← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 211

Sashe 152

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi har Umman mu ta 'kira ta fa'dawa, shirin tafiyar ta kuwa sai ya tashi gadan-gadan, Alhaji Baba tun kafin ya shigo gida 'yan biyun Ammi suka yi masa albishir bayan sun fito daga masallaci.

Ai kuwa shima Alhajin koka'dan be 6oye farin cikin sa ba, a fili ya ringa godiya wa Allah.

Koda Ammi tace da shi ita har ta kammala shirin ta ma Allah ya kaimu goben yace da ita yana yi mata dariyar zumu'din da take.

Sai bayan sallar Isha'i sannan Anty Zainab ta samu daman 'kiran sa, yana zaune gefen mu gama waya ta da Ammi kenan sai gashi itama ta 'kira.

Mi'ka masa wayar nayi ganin an 'kira sa, sai ya 'dauka tare da yin sallama.

Fuskar sa cike da annuri ya gaishe ta.
Tace" Alhaji Mu'een kenan manya Baban Baby, kawai sai na samu labarin wai 6eran Ammi ta haihu".

Dariya ne sosai ya kama shi wanda ya jima be yi irin ta ba dan yasan me Anty ke nufi da fa'din hakan yana dariyar yace" Ni dai kawai asamin albarka Anty...ai komai ya wuce".
Tace" Silly u, kamar ba kai ba Mu'een duk murnar new Babyn ne yau 'din haka?...to Allah raya mana ita da Albarka".

" Ameen Ameen".
Ya amsa ta yana murmushi sai tace" Bani 6eran Ammin to mu gaisa".
'Yar dariya yayi yace" Kai Anty".
" To ba abakin ka naji sunan ba?"
" Ta girma ai yanzu wancan tsohon suna ne".
Ya fa'di hakan yana mi'ka min wayar...gaisawa muka yi da ita, ta ringa yi min sannu tana min fatan Alkhairi sannan muka yi sallama.

Wallahi Yah Deen sosai yake bani mamaki yanda farat 'daya ya canza, tunda nake da shi ban ta6a ganin fara'ar sa kamar wannan lokacin ba.

Daren ranar kuwa Babyn ta ringa kuka, Yah Deen ne yayi ta 'dawainiya da ita har tausayi ya a daren, dan be wani yi baccin kirki ba, gashi ni ban san me zan mata ba kuma daga ni sai shine cikin gidan Mummyn Safwan bayan maghrib ta koma gida.

Da kansa yayi ta rainon abin sa har kusan asubah sannan suka yi bacci ya kwantar da ita kan cikin sa hatta sallah sai da ya makara ranar be yi kan lokaci ba.

Washe gari kuwa sassafe driver ya sau'ke Mummy kafin 8 na safiya ta kammala yi mana duk abinda ya dace.

Ni dai raina tas dan Ammi na tace dani yau zata iso insha Allahu, koba komai zan ga wani daga gida cuz ba 'karamin kewar su nayi ba, balle ma Ammi na da nake da tabbacin tana matu'kar 'kauna ta.

Yah Deen kuwa har mamaki yake bani irin kashe ku'di da yake yi, duk fitan sa in zai dawo gida sai ya dawo da kaya ni'ki-ni'ki koda ba'a ce da shi ana bu'kata ba, hakan ma fa kusan duk siyayyan ya kammala shi tun kafin ranar haihuwan amma duk da hakan be fasa ba kamar akan sa aka fara haihuwa.

Matar Safwan sunzo da Mimah suma muka kusan yini tare da su dan sai da suka yi sallan la'asar kafin suka koma gida suka barmu da Mummy.

Da tafiyar su basu da'de ba sai ga Ammi ta iso,  take naji farin ciki ya lullu6e ni marar misali, har hawaye nayi dana ganta saboda farin ciki, domin tunda na haihu banga kowa daga 6angare na ba bayaga shi.

Ammi ce ta cigaba da kulawa da mu shima tun zuwan ta ya huta da rainon dare Ammi ta fanshe shi.

*****
     Ranar suna yarinya taci suna Aishatu, sosai Ammi tayi farin ciki jin cewa sunan ta aka sanyawa Babyn, da kanta ta yiwa Alhaji Baba albishir 'din sunan ta da aka sanya shima yayi san barka.

Saif ne ya 'kira ni Video call wai yana son ganin Little mummyn sa, na nuna masa ita tana jujjuya hannuwa, yayi ta yabawa da sa mata albarka, shine yace min wai Zaidu Jasmine yake 'kiran ta da shi, 'yar dariya nayi nace masa ai shima Yayan naji haka ya 'kira ta dashi tun ranar da aka haife ta.

Murmushi Saif yayi yace Allah ya raya mana ita, nace Ameen thumma Ameen.

Ranar sunan da rana Anty ta 'kira Yah Deen  suka gaisa, sai yace mata ?" Sunan Babyn Aishatu.."
Tace da shi Ammi ta gaya min tun safe, ubangiji Allah ya sa mata albarka, tunda yanzu kai ka guje ni zaka bani ita ai ko?"
Da sauri yace" Anty wannan in? Gaskiya ki bari sai an samu wani".
Dariya tayi tace" wasa nake maka ma Mu'een ai yanda naji kake wannan fara'ar da ji nasan akwai 'kauna tsakanin ku".

Yace" Wallahi kuwa kamar kinsani Anty, ji nake tamkar in dinga yawo da ita...".
Dariya sosai ya bawa Anty kafin suka yi sallama.

Da Yah Deen cewa yayi wai sai dai mu cigaba da zama da Ammi a Bauchin Ammi kuwa ta'ki Amincewa, duk yanda yaso ya nuna mata baya so muyi nisa da shi Ammi 'kin yarda tayi da batun sa.

