← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 211

Sashe 211

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tana murmushi ta bashi amsa da fa'din" May be bata ji ka ba ne shiyasa ".
Tayi maganar ne batare da ta waigo ta dube shi ba.
Gaba tayi zuwa wajen sink tana wanke hannu yayin da ya 'karaso ta bayan ta ya sarke hannuwan sa a wuyan ta yana sau'ke numfashi.
" *_Nuree na_* "!
Ya ra'da mata a kunne gami da sumbatar bayan wuyan ta.
Fuskar ta 'dauke da murmushi ta sake fa'din" _Ni ban ji ba_ ".
" *Hasken Deen* ".
Ya 'kara fa'da yana mai gangarawa da hannun sa zuwa saman cikin ta.
" _Har yanzun ni banji ba_ ".
Ta sake fa'da tana mai 'ko'karin kwatan kanta daga jikin sa tayi gaba zuwa gaban Gasscooker ta sa hannu tana juya ha'din kayan miya da take soyawa...fuskar ta cike da murmushi.

Sosai ya sake matso ta ya rungume ta a jikin sa ta baya tsam sannan ya sake ra'da mata" *Ciwon zuciyar Deen* ". Cikin kunne.

Wannan karan dariya ya bata sosai ai kuwa tana fara dariyar shima ya taya ta yana jan baya yace" Ai gaskiya ne...." *Nuree na itace ciwon zuciya ta...*".
Kai ta girgiza masa sannan ta cigaba da abinda take yi murmushi ya kasa bariñ fuskar ta.

_They live happily ever after....._

*_Tammat bi hamdil-lah_*

*Me na manta?* 🤔
*Idan ma akwai kuma kuka tuna to ku jefa shi nan inda ya dace da shi...sai kuma ayi min afuwa domin ba laifi na bane laifin Brain 'dina ne* 🤗

*Alhamdulillah!!!...*🖊️
_Anan na kawo 'karshen wannan labari mai suna *NOORUL (Haske nah)...* wannan duk abubuwan dake cikin sa yake 'kir'kira ta ce ba da sunan wani ko wata nayi shi bs, in ma yayi kama da labarin ki/ka ayi min afuwa kuskuren al'kalami na ne bada niyya na aikata ba, ina ro'kon Allah ya yafe min dukkan kura-kuran dake cikin sa ya kuma sa a fahimci sa'kon da labarin ya 'kunsa...(Ameeen Yah Allah)_

_Duk Abinda aka tsinta ciki na kuskure kuma ayi min afuwa ba dan ni ba, duk abinda be yi miki ko maka cikin labarin ba shima dan Allah a watsar da shi kawai kunsan 'dan Adam Ajizi ne ba lallai ne in iya farantawa kowa dake bin labarin ba._

_Masoya na dake wattpad da whatsapp ina gaisuwa ina kuma mi'ka 'dumbin godiya ta, bazan iya lissafo sunayen ku anan ba amma ku sani wallahi ina 'kaunar ku irin unlimited 'din nan._
_Musamman 'yan group 'din_
*DA BAZARMU WRITTERS ASSOCITAION.*
*SALMERH MD PALACE.*
*NOORUL FANS GROUP* *UNIQUE ONLINE HAUSA NOVELS* _....Alherin Allah ya cimmaku a duk inda kuke 'yan uwa na...Allah ya kare ku daga sharrin CORONA, cututtukan zamani da ma dukkan wani abin 'ki._ 🙏

~*Salmern ku nayi muku fatan Alkhairi*~ 😍
_Sai wani lokacin kuma idan Allah ya kaimu in ma zan iya kenan kun san sai a hankali rubutun ba sauqi wahala yake bani sosai_.🤗
🔚🔚🔚🔚🔚

*Taku har kullum Miss Salmerh MD*.

©️ *2020*
Chapter 211 · 0% Book details