Sashe 43
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taso tayi mamaki Antyn dan Rahama ta jima bataje gidan mahaifin su ta kwana ba dayake basa shiri sam da matar baban nasu shiyasa tafiya zama da kaka.
Antyn bata hanata ba sai dai tace da ita idan taje banda rigima dan naga kamar yau matar nan a cike take"
Antyn Rahama ta fa'di hakane saboda dawowan ta kenan daga can gidan.
Yayin da Rahma ta bata tabbacin babu abinda zai faru insha Allahu...
Jinjina kai Antyn Rahma tayi.
Cikin hanzari Rahma ta shirya ta fito bata 'dauki kaya ko kala 'daya ba illa wayar ta da wata 'yar 'karamar jaka ta fito.
" kina nufin haka zakije bako kayan sawa shine har goben?"
Antyn Rahma ta tambaye ta da mamaki.
Rahma sai cewa tayi " zan biya gidan kaka in 'dauki kayana acan".
" Owk...ni dai ki kula please Rahma kinga Daddy ba lafiya gareshi ba balle ya taking side 'dinki kan abu, dan Allah karki shiga harkar kowa ko yaran nan sun miki abu kiyi ha'kuri kinji".
" To Anty insha Allahu zan kiyaye".
Tana fa'din hakan ne tana tafiya izuwa 'kofar da zata sadaka da waje.
Tana fita kuwa sai ta wuce gidan Kaka kamar yadda ta fa'dawa Anty.
Dama kuma keys 'din gidan a wurin ta yake dan haka sai ta bu'de ta shiga.
Tana shiga sai ta 'kira wayar Mu'een tace dashi yazo tana gidan Kaka.
" har ta dawo ne?"
ya tambaye ta.
Sai tace " erh " a takaice.
Batare da wani 6ata lokaci ba ya shirya ya nufo gidan Kaka, sallama yayi a bakin parlour gami da shigowa ciki.
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce* 😍
[1/4, 11:27 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
~Godiya ga dukkan masoyana na ha'ki'ka....ba sai na ambaci suna ba~ ~in kinji aranki ke masoyiya ta ce to da ke nake~ 😍
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *22*
Tafe yake bisa titi yana driving but 'dayan hannun sa ri'ke da waya yana faman trying numbern ta amma ba'a 'dagawa gaba 'daya hankqlin sa ya kasu gida biyu cuz bai san dalilin da ya hanata daga wayar ba.
Bai yi 'kasa a gwiwa wurin cigaba da 'kiran nata ba da tunanin 'kilan ko zai yi sa'a ta 'daga har sai da ya kasance ya jera mata tarin missedcalls a 'akalla guda tara....
Jifa yayi da wayar cike da haushi inda ta tafi can 'kar'kashin 'dayan kujeran dake gefen sa ta fa'da a nan.
Bai bi ta kan wayar ba kawai yasa hannu cikin suman gashin dake kansa ya ja hannun nasa zuwa baya tare da 'dora hannayen sa duka biyu bisa sitiyari ya cigaba da tu'kin da yake yi cikin k'agauta.
A waje yayi parking cikin hanzari ya fito daga motar ya tunkari mashigar gidan cikin hanzari inda ya isa har bakin parlourn gidan ya shiga ciki da sallamar sa.
Wani yaro dake zaune tsakiyar palourn yana wasa da jirgin wasan yara ne ya taso da gudu ya nufo shi yana fa'din " Uncle Hayat oyoyo!....Uncle oyoyo".
Ta 'kafa ya iya rungume shi kasancewar tsayin su da bambanci yayin da Hayat ya sa hannu ya shafo kansa gami da fa'din " yauwa my Sabir ina Baby da Basmah?"
" Lafiyan su 'kalau.... Basma tana bacci Baby kuma tana 'daki".
Sabir ya bashi amsa cike da murnar ganin kawun nasa.
Sai yace
" Owk, ina Rahma fa".
" Anty Rahma bata nan".
Hayat sai ya sake fa'din
" Anty fa?"
" Tana Kitchen".
Cewar Sabir.
Raba jikin yaron yayi da jikin sa gami da fa'din " je 'kiran min ita".
Bai zauna ba kawai ya cigaba da tsayuwa yayin da Sabir ya tafi da dan gudun sa dan isar da sa' kon Hayat.
Har Antyn nasu ta bayyana parlourn bai sani kasancewar ya juya baya ne....
" Ah ah ya haka Hayat ko zama kuma bakayi ba".
Jin muryar ta tana fa'din haka ne ya sanya shi waigowa ya kalle ta.
Da murmushi a fuskar sa ya furta " ina yini Anty"!
" Lafiya 'kalau...
Ta amsa lokacin da take shirin zama bisa kujera.....sannan ta cigaba da fa'din " ban jima da da dawowa daga can gidan ba ma ai amma kuma ban ganka ba".
Yace
"Ehh wallahi Anty na 'dan fita ne yanzun ma wani uzuri ke tafe da ni.....ina Rahma taje ne wai ina ta 'kiran layin ta tun dazu amma bata 'dagawa ".
" Ai kuwa bata jima da fita ba tace itama zata can gidan amma kafin nan zata biya gidan Kaka ta 'dauki kaya....wani abun ne ya faru?"
Ta 'karashe da yi mai tambaya tana kallon sa.
Hayat sai ya bata amsa da fa'din " Rannan tazo zata shiga gida muka ha'du na bata wasu takaddu ta shiga min dasu cuz a lokacin ina sauri ne...to kuma ina a bu'katar su yanzu kuma ban ga ni a 'dakina ba bansan inda ta ajiye ba na dudduba ban gani ba kuma na 'kira ta bata d'aga wayar".
