← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 211

Sashe 88

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Dan 6ata rai yayi ka'dan jin tsawan da Uncle J ya daka masa, dan yaja hankalin sa ya sanya cike da shagwa6a yace" Uncle nima fa ban sani ba".
Kwafa yayi tare da fa'din
" Baka san me ba?"
Sai yace
"Abinda kake magana akai 'din".
Ya bashi amsa da sauri ganin kamar ya dan sauko.
Sai dai Uncle Ja'afar a tsawace ya sake fa'din
"...Dan ubanka ba kai ke neman auren bane da zaka ce min baka san komai akai ba?"

Manyan idanun sa ya zaro waje da jin cewa wai shi yana neman aure....bai iya 6oye mamakin sa ba a fili ya ce" Ni kuma neman aure Uncle..a ina?"
"...Raina min hankali kaji ai dama ka saba...hala yanzun ma cewa zakayi Alhaji sharri yayi maka ko?"

Wani tashin hankali ne ya ziyarce shi marar misaltuwa...maganar da Uncle J ya fa'di 'din sosai ya tayar masa da hankali, kuma wai Alhaji ne ya fa'di masa, to shi yaushe sukayi haka da shi dan Allah, yaushe yace yana neman aure?, babban abinda ya guda kenan wato sanya bakin Uncle Ja'afar cikin maganar cuz ya san 'kaniyar sa zaici bada wasa ba shi ba ai masa wargi, to ma ta ya zai iya 'karyata maganar Alhaji Baba gun 'kanin sa kan wannan batun fisabillahi....
" Tambayar ka nake yi fa Mu'een kayi min shiru".
Maganar Uncle J ce ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi.

Cike da da damuwa da jin haushi Yah Deen yace" Ni dai dan Allah Uncle help me, wallahi bansan da maganar nan ba ni kam sai yanzu, 'kilan ba mamaki auren dole Alhaji yake shirin yi min".
Uncle cewa yayi
" Banson munafurci ni..."
Yah Deen ma sai yayi saurin taran bakin da fa'din" Please Uncle ni dai kazo ka ro'ka min Alhaji ya bar wannan batun nifa ban ce ina son aure ba, hasalima ni ban nemi auren 'yar kowa ba...Allah in kazo zan ma ka bayanin komai da ke faruwa...ni dai help me".
Ya 'karashe maganar kamar zai yi kuka.

Uncle J kam tunanin sa gida biyu ya kasu, sai ya rasa wani 6angare ne yafi rinjaye, jin yanda Yah Deen yayi maganar ya sanya shi ta shin farko ya yadda da batun sa sannan ga Alhaji Baba ma ba zai iya 'karya ta shi ba.

Ji yayi dama a kusa yake da a yau 'dinnnan ba sai an kwana ba zai je a warware wannan maganar tun kafin tayi 'karfi.

Duk da haka bai yi 'kasa a gwiwa ba, take ya shirya cikin ransa cewa kafin 1week 'din da Alhaji Baba ya fa'di dole zai je su ha'du.

" Zanzo nextweek insha Allahu".
Haka kawai ya iy furtawa a fili ga Yah Deen 'din dake ma'kale da waya a kunnan sa yana sauraro... sannan ya yanke wayar kowa zuciyar sa cike da tunani.

   Haka Yah Deen ya 'karasa masallaci ya gabatar da sallar maghrib cikin jam'i bai taso ba sai da ya tsaya yayi addu'o'i masu tsayi akan auren da yaji wai ana shiryawa akan sa, tsoron sa kar Alhaji Baba yace Husnah zai aura masa..yace in kuwa haka ne da ya shiga bakwai ba ma uku ba, wannan dalilin ka'dai ya sanya shi kai kukan sa wurin mahallici akan cewa kar Allah ya sa auren sa da Husnah ya yiwu in dai da ita ne Allah ubangiji  ya tarwatsa auren.

Inma ya zama dole sai Alhaji yayi masa auren ne to ubangiji Allah ya musanya masa da wata mafi alkhairi.

Zai iya zaman aure da kowa koma wacocdb amma banda Husnah, sam ita kam bai jin zai iya rayuwa da ita matsayin matar sa....(ni kuwa nace kaji ja'iri kamar ba shi ne ya 6ata mata tarbiyya ba).

Bai iya ya bar masallacin ba har sai da ya idar da sallar Isha'i, nan suka ha'du da Alhaji Baba a masallaci suka yo gida tare kamar yadda suka saba.

Sai dai yanzu babu wannan rahar da Alhaji Baba ke yi musu duk sanda suke tare da shi, to ada 'din ma ko shi Alhaji bai yi musu hira ba Yah Deen kan ja shi da hirar yana 'dan takalo shi tamkar kakan sa, amma yanzu kam shiru kana ganin su zaka san da bambamci cuz tafiya kawai suke yi kowa da abinda ke cikin ransa, har gara ma Alhajin ya kan 'dan tambaye shi abu jifa-jifa har suka isa gida.

A palour duk suka zauna nan Ammi ma tazo ta same su.
Gaida Ammi yayi sai dai tana jin muryar sa ta fahimci ba dai-dai yake ba, take sai tace" Me ke damun ka?"
Tayi maganar tana kallon sa.
" Headache"!
Ya bata amsa a takaice yana me sakin 'dan 'karamin tsaki.

