← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 211

Sashe 195

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Baba zuciyar sa 'daya ya 'dauke shi ya kai gidan sa wanda kafin hakan sai da ya 'kira Ammi ya sanar da ita cewa suna ba'ki dan ta shirya musu wani abin kafin isan su.

Sai da suka tsaya suka sallaci la'asar a masallaci kafin su isa cikin gidan da su Zaidu da suma suka je masallacin.

Cikin girmamawa kuwa suka gaida ba'kin Alhajin a tare suka isa gidan har parlour Alhaji ya shigar da shi da yake sauran 'yan tafiyan nasa daga wajen gidan suka tsaya suna daga harabara gida, sukan sosai suke jin da'din komai da ya shafi wannan bawan Allah, gashi da sanyin hali, komai nasa ma mai sanyi ne, gidan sa ma ni'ima sosai sassanyar iska ke ka'dawa ta ko'ina.

Parlourn babu kowa dan haka Alhaji Baba yayi mai iso sannan ya umarci Saif da ya 'kira Ammin su yayin da ya tura Zaid 'kiran Mu'een a 6angaren sa.

Koda yaje kuwa Sallah ya same shi yana yi cuz baccin da yayi ya makarar da shi zuwa masjid.
Zama yayi ya jira shi ya idar kafin ya bashi sa'kon Alhajin.

Mu'een kai ya jinjina masa da tunanin me ya kawo Alhaji gida kuma da wannan yammacin?..wanda sai bayan da ya gama addu'o'in sa kaf kafin ya tashi ya fito.

Already Saif ya cika gaban Barrister da duk abubuwan da yaga Ammi ta ha'da na tarar ba'kin so ko da Zaidu ya dawo ma ba wani sauran abu kawai sanar da Alhajin yayi cewa Yayan yana sallah ne amma yana fitowa.

Kai Alhaji ya jinjina sannan ya sallame su dan aganin sa abin bai wani shafe su ba.

Saif kam sam hankalin sa bai kwanta da ba'kon Alhajin ba, musamman ma daya ga yana wani sussunkuyar da kai 'kasa kamar marar gaskiya.

Ko da suka fitan Saif 'kin tafiya yayi ya tsaya daga jikin 'kofa dan ya saka cikin ransa cewar sai yaji abinda ke faruwa.

Ammi ce ta fara fitowa jikin ta lullu6e da mayafin ta, murmushi tayi ganin yaran nata sun hutar da ita sun gama mata komai da ya dace tayi.

Zuwa kawai tayi ta zauna gefen Alhaji Baba sannan ta gaida Barrister, sau 'daya tak ya iya duban ta har suka 'kare gaisuwan bai sake ba kallon fuskarta ta ba.

Ammi kam sam bata gane shi ba..dan haka sai ta dubi Alhaji Baba tana murmushi..ganin hakan ya sashi murmushin shima...gyara zaman sa yayi gami da fa'din" Sirkin ki ne fa..".
Idanu Ammi ta 'dan zaro zaton ta ko sirkin ta ta 6angaren Hudah ne, da yake tasan yanzu ba matar kowa bace tana da damar kula duk wanda taso.

" Alhaji kar dai Hudah ta..?"
Ta tambaya da mamaki.
Sai ya girgiza kansa sannan yace" Mu'een dai".
Tsuke fuska tayi nan take fuskar ta ta nuna alamun tambaya.

Alhaji Baba bai damu ba sai ya dubi Barrister sannan ya dubi Ammi sannan yace" Wai baki gane shi ba ne har yanzu?"
Kai ta girgiza masa duk kanta ya 'daure ma.

Deen ne tafe a hankali kamar yanda ya saba tafiyar sa, yana zuwa sai yaci karo da Saif nan tsaye da mamaki ya dube sa da alamun tambayar me kake anan kuma.
Saif kunya yaji dan haka sai ya sosa kansa yana murmushi yayi gaba.

