su dake aure da yaranta uku, lokuta 'kalilan nan take zama gidan mahaifin ta, bai sani ba ko wannan dalilin ne ya sanya halayyar su ta banbanta da Hayat....sam basu kama ta fuskar halayya ba bayaga jini da ya ha'da su.
Rahma sanyin hali gareta bata da jan fa'da barta dai da rigima wanda ta saba irin na shagwa6a66u sa6anin Hayatu da yake fitinanne, son rigima, ga son shiga abin da bai shafeshi ba sannan ga shi da uban rashin ha'kuri.
Abubuwa da dama ya sani game da ita sa6anin shi da bai ta6a gaya mata komai akan sa ba, banda sunan sa Muhammad da ta sani har yau bata san komai game da shi ba....haka kuma " Bross " da take 'kiran sa da shi har yau bata fasa ba.
Da gaske yawanci sun 'dauka cewa 'kanwar sa ce blood sister kamar yadda take fa'da harma wasu mazan kan zo wajen sa da sunan wai suna neman hanya wajen sistern sa ta fuskar soyayya, yayin da yake murmushi kawai baya furta komai kamar yadda bai jin komai a zuciyar sa koda hakan ya faru.
Kuma bai ta6a isar mata da sa'kon kowa ba, shi kansa bai san me yake ji game da ita ba, ya rasa me yasa har ya sake mata, shin saboda ta kasance 'kanwar Hayat ne ko kuwa dan sau'kin kanta?"
Sam ya rasa dalili 'daya da ya sanya shi.
Cikin haka har suka zana waec suka gama, suna fara zana Neco Rahma ta fara 'daga masa hankali da iyayin wai ita bata son ya tafi ya barta ita menene.."
Haka dai duk ya rasa kan maganganun nata.
Da abin yayi yawa ne a wautar sa sai yake ganin 'kilan hanyar 'daukan fansar sa ce tazo masa cikin sau'ki, Rahma 'kanwa ya 'dauke ta amma ya san koka'dan baya jin ta a zuciya kamar yadda ita ta 'dauke shi, dan haka zai yi amfani da wannan damar yayi wasan 'kwallo da zuciyar ta yadda zai illata farin cikin ta cikin sau'ki sannan ya barta, 'kila idan yayi hakan zaiji sau'ki cikin ransa game da abin da Hayatu yayi masa...harma ya cire abin a ransa.
Sanadin wannan tunanin ya sanya shi sakin jiki sosai da ita, yanda take nuna masa zata yi kewar sa haka shima yake nuna mata zai yi fiye ma da yanda ita take tunani, ya kan 6ata lokacin sa sosai tare da ita, ya kula da karatun ta, ya sanya ta farin ciki, duk abinda take so ya kanyi mata shi, sau tari ta kanso ha'da shi a waya da Yayan ta Hayatu amma Deen sai ya'ki amincewa ya nuna mata ba yanzu ba, a hankali ya fahimci irin shimfi'da'd'iyar 'kaunar da Hayatu yake yi mata matsayin ta na 'kanwa agare shi kuma auta duk da yake akwai 'kanne 'yan uba amma Hayat baya ha'da soyayyar da yake yiwa Rahma da kowa.
Deen sai ma yaga kamar komai na tafiya masa ne yadda ya kamata, cuz yasan duk abinda zai faru da Rahma to Hayat ne biyu da zai fi jin ciwon abin bayaga mahaifan ta.....kenan Rahma tamkar kibiya ta zame masa da zai harba ta tafi direct izuwa ga fansar ransa.
Duk shirin da Deen keyi cikin ransa Rahma bata da masaniya akai ko 'daya kuma bata ta6a tunanin akwai abu makamancin hakan cikin ransa ba.
Kafin su kaiga kammala Neco ne mahaifin su Rahma ya samu paralize, barin jikin sa na dama ya daina aiki gaba 'daya sanadiyyan hawan jini.
Ranar shi ya dinga kwantar mata da hankali yana bata ha'kuri da kalaman kwantar da hankali har ta daina damuwa sosai.
Ba 'karamin tausaya musu yayi ba dan kuwa yasan su Hayatu marayu ne mahaifiyar su ta jima da rasuwa ga shi kuma yanzun abinda ya faru ga mahaifin su.
Yanda tausayin Rahma ya shige shi har sai da ya sanya yayi watsi da dukkan mugun shirin sa, gaba 'daya sai yake jin zai iya yafewa Hayatuddeen komai ma sanadin mutunci da karamci irin na Rahma, ga kuma tausayin ta da ya kamashi.
Jikin mahaifin su kuwa babu sau'ki sam sai dai ace Alhamdulillah, haka aka dawo dashi gida aka kwantar likita na zuwa duba shi, rayuwar kenan dama, shiyasa ake so ka mori lokacin ka kafin abubuwa sufi 'karfin ka ta yadda bazaka iya jayayya da su ba, duk wani izzar da 'kafafan ka gadarar ka lafiya ce, idan babu ita haka zaka zauna komai sai dai kaga anayi amma idan Allah bai so ba ko tankawa baka isa kayi ba balle har ayi da kai, hakan ma idan ya barka da numfashi kenan, idan kuwa yaso sai ya zare ranka kana ji kana gani baka isa kace miye dalili ba, haka zaka tafi ka bar duniyar daga kai sai ayyukan ka, babu dukiyar, babu gadara, babu izzah balle 'kafafa, duk ka barsu anan.
