Sashe 73
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Munafuka kawai, ba kina jin Ammi ke zagi na ba lokacin bakiyi kuka ba sai yanzu?"
Daga jin yanda yayi maganar zaki fahimci cewa cikin 'karfin hali yake yinta amma dan masifa da sabo da yayiwa zuciyar sa da shi ya sanya shi tilastawa kansa yin sa.
Ina so ince masa " Allah ni banji ba". amma tsoron yin magana nake yi.
"...Kuma ranar nan da kika je kina yi mata kuka 'din yankan jikin ki nayi?"
Naji ya 'kara fa'di.
Sai na jijjiga kaina alamar a a still ina hawaye.
" Na dake ki ne..ko kuma ke ka'dai na bari kika yi aikin?"
Nan ma da sauri na girgiza kaina.
"...oww wato munafurci dan ki ha'da ni da Ammi na ko?"
Da 'kyar nayi dauriyan furta
" Dan Allah kayi ha'kuri wallahi bazan sake ba...." Nayi maganar murya ta na cracking.
"...kima sake"
Ya tare ni da fa'din haka.
"Ai kin isa".
Ya sake fa'di.
Sai nayi shiru ina kallon sa hawaye na na zuba ji nake tamkar in zura da gudu inyi waje.
"..Ba kin sami 'daurin gindi daga wurin Ammi ba?
" a a kayi ha'kuri"
Nace dashi da muryar kuka.
Bai ce dani 'kala ba kawai sai naga ya koma baya ya kishingi'da, da hannun sa ya nuna 'kasan 'dakin sannan yace " Zo nan"!
Sheshsheka na saki cike da tausayin kaina a hankali na matsa kusa neasa ka'dan da shi na tsugunna kan gwiwoyi na cuz wannan karan ba 'karamin tsorata nayi da shi ba.
Tashi yayi ya dan rankwafo Kano dan gami da kama kunnan sa ya wani 'kan'kance idanu tare da nuno ni da yatsa yace
" Daga yau...me nace...?"
Namaimaita " Daga yau" kamar yanda ya fa'di.
" Idan kika kuskura kwana uku ta cika ban ganki cikin gidan nan kin zo sharewa ba wallahi take wuyan ki zanyi in karairaya ki...kinji abinda nace ko?"
Da sauri na 'dage kaina sama wani hawayen na sake gangaro min.
"..Useless kawai..."
Ya fa'di tare da komawa baya ya jingina da kujera sannan ya 'kara fact 'din " 6ace ki bani wuri".
Da sauri har ina 'ko'karin fa'duwa na tashi na nufi 'kofar fita sai kuma naji yana sake fa'din " Saura inji abakin Ammi....kashe ki zanyi da wu'ka babu ruwa na".
Da sassarfa na fice daga gidan ina share hawaye na...ko nayi niyyan yin shiru sai in kasa saboda takaici da kuma girman tsorata da nayi gashi ya hana ni sanar da Ammi.
Gudun kar in je gida ina kuka ne ya sanya ni zama jikin wani gida na sha kuka na son raina sannan na share hawayen tas na tashi na 'karasa gida ina sakin ajiyan zuciya.
Ko da naje a parlour na tarar Ammi inda tana gani na kuwa ta tsura min idanu, sai nayi 'kasa da kaina ina 'ko'karin wucewa ciki sai tace da ni " zo nan Hudah..me ya same ki?".
Ta 'karasa da tambayata cike da kulawa.
Kaina 'kasa amma sai na kasa cewa da ita komai..ban sani ba aseh shirun nawa ya sa Ammi tabbatar da cewa akwai abinda ke damu na.
'Dan 6ata rai tayi tace " Shine ko?"
Jin haka yasa nayi hanzarin girgiza mata kai alamar a a.
" To menene?"
Ta sake tambayata tana kallo na.
Kaina kasa nace" ba komai fa Ammi".
Yanda nayi maganar yasa ta tsaya 'kare min kallo sosai tana karantar yanayi na.
Ganin har a lokacin ban 'dago na kalle ta ba ya sanya ta 6ata rai sosai a fili tace " Wato Mu'een bai jin magana ta ko?"
'Dagowa nayi da sauri jin ta ambaci sunan sa baki na har na rawa nace da ita " Ni..fa Ammi ba shi..bane...na ha'du da shanu da yawa a hanya ne irin na rannan... shine suka bani tsoro nayi ta kuka".
Ido ta tsura min sosai tana kallo na yayin da wasu hawayen ke sake sau'ko min ban kuma 6atawa kaina lokaci na share su ba dan nasan ko na share ma ba tsayawa zasu yi ba.
Can sai Ammi saki ajiyan zuciya ta janyo ni jikin ta cikin kwantar da murya tace" Ya isa haka nan to daina kukan kinji...bama zaki sake zuwa can 'din ba balle ki ha'du da su".
Jikin ta na kwantar da kaina ina ta sakin ajiyan zuciya, sam Ammi kam bata yadda da magana ta ba amma ta bari cikin ranta...musamman ma data ga yanda na yini sukuku a gidan babu walwala abin sai ya dame ta sosai dan tasan ba ganin shanu ka'dai ne zai sani hakan ba.
Da yamma kuwa sai gashi yazo gidan cuz ranar basu da buga 'kwallo.
Gaida Ammi yayi ta amsa babu yabo babu fallasa fuskar ta wasai, d next thing abinda ya fito bakin ta shine..." Me ka yiwa Hudah ta da na aika ta da safe?"
'Dan 6ata rai yayi cike da basarwa yace " Ammi wa ce kuma Hudah?"
" Bansan iskanci Muhammad kai kace in sa akai ma abu kuma sai ka je ka samin yarinya kuka?"