Gyara zama Alhaji Baba yayi sannan ya furta" Daga Abuja yake tafe kan batun auren 'yar sa...
Dai-dai nan Mu'een yayi sallama ya shigo wanda ya dakatar da Alhaji Baba daga maganar da yake yi.

Wuri ya zo ya samu ya zauna daga 'kasa sannan ya gaida su Alhaji Baba da ba'kon na sa daya gani zaune.

Cigaba Alhaji Baba yayi da bayanin sa wanda ya fara da yi musu bayanin farkon abinda ya kawo Barrister wajen sa...Mu'een na jin batun ya 'daure fuska tamau dan shi har ga Allah baya son wata damuwa yanzu balle Jiddah da yake ganin itace farkon tubalin rushe masa farin cikin rayuwar sa.
Ammi kam ba'ki ta ta6e jin abin sam bai yi wani tsari ba.

Daga hakan Alhaji Baba ya gangara da yi musu bayanin waye asalin Barrister.

Atare Ammi da Mu'een suka mi'ke tsaye suna duban Barrister da idanun su kamar zasu cinye shi 'danye.

Ammi kam mamakin kanta ma tayi da har ta kasa gane shi tun farkon shigowar ta, sai da ma Alhaji yayi bayanin kafin ta gane shi sarai.

Idanun ta ne suka cika da 'kwalla hannu ta 'dago ta nuna shi da yatsa amma ta kasa fa'din komai, tsoron ta kar ya sake dawowa cikin rayuwar su da niyyan sake tarwatsa musu farin cikin su, hawaye ne ya fara gangaro mata tana share su....

" Aishatu ki yafe min dan Allah ha'ki'ka ban kyautawa rayuwar ku ba dana kasance mai son zuciya ta..."
Ciki kawai Ammi ta wuce batare da ta kai ga jin 'karshen maganar tasa ba, 'dakin ta ta shiga ta kullo 'kofan ta dinga kuka, bata son abinda zai sake 'daga mata hankalin iyalan ta sam, bata son dawo da abinda ya wuce, me yasa Barrister zai dawo cikin rayuwar su a wannan lokacin..me kuma ya rage musu da zai dawo dan sake mallakewa?

Hankalin Ammi sosai ya tashi da ganin Abban Jiddah, bazata ta6a manta rashin imanin da ya gwadawa rayuwar su abaya ba wanda dalilin sa suka guji zama cikin gari suka ha'kura da duk wani jin da'di, don su tseratar da rayuwar su yasa suka dawo nan da zama sai gashi da 'kafafun sa ya sake biyo su da wani batun kuma.

Ammi na shigewa Mu'een ma ya kama hanyar barin 'dakin shima a fusace batare da ya furta ko kalma ba, ji yake badan Alhaji Baba ne ya kawo shi gidan ba da babu abinda zai hana shi tara masa mutane...Alhaji Baba na ganin cewa shima barin su zai yi yasa shi saurin ambatan sunan sa.

Cak ya tsaya sannan ya waigo ransa a matu'kar 6ace fuskar sa babu alamun fara'a ko ka'dan..yace" Alhaji ni bazan auri 'yar sa ba..kawai ya koma inda ya fito".

Yayi maganar ne batare da ya ko kalli inda Abban Jiddah yake ba, a ganin sa bashi da ko arzi'kin da zai samu kallo mai kyau daga gare shi.

