← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 211

Sashe 82

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye ya fara yayin da ya sunkuyar da kansa 'kasa gwanin tausayi, yayin da Alhajin ya cigaba da fa'din...." Nawa ma kwata-kwata kake da har zaka lalata rayuwar ka da biyewa matan banza..ko dan kaga na barka kayi rayuwa dai-dai da mura'din ranka shiyasa kake ganin yes kana da 'yan cin kanka yanzu?....laifi ne Muhammad dan nayi maka abinda ranka kake so?, ko laifi ne dan na barka ka zauna a gida kai ka'dai kamar yadda ka bu'kata...wato gani mutumin banza shine ka shirga min 'karyar abu take zuwa amsa to ko kaina malamin dake karantar da ita ai iyaka kenan..."

'Kasa ya zube yana kuka yake fa'din " Alhaji dan Allah kayi ha'kuri ka yafe min...wallahi ba nufi na kenan ba..."

" Shut-up da Allah munfukin banza...hala ka manta ni ne na haife ka...ni zaka yaudara da kalaman ka Mu'een...?"

Ammi ce tayi saurin isowa gaban sa tana tambayar" wai me ke faruwa ne Alhaji?.
Bai amsa ta ba sai ya koma kan kujera ya zauna Ammi sai ta bishi da idanu..ita kam mamaki duk yabi ya cika ta, a bai-bai take fahimtar maganar ta su.

Ajiyan zuciya Alhaji ya sau'ke bayan ya zauna 'din.

Kallon Yah Deen ya sake yi da har yanzu yake tsiyayar da hawaye, wannan karan cikin natsuwa ya ce dashi " Waye mahaifin ta kuma a ina yake ka sanar da ni?"

Baya so ya sake wasa da hankalin Alhajin dan haka sai yace " Mahaifin ta ya rasu".
Ammi kam kallon ta take ta rarrabawa tsakanin su sun 'daure mata kai gaba 'daya.

Alhaji kam cewa ya sake yi " Sunan sa na tambaya".
Kansa 'kasa ya amsa da
" Alhaji Hamza Ar'kilah".

Alhaji na jin haka ya tashi tsaye tare da 'daukan hular sa ya yi waje...Ammi kam da idanu ta raka shi har ya 'karasa barin parlourn sannan ta samu damar zama bisa kujera itama cikin tashin hankali.

Yah Deen tasowa yayi ya tsugunna gaban ta tare da kwantar da kansa bisa cinyar ta yaci gaba da kuka kamar wani 'karamin yaro.

Bata iya tace da shi komai ba har sai da ta dai-dai ta natsuwar ta kafin ta 'dau hannu ta 'dora bisa kan nasa dake jikin ta..." wai me yake faruwa ne Muhammad kaina ya kulle na kasa fahimtar komai...me maganganun Alhaji suke nufi?"

'Dago kansa yayi da raunin murya yace " Ammi dan Allah ki bawa Alhaji ha'kuri, Allah ba laifi na bane...ita ce take zuwa wuri na, sau tari na kan mata magana amma bata ji haka duk lokacin da ta ga dama zata 'dauki hanya tazo batare da ta sanar dani ba sai dai in ganta....to ya zan yi Ammi?... kuma babu komai tsakani na da ita kawai fa makarantar mu ce 'daya....shi kuma Alhaji yana zargin wata ala'ka ce daban a tsakani na da ita".

Hannun Ammi yayi saurin kamowa yace" Ammi please ki bawa Alhaji ha'kuri ya fahimce ni, abinda yake zargin bashi bane...kuma nayi al'kawarin daga yau insha Allahu bazata sake zuwa ba".

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻 ~MASOYA NA INA GODIYA SOSAI~ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *41*

Ammi 'dayan hannun ta ta 'dago ta shafa sumar dake kwance a kansa, cikin sanyin murya da kulawa tace da shi" ka kwantar da hankalin ka in dai ka tabbatar iya abin kenan kar ka damu, babu abinda zai faru, shima Alhajin ransa ne ya 6aci shiyasa amma zan masa magana insha Allahu zai sau'ko".
Kai ya jinjina mata alamar gamsuwa da maganar ta sannan a hankali Ammi ta kamo hannun sa ta mi'kar da shi tsaye, idanun sa jajazur kamar wanda ya yinin kuka.
Ammi ce tace da shi" je ka huta maza ka daina 'daga hankalin ka".
Bai 'kara furta komai ba kawai ya kama hanyar fita daga parlourn yayin da Ammi tayi zugum tana tunanin ma'kasudin zancen, ita a ganin ta ai laifin duk na yarinyar ne tunda ita ke zuwa wajen sa ba shi ke binta ba, toh me yasa laifin zai zama nasa shi ka'dai kuma?
Cikin ranta ta gama kudurta cewa zata fahimtar da Alhajin gaskiyar lamari kamar yadda Yah Deen ya bayyana mata, kar yaje yayi fushi da 'dansa a banza bacin ba shi ke da laifin ba...( a ganin Ammi kenan).

*****
      Bangaren Alhaji Baba ba kuwa da fitar sa bai zame ko'ina ba sai gidan gona, ransa a matukar 6ace yake, duk komai ya jagule amma haka ya danne kawai ya shiga tunanin mafitar da ta dace da matakin da ya kamata ya 'dauka tun kafin abin yazo yafi 'karfin sa.