" Allah ya sawwa'ka..kasha magani ne to?"
Tace tana duban sa da kulawa.
" Zan sha idan na koma".
Kai ta jinjina tare da mi'kewa ta gabatar musu da dinner ta kuma 'kwalla 'kiran suna na.

Kafin in fito ma har sun isa ga dinning 'din sun zauna, da fitowa ta kuwa ganin su uku ne ya sanya na isa na zaune raku6e gefen Ammi kamar wata ba'kuwa...Ammi kam bata kulani ba da yake tasan abinda ke sani yin hakan ba ya rasa nasaba da wanzuwar Yah Deen a wurin.

Alhaji Baba ne yace dani" Ba zaki dai na wannan ra6e-ra6en bako Uwata, maza saki jikin ki ki ci abinci".

" Hmm".
Kawai Ammi tace tare da karkatawa ta kalle ni sai na sake du'kar da kaina.

Sai da ta gama zuba min abincin kafin tace dani"  bismillah"
A hankali na kai hannu na na wanke kafin na janyo abincin gaba na, har a lokacin Yah Deen bai ko kalli inda nake ba balle in san cewa ya san da zama na, a hankali na 'daga kaina na kalle shi ganin bai ma san da ni wurin ba ne ya sanya ni fara cin abincin a hankali.

Shi kam bai fi hannu uku yayi ba ya kawar daga gaban sa tare da 'dauraye hannun sa yaja baya.

Babu wanda ya kula shi cikin Ammi da Alhaji nima kuwa kaina 'kasa ban kuma kallon inda yake ba, sai dai har lokacin na kasa sakin jiki na, Ammi ne ta waigo ta kalle ni tana shirin yin magana na riga ta da fa'din " Ni na 'koshi Ammi".
" kin tabbatar?"
Alhaji Baba ya tambaye ni sai na 'dage masa kaina alamar " Erh".
" Yau abincin Ammi yayi ba'kin jini kenan".
Alhaji ya fa'di yana 'yar dariya tare da maida idanun sa kan abincin.

Ammi sai tayi murmushi kawai.
A hankali na tashi na bar table 'din cikin raina nake tunanin wannan shi kullum bai canzawa.

Yah Deen ma da yake zuciyar sa cike take da damuwa hakan ya sanya bai 'kara mintina sha biyar cikin gidan ba yai musu sallama Ammi na tuna masa shan magani yace zai sha... daga haka ya wuce can gidan da yake.

Yana kwance yana aikin tunani yaji 'karan shigowar sa'ko cikin wayar sa, da yake wayar na hannun sa hakan yasa bai 'dauki dogon lokaci wurin duba text 'din ba.

Nan ya ci karo da bank transfern ku'di daga Uncle J kimanin 40K ya tura mai.

Take ya 'kira sa yai masa godiya, anan ne Uncle J ya ji yanayin yanda muryar sa take a 'dan dusashe sai yace" Me ke damunka kuma Mu'een?"

Kamar zai yi kuka yace" Ni dai Uncle please help me out of this issue...tsoro nake ji kar Alhaji Baba ya 'daure ni".

" Ka kwantar da hankalin ka nextweek insha Allahu zanzo mu gana da shi...ina dai ka tabbatar ba kai ka nemi auren ba?"
Sai yace
" Haba Uncle ina ni ina neman aure tun yanzu?"

'Yar dariya Uncle J yayi yace " Rabu da Alhaji 'kila dan ya koma 'kauye ne shiyasa zai maka irin na su".

" Ni dai banso...Uncle please kazo da wuri".
Ya fa'di kamar zai yi kuka.
Uncle Ja'afar kuwa
" Insha Allah" kawai yace da shi wanda daga haka suka yi sallama da shi yana 'danjin dama-dama, sai dai wani 6angaren hankalin sa ya kasa kwanciya da 'karya ta mahaifin sa da yayi, tsoron kar idan Uncle J ya tunkare shi da maganar shi mai ze ce? kar dai ya bayyana masa komai cewa mata ke zuwa wajen sa shiyasa zai yi masa auren...hankalin sa duk ya kasa kwanciya ji yake tamkar ya fasa tafiyar ma gaba 'daya..amma ya san hakan ma ba wata mafita ba ce mai amfani tunda koda yana nan 'din ma bai isa ya hana Alhaji abinda yayi niyya ba.

A wannan daren sam bai iya yayi baccin kirki ba, yaso ya 'kira Husnah ya tambaye ta ko taji  wani labari amma sai ya bawa zuciyar sa ha'kuri akan kar yayi gaggawa tunda bai ji daga bakin Alhaji ba.

Washe gari da sassafe misalin 'karfe takwas ya fito, da yake weekend ne so a wajen gidan ya samu Alhaji Baba zaune yana hutawa,  anan suka gaisa ya sanar da shi batun tafiyar tasa...fuskar Alhaji babu yabo ba fallasa yayi masa fatan Alkhairi..daga nan ya shiga wurin Ammi da tunanin ko zai samu jin wani sirri game da batun auren da daga bakin ta...ni kam a lokacin ina can ina bacci na a 'dakin Ammi.

Ga mamakin sa koka'dan Ammi bata kusanta maganar ta da batun aure ba, ga dukkan alamu itama bata san shirin Alhaji akan sa ba...cikin ransa ya ayyana wannan karan kenan Alhaji Baba shi ka'dai ya ya yanke shawarar sa cikin ransa.
Chapter 88 · 0% Book details