← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 211

Sashe 63

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi da idanu ta bishi har ya shige bayin tana murmushi sai ta girgiza kanta tare da tashi ta bar 'dakin.

Zuwa tayi ta ha'do mai tea lafiyayye ta kawo ta ajiye masa kuma har a lokacin bai fito daga bayin ba.

Bata damu ba kawai tayi ficewar ta da yake taji motsin ruwa tasan hakan kawai yayi ra'ayi.

*****
     Dawowar mu makaranta bayan mun 'dan huta ina ta bawa Ammi labarin makaranta yanda na fara 'ko'kari a ajin mu da yake Saif na 'ko'karin koya min wasu abubuwa yanzu shiyasa nake 'dan 'ko'kari.

Ammi sai jinjina kai take yi, ita kam duk hankalin ta na wajen sane, ai kuwa dakatar min da surutun nawa tayi da fa'din muje ki gaida yayan ki"
tashi tayi ta nufi dinning ta ha'da abinci a plate 'daya sannan ta umarce ni da in 'dauko mata tayi gaba ina 'dauka sai na bita abaya.

Ta riga ni shiga 'dakin...amma koda na isa nima sai na tsaya kamar yadda na ganta tsaye tana kallon sa.

Mi'ke yake akan kujerar dake 'dakin yana kallon sama idanun sa a rintse ban san ko bacci yake yi ba ko kuma idanun sa biyu.

" _Mu'een_ !"
Ammi tace sai naga ya bu'de idanun sa a hankali, kallo 'daya yayi wa Ammi sai ya tsaida idanun sa akaina ya 'kura min su yana kallo na, ni kam sai na yi 'kasa da nawa idanun gami da matsawa bayan Ammi na 6uya ai kuwa da ya daina hango ni sai ya lumshe idanun sannan ya mi'ke ya zauna ya fuskanci Ammi.
Duk abinda ya faru Ammi na lura da shi amma sai ta basar cuz tasan with time ne zai daina idan mutuwar tabi jikin sa.

" Ya jikin naka?"
Ammi tace da shi tana zama gefen sa.
Sai yace " ni lafiya ta 'kalau Ammi".
" hakan ake fata ai....ga abinci please ka samu kaci ko ka'dan ne"
Tayi maganar tare da mi'ka min hannu a 'ko'karin ta na kar6an abin da ke hannu na.
Da sauri na 'karaso na bata.
Yana shirin yin magana ta dakatar dashi da fa'din " ban son musu Mu'een tun safe me kaci?"
Kallon fukar ta yayi batare da ya sake magana ba, sai ta jinjina mai kai tana bu'de abincin gaban sa take fa'din " ai nasan abinda zai fito bakin ka, bai wuci kace ka 'koshi ba...nd u did not anything since morning, tea 'din ma ban yadda ka shanye ba"

" Allah Ammi nasha da yawa ma..." ...taran sa tayi da fa'din .."sai ka 'kara wannan ma koka'dan.

Goshi ya tattare gami da kawar da kansa gefe.

_Comment Vote and Share_ 👌🏻

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻😍 *Dedicated to 'kawa AMEEN D. ABDULLAHI...fatan Alkhairi 'kawar kirki...Allah ya 'kara dan'kon 'kauna* ~{Ameen}~ 🙏

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *33*

Ammi bata damu ba kawai ta daidai ta zaman ta tare da bu'de abincin ta sanya spoon ciki.

"..Ina yini?"
Na fa'di kaina 'kasa kuma batare da na ambaci sunan kowa ba...haka kuma in ce masa ya jiki ma sai ya min nawi a baki na.

Shima 'din 'dan ra'ayi kuma bai amsa ba, sai da Ammi tace da shi..."..da kai fa take".
Bai ko 'dago ya kalle ni ba ya amsa da fa'din " lafiya "a takaice.

Ji nayi duk babu da'di, duk da yake ma ba yau na fara gaishe shi yana amsan min a hakan cikin halin ko in kulan ba amma na yau 'din ka'dai sai naji na muzanta.

'Daga ido na nayi na saci kallon sa...yanzun ya 'daga kansa sama ya jingina da jigin kujerar hannun sa a 'kirjin sa idanun a kuma a lumshe...hararar sa nayi gami da kauda kaina gefe, cikin raina nace " wannan ko bashi da lafiyan ma ba zai canza hali ba".

Muryar Ammi ne ta katse min tunani na..inda naji tana fa'din" yauwa 'yan matan Ammi je kawo wa Yayan ki ruwa...amma ki duba ba mai sanyi sosai ba kinji?"
Kai na 'daga mata tare da juyawa sum-sum na fita daga 'dakin.

      Ina fita sai Ammi ta 'debo abincin ta nufo bakin sa da shi " open ur mouth".
Ta fa'di da yaren su, ganin ta kusanto bakin sa da abincin ne ya sanya shi bu'de baki batare da musu ba ya ansa.

      A hankali yake taunawa da'din abincin na ratsa shi, wanda ko 'kamshin abincin ka'dai ma ya isa ya ja ra'ayin mutun ga cinsa, doya ce da taji manja da bushashshen kifi harda kayan lambu...sosai yaji da'din abincin dan haka koda Ammi ta 'kara bashi be yi gardaman kar6a ba, lokacin da ta 'debo zata bashi ne a karo na uku har ya bu'de baki sai cak idanun sa suka sar'ke da nawa da isowa ta wurin kenan.

