Sashe 120
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwatsam ranar sai ga waya daga mahaifi na da wata safiya, inda yake ro'kon Alhaji Baba da ya bari akai Hudah (ni) 'dakin mijina, bai fito fili ya fa'di dalilin sa na yanke wannan hukuncin ba amma duk da haka Alhaji Baba ya fahimci dalilin da ya sa shi fa'dar hakan cuz dama yasan lamarin ba zai ta6a 6oyuwa ba.
Cikin kwantar da murya yace da Baban mu
" Wai da ni cewa nayi idan yazo kawai ya sakam min ita tunda dama can bai san da maganar auren ba kaga shikenan...."
Taran sa Baban mu yayi da fa'din" A a Alhaji kar ayi haka, abashi matar sa kawai rabuwar ai bata da wani amfani".
Alhaji Baba zai sake magana sai Baban mu yayi saurin fa'din" Dan Allah Alhaji kar kace komai...kawai ni dai na ce abashi matar sa".
Dole tasa Alhaji Baba yin shiru ganin cewa mutun dattijo irin Baban mu ke ro'kon sa akan 'dan wannan lamarin yasan abin ya girmama ne...duk da yasan kawai dauriya ce yayi har ya sa shi iya yanke hukuncin akai ni 'dakin mijina alhalin yasan 6oyayyar halayyar mijin nawa.
Sai da ya zauna yayi nazari sosai akan hakan kafin for the first time tun bayyanar cikin Ma'u sai yau ya sami Ammi da maganar inda yayi mata bayani filla-filla harda abinda mahaifina ya fa'di.
Ammi kam shiru tayi saboda tsabar mamaki, wai jin Mu'een 'din ta ke da wannan alhakin, sai dai bata jin zata iya barin 'yar ta zama tare da shi, tunda rayuwar da ya zabarwa kansa kenan sai yaje yayi tayi...ita bata san me zata ce da shi ba.
Da yake ita ba shiga cikin jama'a take sosai ba dama da Ummah ta suka fi zumunci a kaf 'din garin , Ummah ta kuwa nasan koma menene zai faru bazata ta6a bu'dan baki tayi mata bayani ba...musamman ma da yake abin ya shafi 'dan ta ne na cikin ta.
Ammi kam bata 6oyewa Alhaji Baba ba take ta bu'di bakivta bayyana masa cewa ita bazata ta6a yarinyar ta zama da shi ba tunda haka halin sa yake...wannan abin.kunya da me yayi kama, mutun haka kawai batare da an tambaya ko matsa shi bavya 'dau ki kyauyar yarinya sukutum ya basu auren ta amma sai gashi tun ba'aje ko'ina ba sakayyar da zai musu kenan...hawaye Ammi take tsiyayar wa tsabar takaicin halin Yah Deen...cikinvranta take tuno ranar da ya ta shirga mata 'karya akan case 'din sa da Alhaji Baba akan Husnah ashe ninke ta yayi abai-bai har ta yarda shi cewa ba komai ke tsakanin sa da ita ba...ga shicda Allah ya tashi kama shi sai yasa shi aikatawa a inda bai isa ya musanta ko 6oye abinda ya faru ba...tace wallahi yarinya ta tafi 'karfinvta zauna da mazinaci yake can ya nemi irin sa amma ba 'yata ba.
Da 'kyar Alhaji Baba yata bata baki gami da convincing nata ta sau'ko bisa umarnin mahaifina yace baya so yaga kamar ko bai ji maganar sa bane shiyasa amma ko shi ba so yake yi ba da niyyar sa araba auren kawai amma bakomai su cigaba da addu'a kamar yadda Baban mu ma ya fa'da....zai bashi Hudah amma bisa shara'di..Ammi hawauen ta kasa tsayuwa yayi, takaicin halin Yah Deen take sosai, tarasa meyasa ya za6arwa kansa irin wannan rayuwar...ace tun a yanzun sa ya san ya bibiyi mata to gaba idan ya fi haka shekaru kuma bata san me zai aikata ba...fatan ta kawai shine Allah ubangiji ya shirya mata shi.
Babu wanda ya bi takan sa har a lokacin, Ammi.bata 'kira shi haka ma Alhaji Baba...Sai dai shi Mu'een ne kan 'kira Alhaji su gaisa dan Ammi kam ma yanzu ko 'daukan wayar sa bata yi...da farko abin na damun sa saboda be san dalilin hakan ba amma daga baya sai ya share da yake suna waya da Alhaji kuma bai ta6a sanar da shi cewa akwai matsala ba..hakan yasa a kullum sai dai ya bada sa'kon gaisuwa yace a gaida su...ga shi Imrana ma tuni yana Kano shiyasa ma bai san da labarin abinda ke faruwa cikin garin nasu ba.
*****
Cikin Ma'u nada wata uku sannan Yah Deen suka dawo hutu wanda yazo da tsananin son ganin mahaifiyar sa dan ba 'karamin kewar ta yayi ba...amma cikin rashin sa'a ko da yaje sam Ammi bata wani nuna alamun jin da'din ganin sa kamar yadda ta saba ba.
Ko gaisuwa ma da yayi mata bata amsa ba sai ma ta tashi ta bar shi a wurin zaune.
Baki bu'de ya bi hanyar da ta fice da kallo cike da mamakin dalilin da ya kawo hakan.
Duk iya tsawon tunanin sa bai iya ya tuno laifin da yayi mata ba....ya kwashe a 'kalla kusan mintina ashirin bai ko yi motsin kirki ba saboda damuwa.
Wai yau Ammin sa ce ke share shi bayan tsawon watannin da suka 'dauka basu ga juna ko jin muryar juna ba?