Da yaga ta dage kuma sai ya 6ullo da batun wai taya za'a yi tafiya mai 'dan nisa da Baby kwana biyu bayan suna ai wahala za'a bawa babyn.

Ammi tace" Idan zamu tafi sai ka hana kaji tunda ka isa".

Daga lokacin tafara yi mana shirin tafiya Shuwarin dolen sa kuwa ya kaimu da kansa har gida.

A gidan Ammi muka sau'ka ni dai ban damu ba dan ni ko ina ma gida ne a wuri na.

'Yan biyu kam kasa ganewa nayi shin cikin su waye yafi son Baby, dan kowa be 6oye soyayyar da yake yi mata, da an mata wanka zaki ga kowa na rubibin 'daukan ta photo.

Duk iskanci da girman kan Zaidu kawar da shi yayi ya daina yi min, sai dai inga yana yiwa wasu musamman da ya kasance yanzu ana 'dan zuwa gaida mu jin mun dawo, har masifa ranar yayi wa Saif wai yana kashe mata idanu da flash light 'din wayar sa me yasa ba zai 'dauke hasken ba idan zai mata oic 'din, su Zaidu manya  dan wai yaga idan wayar tayi haske sai tayi saurin lumshe idanu shine yake masifar.

Dole yayi kane-kane ya hana Saif yin yanda yake so akan 'daukan Baby photo.
Ammi tayi ta musu dariya tana fa'din ni dai kar a takurawa takwara ta.

Akwai lokacin da har hana Baby yake yi idan anzo ganin ta in ya kasance tana wurin sa akaje kar6o ta sai yace bacci take yi, musamman idan yaji ance ba'ki ne suka zo dan shi asalin sa ya tsani yaga ana shige da fice a gidan su.

Ko ranar da su Ummah ta suka zo ma haka yayi musu, da yake bai san su bane suka zo a lokacin, sai da Ammi ta tashi da kanta taje ta anso Babyn tana masifar" Ka bari idan ka haifi naka sai ka yiwa mutane abinda ranka ke so amma yanzu bazaka ringa yiwa mutane iya shege akanta ba, ai ko wacce ta haife ta ma tana cikin hankalin ta balle kai".

Sai yace" Allah damunta ake yi, bakya ganin da dare bata fiya bacci bane kuma duk saboda jagwalgwalatan da ake yawan yi ne".
Tsaki Ammi tayi ta taho da Babyn.

Da ta dawo ne take basu labarin irin bakin halin da Zaidu yake nunawa akan Babyn tace ko mahaifin ta iyaka abinda zai yi kenan.

Abin sosai ya bawa su  Ummah ta dariya.

Addah Maryam ma musamman tazo daga Darazau suka zo da matan Yaya Usman, matar Baban mu ma ta zo har gidan Ammi ta kawo mana Turmin zani da riga wa Baby, da yake ta dawo gida da jimawa har tana shirin yin wani auren ma yanzu.

Satin mu uku a gida sannan Anty Zee ta iso, a lokacin ma Baby harta fara wayo, _Jasmine_ mafi yawan mutane ke 'kiran ta da shi, amma 'yan biyu kan 'kira ta da Baby Jas, little Mummy, Angel, ko kuma Daddy's girl, ko wani suna suka ga dama 'kiran ta suke yi da shi...Alhaji Baba ka'dai ne kan 'kira ta da _amarya ta_ .

'Bangaren Yah Deen ma kusan duk weekend a Shuwarin yake yin ta, ko gajiya da tafiyar baya yi sa6anin da da yake 'daukan tsawon watanni bai zo ba.

Kowa yanzu ya saki ransa da shi, ana ganin kamar halayyar sa ta canza ne, yayin da mahaifan sa suka fi kowa farin ciki gami da 'kara gode wa Mahallici,  dan aganin su yanzu Mu'een ya nutsu ba kamar baya ba, ni kam bana cewa komai koda kuwa hirar ta ha'da dani,  domin a gani na babu amfanin fa'din wani abu bayan wanda su suke gani a zahiri, ko ada ma dan ban san menene so ba ban iya tona asirin sa ba balle yanzu da na san ina matu'kar son miji na ne zan fa'di aibun sa?hakan yasa sai in bisu ayanda suka 'dauki maganar har ta wuce gaba 'daya...addu'ar ce dai nima insha Allahu bazan daina ba.

Wani zuwa da Yah Deen yayi ne su Ishaq ma suka zo dole kuwa sai da aka gyara musu gidan mu dake bayan makaranta  aka yi musu masau'ki acan.

Washegarin zuwan su Ishaq sai ga Anas ma yazo shi da wani abokin sa, amma su basu kwana ba suka koma aranar,  duk yanzu sun zama manyan mutane kowa ya kama aikin sa aure ka'dai ne ya rage musu...Imran kam.ma already an sanya rana lokaci kawai ake jira yayin da Ishaq ke shirin sanya manya cikin tasa maganar auren, Anas ne dai yace shi ba yanzu ba tukunna.
Ku'dade kowa ya bayar wai asiyawa Baby riga abin ba'a cewa komai..suma da Babyn suka fita harabar gida duk suka yi photuna cikin nuna farin cikin su.

Ishaq ne yake zolayan Yah Deen wai gaskiya za'kewar tasa tayi yawa kan Babyn, ganin cewa  duk sati sai yazo Shuwarin.

Yah Deen yana dariya ya bashi amsa da fa'din" Iyalai wasa ne angaya maka? yaro bazaka san dad'in su ba sai ka ajiye naka sannan..wallahi ganin su ka'dai yana sani natsuwa inji kaina nima wani ne a rayuwa, shiyasa kaga bana iya 'daukan lokqci banzo gare su ba".
Chapter 152 · 0% Book details