ALLAHU AKBAR RAYUWA KENAN....
ALLAH UBANGIJI KA BAMU LAFIYA MAI AMFANI, KA TSAREMU DA AIKATA MUMMUNA, YAH ALLAH KAYI MANA KYAKKYAWAN 'KARSHE....AMEEEN
〰〰〰
Ranar da ya gama rubuta Neco Rahma har kuka tai ta masa dagaske wai ita son shi take yi kuma bata son ya rabu da ita.
Ba 'karamin mamaki yayi ba da jin furucin nata dan bai ta6a kawo faruwar hakan tsakanin su ba.....dan duk wani shirin sa da yake yi cikin ransa ma ya jima da watsar da su.
'Kin bata amsa yayi kawai ya shareta dan ganin kamar shirme take yi, amma yarinyar ta matsa masa sosai tun baya kula ta kan hakan har dai ya fara biyeta amma bawai dan yana jin soyayyar ta cikin ransa ba.
Har suyi graduate suka yi bankwana da makarantar Rahma bata janye kan batun soyayyar ta ba.
Kamar wasa sai take jan shi zuwa gidan kakar ta suna hira, baya damuwa sam dan kuwa yanzu ya gama makaranta kuma ba abokai ne da shi sosai ba balle ya dinga zuwa wurin su, itan ce dai ne abokiyar shi ita ka'dai shiyasa duk ranar da ta nemi ganin sa ya kan bar duk abinda yake yi ya shirya yaje suyi hirar su da shi sannan ya dawo gida.
Wasa-wasa soyayyar sa tayi 'karfi a zuciyar Rahma, yayin da shi a kullum yake yi mata kallon 'kanwar sa, duk kuwa da cewa ya san irin girman soyayyar da take masa amma hakan bai sa ya bata wannan matsayin cikin zuciyar sa ba, har yau bai ji Rahma ta canza daga matsayin 'kanwa zuwa wani abu daban ba agareshi.
Bai sani ba ko wannan dalilin ne ya sanya duk iya zaman da zasuiyi dashi bai ta6a jin komai ajikin sa ba ko zuciyar sa.
Rahma ce ta fara koya masa ta6a jikin junan su, misali kamar idan anyi abin dariya ta kan kwanto jikin sa tayi dariyar, wani lokaci sukan sha hannu da shi a hira, wasa-wasa har wasu lokutan ta kanyi pillow da cinyar sa idan suna zaune su biyu suna hira.
Deen bai ta6a hanata ba, duk kuwa da yasan cewa hakan ba abu ne mai kyau ba, hujjar da ya ri'ke kawai itace na cewa ai bai jin komai ajikin sa.
Hakan yasa shima ya 'kara sakin jiki da ita sosai wanda har ya zarce ka'idan addini.
Daga ita sai kakar ta suke zama agidan shiyasa idan yazo ya kan shiga har ciki ya gaida kakar sannan su fito haraban gidan ta bayan 'dakuna kan wani dakali su sha hirar su anan.
Kaka bata damuwa da lamarin su cuz ta san cewa dokar mahaifin su Rahama iya secondary ne kawai tana kammalawa auren ta zai yi shiyasa kaka bata damu da lamarin su ba, balle da take ganin yanda Deen 'din yake duk sai bata yi tunanin cewa yaro ne shi ba.
Deen na da cika ido gashi kuma da ladabi hakan ne yasa kaka tayi zaton ko manemin auren Rahma ne shi shiyasa bata ta6a taka musu birki ba.
Balle da jinyar mahaifin su Rahman ya sako ta agaba ma sai ya kasance bata zama sosai, bata nutsu bama balle ta zauna wuri guda....koda bata nan kuwa still a cikin gidan suke hirar su kamar yanda suka saba, duk bayan kwana biyu Rahma take zuwa gaida mahaifin ta, koda ta tambayi Deen cewa shi bazai je ya gaida mahaifin nata bane take sai yace mata " a ah, bazai iya zuwa ba..amma yana yi masa addu'ah kullum, bata damu ba koda taji hakan dan zaton ta ko kunyar zuwa yake ji.
*****
Akwai wata rana da kaka bata nan taje can gidan daga nan kuma zata wuce wurin rasuwa kuma bazata dawo ba sai anyi bakwai saboda 'yar uwar tace ta rasun, bayan tafiyar tata sai Rahma ta koma gidan Yayar ta kafin dawowar kakan...wacce itama taje gaisuwan amma bata kwana can ba ta dawo gida.
Kwanan Rahma biyu a gidan sai ta fara jin babu da'di cuz bata samun yin hira da Mu'een a gidan bata ma ta6a bari yaje can 'din ba dan tana tsoron Antyn nata.
Da kewar sa ta dameta sai ta shirya tace da Antyn nata zata koma gida amma gobe zata dawo.