Bai iya ya bar gidan ba har Alhaji Baba ya dawo wanda bayan gaisuwa sai ya fara shigar da 'korafin sa kan Ammi kamar zai yi kuka...Alhaji Baba kuwa ce ma yayi" Abinda ya dace da kai kenan Muhammad..ko nima daka gani ina amsa gaisuwar ka ne saboda wasu dalilai amma abin kunyar da ka jawo mana cikin garin nan hukuncin da yafi haka ya dace ya hau kanka....nan Alhaji Baba yayi masa maganar cikin da yayi wa Ma'u inda yai masa ba da'di cike da 6acin rai ya nuna masa kuskuren sa...jikin Alhaji har na karkarwa saboda 6acin rai...shi kansa Yah Deen hawaye yake tsiyayarwa jin yanda mahaifin sa ke faman yin Allah wadai da halayyar sa..yasan ba 'karamin 6aci ran Alhaji Baba yayi ba.
Ammi kam ko kallo ma bai ishe ta ba, tsaf ta fice a harkar sa ta daina ko kallon inda yake, yayin da tashin hankalin jin abinda ya faru a bayan san ya matu'kar 'daga masa hankali, bai ta6a yin tunanin yarinyar zata iya 'daukan ciki ba dayake ya bata magani daga baya kafin ta tafi...wancan karon da Husnah ta samu cikin sa hankalin sa ya tashi sosai har yasa shi zubar da cikin saboda gudun kar iyayen sa su san abinda take aikatawa, to sai gashi da Allah ya tashi kama shi yanzu sai labarin ya fito daga bakin mahaifin sa...'karshen tika tikin tik...'karya ta 'kare ya zaiyi kenan...ya zaiyi ya iya kallon mahaifin sa ya 'karyata wannan batu, ya zaiyi ya raba Ma'u da wannan cikin kafin ta haife sa...ina zai je da 'dan shege 'dan da ba ta hanyar aure ya same shi ba? _Uncle Ja'afar_ mutumin da ya fa'do ransa kenan a dai-dai lokacin take sai ya rintse idanu yana maimaita kalmar...innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Kwata-kwata ma ya manta da faruwar wani lamari tsakanin su kwatsam sai ga wannan mummunan labarin, ji yake tamkar ya bu'de 'kasa ya shige ciki...yanzu iyayen sa sun riga sun san 6oyayyiyar halayyar sa...yanzu kenan kowa kallon mazinaci zai ri'ka yi masa? Mai lalata 'ya'yan mutane.
Abubuwan duk sun taru sun yi masa yawa...ga fushin Alhaji, ga Ammin sa, ga tsoron kar Uncle Ja'afar yaji, ga shi 'karfi da yaji yana ji yana gani za'a haifa masa 'dan da ba na Sunnah ba kuma na shicda ikon hana faruwar hakan sam, ga tarin abin kunya ga kuma wai inji Alhaji Baba dole sai ya aure ta bayan ta haihu uwa uba ma kuma wai ya ha'da da matar sa su zama biyu...abin ya 'daure masa kai sosai, ina ya samu mata shi da har za'ace ya ha'da su su zama biyu...tunda yake a rayuwar sa bai ta6a jin kansa cikin tsananin damuwa da tashin hankali irin na yau ba, tafiya yake amma sam bai san inda yake saka 'kafafun sa ba...gaba 'daya hankalin sa baya jikin sa bai san inda ya dosa ba.
Tafiya ya ringa yi kawai cikin duhun daren yana tunani, wanda tashin farko kawai tsintar kansa yayi kan barandar makaranta...nan ya zauna ya du'kufar da kansa yana kallon 'kasa hannayen sa sar'ke cikin juna...nazari yake so yayi amma gaba 'daya ya rasa ta inda zai fara, duk abubuwan zuwa suke yi suyi masa karo a zuci.
Nawin da yaji 'kirjin sa nayi masa ne a lokacin ya sanya shi komawa ya kwanta da bayan sa hannun sa 'daya dafe da 'kirjin nasa yayin da ya dafe kansa da 'dayan hannun...bai ta6a tunanin akwai ranar da zai tsinci kansa cikin irin wannan halin ba sai yanzu da ya yaji shi aciki gashi ya rasa hanyar 6ullewa.
Bai san tsawon lokacin da ya 'dauka yana a hakan ba sai kawai jin 'kiraye-'kirayen sallah Asuba yayi.
Idanun sa nawi suka yi masa ga zogi lokacin da yake bu'de su ganin inda ya tsinci kansa ne ya sa shi saurin tashi zaune, mamaki ya so kama shi amma tuno abinda yake faruwa da shi ya wanki mamakin sa gaba 'daya.
Cikin hasken alfijir 'din dake haskawa ya tashi a hankali ya lalla6a ya isa gidan sa...sai da ya watsa ruwa ya saka jallabiya sannan ya tada sallar asubah wanda a lokacin har ma an idar a masallaci gari ya fara haske.
Da idar da sallar ko azkar bai tsaya yi ba kawai ya lalu6o wayar sa ya dannawa Imrana 'kira...wanda cikin sanyin murya yayi masa bayanin komai da ke faruwa harda zafin da iyayen sa suka 'dauka akansa da kuma hukuncin da Alhaji Baba ya yanke akan sa.
Imrana kam kwantar masa da hankali ya ringa yi da fa'din kar ya wani 'daga hankalin sa ba abinda zai faru...dama ai haka a rayuwa, balle wannan da ya kasance kuskure ne yasa har asirin abin ya tonu amma Insha Allahu komai zai wuce in auren ne ma ba sai ya aure tan ba kawai indai hakan zai sa hankalin su Alhajin ya kwanta...rayuwar gidan sa kuma ai a hannun sa take sai yadda ya so yayi agidan sa.