" ohh....wai waccen yarinyar ?"
" a a uwar ka nake nufi".
Ta bashi amsa ada'kile.
Ganin haka sai ya sashi zuwa gefen ta ya zauna yana fa'din " Allah Ammi ni duk bangane abinda kike min ba kwanan nan, gaba 'daya kin daina 'kauna ta saboda yarinyar can, komai nayi masifa kike min....ki tambaye ta mana in akwai abinda nayi mata ai da zata sanar dake na sani tunda ba abakin ta nake zaune ba".
Ya 'karashe maganar da sanyin murya.
Kauda kai Ammi tayi tare da fa'din " kai de ka sani, gaba ai tafi baya yawa.."
" Ni dai yunwa nake ji Ammi..abar zancen please".
Yayi maganar yana shafa cikin sa.
Dinning ta nuna masa tace " Ga can abinci je ka 'diba kaci mana".
" Da kaina kuma Ammi?"
Wani kallo da tayi masa ne ya sashi sakin murmushi ya mi'ke yana girgiza kansa..cikin ransa yake fa'din " ai dole ma in ringa cin uban yarinyar nan ko dan huce takaici na".
Ban gayawa Ammi cewa yace in dinga zuwa yi masa shara ba gudun kar tayi masa masifa ni kuma ya kashe ni, dan haka duk ranar da ya kamata inje sharar bana magana sai dai kawai inna shirya zuwa makaranta sai in bi ta gidan inje inyi masa kamar yadda ya fa'da, sau tari sai a lokacin break nake samun zuwa idan har nabi yi masa sharan dan wani lokaci harda wankin kayan ball da socks 'din sa yake bani, dan mugunta kuwa yana gani na sanye da Uniform amma bai ta6a cewa in bari in yi tafiya ta makarantar ba...sai dai abu 'daya bai ta6a duka na ba.
Idan kuma ranar babu makaranta to sai lokacin islamiya nake zuwa nayi masa aikin, wanda zuwa yanzun na fara fahimtar bashi ka'dai ke zama cikin gidan ba harda wani abokin sa mai suna Imrana dan ina yawan ganin ya shigo ko kuma wani sa'in su fita tare ...'dan iska ne na na 'karshe sam tarbiyya bata wadace shi ba, kusan kowa kuma ya san halin sa a garin...shima Yah Deen 'din gurin ball suka ha'du dashi har suka 'kulla abota.
Ni dai magana bata ta6a ha'da ni da shi ba illah gaisuwa idan na gaida shi ya amsa min da muryar sa da take abu'de, shima 'din kuma baya shiga harka ta musamman da yake idan nazo komai a tsarge nake yin sa bana sakin jiki na, kuma ma shi ya zaci ko 'kanwa nake ga Yah Deen shiyasa bai ta6a nuna min halin sa ba sam..shima sai yake min kallon 'kanwar sa..gashi kuma ma yana gudun zuciyar Yah Deen sosai shiyasa ya tsaya iya matsayin sa.
*****
Ma'u itace mutun na farko da ta fara fahimtar halin da nake ciki na rashin zuwa makaranta akan lokaci, da kuma zuwa gidan Yah Deen da nake yawan yi yanzu, dan ma mun 'dan jima bamu ha'du da ita ba nasan da tuni ta jima da fahimta, amma da yake mahaifin ta ya hanata yawan fitan nan da take yi shiyasa bata san da faruwar hakan ba.
Akwai wani 'dan wan mahaifin ta da yake son ta da aure, mahaifin ta yaso ya ha'da auren su idan shekarun ta sun kai amma sai Ma'u ta nuna sam bata ra'ayi, hakan yasa ya barta batare da ya takura ta akan hakan ba, sai dai ya taka mata burki akan yawan fitan da take yi illah zuwa makaranta shima 'dib jifa-jifa ne...shiyasa ma muka kwan biyu bamu ha'du da ita a unguwar Yah Deen ba.
Wata ranar laraba ne da aka tashi a makaranta muna hanyar komawa gida hanya ta ha'da mu da ita sai take ce min" Yauwa dama ina so in ganki in tambaye ki"
Da " To gani ai " na amsa ta sai tace..." wai me yasa yanzu nake yawan yin lattin Islamiya da makaranta tace kinga fa yau Allah da kin sha duka sosai badan na bada ha'kuri ba?"
Take na 6ata raina kamar dama jira nake yi kamar zanyi kuka nace da ita " Ba wannan Yayan bane yake sani aiki kullum, kuma yace kar in fa'dawa Ammi shiyasa idan zani makaranta sai in bi inyi masa aikin".
Ido ta zaro tana fa'din wai dama har yanzu yana nan ne?"
Kai na 'daga mata alamar " Erh"
Ma'u kam sai tace kar in damu duk ranar da zanje aikin inbi ta gidan su zata na raka ni sai mu gama da wuri mu tafi.
Da murna ta na amsa da to har muka rabu kuwa ina jin farin ciki har cikin raina.
Tun daga lokacin muke zuwa gidan ni da Ma'u duk kuma jikin mu da kayan makaranta muke zuwa, cikin sa'a kuwa muna yin aikin kaf mu gama mu kuma wuce makaranta batare da mun yi latti ba, haka kuma wani lokacin har mu tafi bama ha'duwa da shi da yake ni dama in ba ganin sa nayi ya fito ba ban 'kwa'kulo shi dan wai in gaida shi.
Sau uku kacal muka je da Ma'u Allah sai ya taimake ni ya tattara ya koma makaranta, ranar da ya tafin kuwa nafi kowa farin ciki tamkar in zuba ruwa a 'kasa insha haka nakeji.