Bakin sa yayi saurin rufewa tare da yin 'kasa da idanun sa, a hankali sannan ya kai hannu ya kar6i spoon 'din daga hannun ta can 'kasan ma'koshi ya furta " Ammi let me..."
Ita ma Ammi ba ta hana shi ba ta sake mai tare da sakin murmushi, inda batare da 6ata lokaci ba ya 'karasa kai abincin bakin sa.

    Bai sake bi ta kaina ba dan ko inda nake bai sake kalla ba ya cigaba da cin abin sa cikin ransa yake tunanin ai idan yaran nan suka ga Ammi na bashi abinci a baki ai raina shi zasu yi....daga haka ya 6ige da tunanin kama da nake yi da marigayiyar sahibar sa.

A hankali na yi sallama tare da 'karasowa gefen Ammi na mi'ka mata cup da ruwan da na 'dauko...tana kar6a na juya na fita batare da na sake jiran komai ba.

   Ammi bata fito ba sai da tabbatar ya ci abincin tukunnna.
   Bai ma ci ko rabi ba ya ture gami da sanar da Ammi cewa ya ishesa abincin.

Ruwa ma ka'dan yasha ya ajiye.
  Ammi sosai taji da'din hakan dan haka da fara'ar ta ta fito da ragowar fuskar ta cike da annurin ganin jikin nasa Alhamdulillah sai godiyar Allah.

Har lokacin dawowar Alhaji Baba tayi Yah Deen bai fito parlour ya zauna ba, masallaci kawai yake fita da ya dawo kuwa sai ya wuce 'dakin sa, sai bayan sallar maghrib ne ma suka 'dan zauna da Alhaji can harabar gida har isha ya same su wurin, daga can suka wuce masallacin.

Dawowar su sai kowa ya wuce 6angaren sa wato su Saif da Zaidu, Yah Deen kam tare suka shiga 'dakin Alhaji amma bai wani jima cikin 'dakin ba ya fito ya wuce nashi 'dakin,
ko gun dinner ban gan shi ba...muna gamawa kuwa Ammi tace in jira muka kai masa abinci....

Tun dawowar sa daga 6angaren Alhaji Baba ya shige bayi kusan 30mins ya 'dauka ciki kafin ya fito da niyyar shirin bacci....a tsanake yake yin komai, cuz babu abinda zai aikata cikin rayuwar sa batare da ya ha'da da tunanin Nanne ba, shi kansa bai san wani irin so yake yi mata ba, bai ta6a tunanin zai so abu har hakan ba sam, sai gashi ya tsinci kansa dumu cikin wata iriyar soyayya mai cin zuciya sossai lamarin ke karya masa zuciya, yanzu ne ya fahimci ashe tun zaman sa da Rahma bai ta6a son ta ba, bai ta6a 'kaunar ta ba, bai ta6a jinta a zuciya kwatankwacin yanda yake jin Nanne ba.
" Toh menene?...ya tambayi kansa...saboda ko lokacin da sha'kuwar su da ita yayi 'karfi yayai zaton ko soyayya ce ashe ba haka bane, bai kuma ta6a zama na musamman yayi tunani akan Rahma ba ko ada 'din, Rahma bata ta6a shiga cikin rayuwar sa ta mamaye shi ba...gara ma ranar ha'duwar su da ita na 'karshe wannan ya san bai manta da incident 'din da wuri ba...yakan yawaita tunawa da wannan ranar musamman idan feelings ya tsananta masa ya abu na farko da yake fara tunawa shine that moment...baya ga haka kuwa sam-sam babu komai, shi kansa yana mamakin yanda  Rahma tayi saurin fita daga rayuwar sa...sa6anin Nanne da komai zai aikata ta kan fa'do ransa.

Tsaye yake yana 'ko'karin 6alle  botiran silky rigar baccin daya sanya a jikin sa ta bacci, ga dukkan alamu bai jima da fitowa daga wankan ba bazaka ta6a gane yanayin da yake ciki nan take ba in dai ba sanin kirki kayi masa ba, a zahiri kenan....sai dai a ba'dini abin ba haka yake ba, shi ka'dai ya san zafin da 'kirjin sa ke yi masa....yana basarwa ne kuma kawai dan ya san koma wace iriyar damuwa zai shiga hakan bai isa ya dawo masa da Amina ba.....sanin hakan da yayi ne ya sanya shi 'ko'karin tilastawa zuciyar sa dangana bayan da ya 'kara tabbatar wa kansa cewa wanda ya mutu ya mutu kenan.
      At times yawan tunani ke 'kara masa zafin 'kirjin musamman idan ya tuno yanda ya 'kwallafa ta cikin ransa, ya gama tsara musu rayuwa tun ma kafin ta san da zaman soyayyar tashi, tunanin Mu'een ko da yaushe nata ne, sanyin halin ta na birge shi, yanda take komin ta cikin sanyi da natsuwa...sosai hakan ya 'kara bada babbar guddummawa wajen dasuwar soyayyar Nanne cikin ransa jijiya da gangan jikin sa, yana jin tamkar rasa Amina da yayi shine babban hasara da yayi cikinrayuwar sa ta duniya....muhimmin gurbi ya ke6e mata cikin zuciyar sa.

Ire-iren tunanin kenan da ke 'kara sashi jin matsanancin ciwo a 'kirjin sa, amma sam bai damu da ciwon ba shi, he wish shima 'din da ya bita a ganin sa hakan zai fi masa sau'ki.
Chapter 63 · 0% Book details