Anty baki ta ta6e gami da fa'din
" su Rahma sarkin shirme yanzun kuma ko ina ta ajiye sai Allah".
Juyawa yayi kawai tare da fa'din " bari in duba ta gidan kakan 'kilan can ta tafi da su...."
Yana maganar ne yana tafiya izuwa hanyar da zata fitar da shi daga palourn...." bazaka tsaya kasha ko ruwa ba Hayat?"
Cewar Antyn nasu batare da ya juyo ba ya bata amsa da fa'din.... " ah ah Anty ina sauri ne".
Daga haka bai sake magana ba ya fice daga parlourn.
*****
Fitowan ta kenan daga bayi sai ta duva cikin kayan ta ta lalu6o 'yar shimi da wando ta sanya ajikin ta kasancewar yau garin akwai zafi ga kuma matsalar wuta da suke fama da shi a unguwar wanda ba dan hakan ba da zafin ba zaiyi tsanani sosai ba, ruwa ta watso ajikin ta mai d'an sanyi amma still bata ji sassauci ba....'dan karamin tsaki ta sake gami da nufar inda ta ajiye 'yar jakar da ta tazo da ita.
Wayar ta ta lalubo daga ciki wanda ta jefa ta ciki tun bayan da ta gama waya da Mu'een 'dazu.....wanda ko yanzun ma ta 'dago wayar ne da tunanin ko ya sake 'kiran ta cuz ta jima cikin bathroom 'din tasan babu mamaki ya 'kirata bata ji ba.
Sai dai madadin taga 'kiran Mu'een sai kuma taci karo da na yayan ta Hayatuddeen.
Da mamaki take duban wayar ganin tarin missedcall 'din da yayi mata.
Ido ta juya cikin ranta tace
" zanzo ma har gidan Yaya amma kafin hakan wallahi sai naga mai sanyi na...."
Tunanin Rahma ko dan ta kwana biyu bataje gidan bane shiyasa yake neman ta....dan haka take sai ta yanke shawarar 'kiran sa tace dashi tana hanya ma yanzu.
Sai dai tana shirin sake 'kiran nasa sai taji sallamar Mu'een daga 'kofar parlour.
Ai da sauri tayi gefe da wayar ta fita batare da ta ko kula tabi ta kan yanayin suturar da ke jikin ta bama balle ta tuna da 'kiran Hayat.
A haka ta bayyana gaban sa a parlourn fuskar ta cike da murmushin ganin sa.
Shi kam idanu ya lumshe a hankali gami da kawar da kansa gefe batare da ya tankata ba ya wuce kujerar da tafi kusa da shi mai zaman mutum biyu ya zauna.
Da 'dan hanzari ta taho inda yake tare da zama gefen sa kan 'kafarta 'daya yayin da 'dayar ta sau'kar dashi 'kasa.
Da smiling face tace da shi
" I thought bazaka zo ba ai dan baka bani wani response mai kyau ba 'dazun...."
Takaitaccen kallo yayi mata gami da yin baya ya jinginu da jikin kujera sannan a hankali tamkar ba zai yi maganar ba yace da ita " ina Kaka?"
Fari tayi da idanun ta tana murmushin tace " bata fa dawo ba dama...kawai nace tana gida ne dan ina so in ganka dan nasan in kasan bata nan ba zuwa zakayi ba...ni kuma Allah kwana biyun nan da ban ganka ba karka ga yanda na kasa natsuwa........".
" Shine kuma dan baki da kunya kika fito a haka ko?"
Ya tare da fa'din hakan kuma yayi maganar ne a tsare.
Jikin ta tabi da kallo wanda sai a lokacin ma ta gani ta kuma tunawa da yanayin suturar da ke jikin ta....'yar shimi ce da ba'kin skinny da yabi jikin ta ya zauna sosai.
Yatsina fuska tayi tace da shi
" Share kawai Bross mantawa nayi...kuma ma ai kaga ana zafi sosai yau d'in gashi ba wuta zanfi shan iska a hakan ko?".
Deen be sake kulata ba yayi shiru gami da kawar da kansa gefe, dole yake so ya tilastawa idanun sa barin kallon ta amma bai san meyasa yau 'din zuciyar sa ta kasa bashi ha'din kai ba.
Ido ya lumshe a karo na biyu a hankali amma still bai daina hango ta cikin runtsatstsun idanun nasa ba wani abu yake jin na fisgar sa.
" Bross meke damun ka yau 'din please?"
Yaji muryar ta ta daki kunnuwan sa cike da kulawa da marairaita.
Sai ya bu'de idanun sa ya sauke su kan fuskar ta gami da fa'din " me kika gani?"
" Kamar baka yi farin ciki da gani naba?"
" haka nace miki?"
Bata bashi amsaba kawai sai ta 'dago hannun ta ta ta6a fuskar sa da niyyar jin yanayin jikin sa cuz bata yadda cewa bashi da lafiya ba a yanda ta ganshin.
Amma ga mamakin ta sai taji jikin sa normal ba wani zazza6i yayin da Deen ya cigaba dabin ta kawai da kallo batare da yayi yun'kurin dakatar da itaba.
Baya tayi ta mi'kar da 'kafafun ta wanda hakan ya canza mata yanayi daga zama zuwa kwanciya rib da ciki sai ta 'daura kanta da hannayen ta duka biyu bisa cinyar sa.....cikin shagwa6ar ta tace da shi " dan Allah Bross ka gaya min me ya same ka....ko laifi nayi maka?"