Har cikin ransa baya zargin Mu'een da aikata mummunan aiki makamancin alfasha, amma bai san meyasa ba sam zuciyar sa ta kasa amincewa da abinda Mu'een ya sanar dashi, ya kasa amincewa da ala'kar sa da wannan yarinyar, dole yasan akwai wani sirri a 6oye dake tsakanin su wanda bakowane ya sani ba, rashin cikakkiyar shaidar zahiri ne ya sanya  shi ya yadda ba komai 'din kamar yadda Ma'een ya fa'di, sai dai hakan bashi zai hana shi cigaba da bincike akansu ba, matsayin sa na baligi kuma cikakken namiji baya so ace ya saba da ke6ancewa da mata tun yanzu, koma dan gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, ita Zina kusantar ta ma Allah ya hane mu da yi balle aikata ta gaba 'daya, sannan matu'kar kana so imanin ka ya cika dole ne sai ka gujewa alfasha tun kafin faruwar ta ba, ba wai sai ya faru kazo kana dana sani ba bacin idan an aikata ba'a iya goge shi sam shiyasa gara ya yiwa tukfar hanci ya kare daraja da mutuncin ahalin sa tun lokaci bai 'kure mai ba.

Tunanin hakan ne yasa shi yanke shawarar nemawa Mu'een auren ta, cuz in dai har zata iya barin garin da iyayen ta suke matsayin ta na 'ya mace ta taho gurin sa to dole akwai wani 6oyayyen abin...hujjar haka kawai ya ri'ke, kuma ta gamsar da shi, babu mamaki cikin su zuciyar 'daya na son wani ko kuma ma duk ya kasance suna son junan su Yah Deen kawai ke 6oye masa da fa'din course mate 'din sa ce ita.

Bai sake bi ta takan Yah Deen ba, kuma ko da Ammi ta fara mai magana ma bai wani jira ya gama sauraren ta ba kawai ya dakatar da ita da fa'din...." Ta yi addu'ahn tabbatuwan Alkhairi kawai, idan ya gama shirya abinda zaiyi insha Allahu zai sanar da ita komai".
Abinda yace da ita kenan wanda hakan yasa dolen Ammi taja baki tayi shiru amma abin na nan cikin ranta...da ta tuno yanda Mu'een ya bar gidan kuwa sai ta sake shiga tashin hankali, hakan ne ya sanya ta saurin sake fuskantar Alhajin kana tace " Amma Alhaji please kar kayi fushi da shi,  kasan fushin iyaye ba alkhairi bane ga 'ya'ya, musamman ma shi Mu'inuddeen 'din karka ga yanda ya 'daga hankalin sa".

Takaitaccen murmushin takaici Alhaji Baba yayi yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar hannun sa yace da ita " Ni banyi fushi da shi ba, garga'di ne kawai nayi masa saboda gaba".

Ammi bata sake magana ba cikin ranta ta furta" Allah ya kyauta" daga haka bata 'kara fa'din komai ba.

*****
      Husnah ma wannan karan ranta ya 6aci sosai da abinda Tah Deen yayi mata hakan ya sanya ta shareshi, kwata-kwata bata neme shi ba, da kuma ta tuna kwanaki 'kalilan ne suka rage musu su koma school hakan sai ya sanyaya ranta, tasan koma menene da sun koma school za'a wuce wurin shikenan.

    Wannan tunanin ne ya sanya ta sakin ranta ta cire damuwar dake zuciyar ta ta cigaba da rayuwa.

Yayin da Yah Deen kuwa koda wani lokaci zuciyar sa cike take da tsoro da kuma fargabar irin matakin da Alhaji Baba zai 'dauka a kansa, zaton sa ma ko zai hana shi zama a gidan ne kwata-kwata ko kuma ya hana shi komawa school, amma ga mamakin sa ko ta kan sa Alhaji Baba bai sake bi ba...balle yace ya rufe gidan ya kai keys 'din gida.

Shikuwa fargabar tunkarar sa yake yi a wannan halin, sannan har a lokacin ya'ki kunna wayar sa saboda kar Uncle 'din sa ya 'kira shi yaji yanayin da yake ciki yai masa titsiye, cuz ya san halin Uncle Ja'afar muddin ya san abinda yake aikata bazata yi masa da'di ba.

Rashin jin komai daga aalhaji game da batun barin gidan ne ya sanya shi tunanin 'kila makaranta ce Alhaji zai hana shi zuwa kuma hakan ya barwa ransa.

'Bangaren Ammi kuwa da taga shiru bai le'ko su a gida ba har kwana uku sai hankalin ta ya fara tashi gashi bata samun wayar sa, and su Saif ba sannan balle tasa su dubo mata shi, babu kuma wani 'kwakkwaran aboki nasa 'daya da tasani agarin balle tai 'kiran sa ta tambaye shi abin sosai yai mata karan tsaye a ma'koshi.

Ni ce ka'dai a gaban ta wadda take tunanin zata iya turawa can amma kuma ranta bai kwanta da hakan ba sam.

     Ran cikar kwana na ukun ne ta 'kudira cikin ranta cewar koma menene zai faru ayau 'din nan sai ta ga 'danta da iznin Allah, ko ita da kanta zataje ta dubo ya yake tunda wayar sa ma har a lokacin bata tafiya.
Chapter 82 · 0% Book details