Yana shirin juyawa yajiyo muryar sa na fa'din" Haba Muhammad ka dubi girman Allah kayi ha'kuri, kai fa musulmi ne..."
" Kai kuma kafiri kake ai a lokacin da ka zalunci iyaye na ko..."
ya furta hakan ne a matu'kar fusace wanda yasa Barrister saurin 'kasa da kansa.. cigaba yayi da fa'din.
" Kai har kana da bakin magana ne? ka ro'ke ni, ni in auri 'yar ka? in ba ma rasar kunya ba har ka isa ka zo gaban mahaifi na ka ce wani kana so ka ha'da jini da shi bayan duk zaluncin dakayi masa?
bani da wayo fa a lokacin amma har yau 'din nan ban ta6a mantawa da kwanan cell da ka sa mahaifi na ba na tsawon kwanaki bacin babu abinda ya aikata..ciwon hakan nake ji sosai..haushin kaina nake ji da ban canza ma kamanni ba..."
Abban Jiddah kam duk yayi laushi da raunin murya ya fara fa'din" Kayi ha'kuri...."
" Bazan yi ba..."
Mu'een sam baya bari ya kai ga jin 'karshen furucin Abban Jiddah sai ya yanke maganar tasa.
A zafafe har jijiyoyin kan sa na nunawa yayin da idanuwan sa suka fito sosai suka yi ja.

"...bazan yi ha'kurin ba.."
Ya sake maimaitwa...har ya juya sai Alhaji Baba ya sake 'kiran sunan sa.

Wannan karon bai waigo ba cike da dakiya yace da Alhajin" Ni bazan auri 'yar sa ba har abada Alhaji, idan Jiddah ta kasance mace 'daya da ta rage ne a duniya ni bazan ta6a auren ta ba...".
" Kana so ka nuna cewa ni ban isa da kai ba ne ko?"
Da jin hakan sai yavjuyo yacdawo gaban Alhaji Baba ya dur'kusa kansa 'kasa yace" Kayi min afuwa Alhaji amma harga Allah bazan iya auran 'yar sa ba...Alhaji kai mahaifi na ne kuma ka isa da ni kana da damar da zaka za6a min kowace irin mace kuma ni me biyayya ne agare ka zan aure ta in zauna da ita amma dan Allah Alhaji kar ka tilastawa kanka ha'da jini da wannan tsohon azzalumin domin har abada bazan ta6a iya yafe masa cutarwar da yayi wa rayuwar ku ba...".

Shiru Alhaji yayi ya lumshe idanu yana sauraran sa.
Da gama fa'din hakan sai ya tashi bai sake bi takan Alhaji ba kawai ya wuce gaban Abban Jiddah ya tsaya ido cikin ido yake duban sa kafin yace" Fatan ka fahimce ni?...ni bana ha'da jini da maciya amana masu zalunci irin ka...kasan halin da muka shiga ta dalilin ka ne abaya? ko kuwa kasan 'kuncin da ka jefa mahaifa na aciki saboda son zuciyar ka? dalilin ka muke rayuwa a wannan garin ba dan muna so ba duk kasan hakan ne? sanadin ka mahaifa ne ke rayuwa a 6oye kamar basu da 'yancin kai basu shiga mutane, ka haramta mana rayuwa a inda muke so ka rufe mana duk wani hanyar jin da'din mu, lokacin da ka zalunci iyayena kayi tunanin yadda rayuwa zata kasance musu ne baka yi ba...kayi tunanin halin rashi da zasu fa'da ne? d answer is no..duk baka yi wannan tunanin ba saboda son dukiya ya riga ya rufe maka idanu ka manta da farin cikin wasu sai naka..mutum ya gina gidan sa baka san ta yadda aka yi ya samu hakan ba amma kasa an 'kone shi, baka yi tunanin abubuwan sa muhimmi dake gidan da zai iya rasawa ba duk ka sa an 'kone su gaba 'daya, zaton ka ma ko duk muna gidan, sai Allah ya nuna maka gazawar ka ya tseratar da mu,...duk a lokacin baka yi tunanin rashin imanin da ka aikata ba, baka yi tunanin farin cikin wasu da ka da'kile ba sai yanzun da kake farautan naka farin cikin shine zaka kwaso 'kafafun ka ka zo mana gida? hadda kwantar da kai na munafurci ko?"
Chapter 195 · 0% Book details