Sashe 72
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ma abin ya bar ranta da tayi tunanin kowani bawa kafin a halicce shi sai da littafin 'kaddarar sa ta zanu, komai yana tafiya ne bisa tsarin ubangiji to ita waye da zatace ba haka ba...tun da Ummah tayi wannan tunanin sai ta watsar da komai ta cigaba da harkokin ta, Addah ta ma yanzu ta samu sau'ki tunda ta fa'dawa mijin ta halin da take ciki a gidan shi kuma ganin gidan harda matan yayyen sa so ba dama shi yayi magana hakan yasa yaje ya dur'kusa ya zayyanawa mahaifin sa komai...da kansa ya tara su ya musu 'kira da babban murya akan baya son fitina kuma basu bawa mai tada ta goyon baya ba dan haka kowa ta kiyaye bakin ta, idan abin magana ne da wuya ka rasa ko wani mutun da shi me yasa za'a ringa takurawa Saudah a hana ta sakat bacin ba ita ce da alhakin komai ba...daga 'karshe yace kowa taja girman ta kowa ta kama mutuncin kanta baya son ya 'kara jin wani abu makamancin hakan ya taso in kuma ba haka ba to shikenan..yace da kansa zai 'dauki mataki akan koma waye".
Wannan jawabin ne ya 'dan samawa Addah ta sassauci a gidan har yasa ta koma ta cigaba da rayuwar ta kamar da can.
Baban mu ya kanzo duk lokacin da ya samu dama sai dai baya yin ko sati yake komawa 'kar'karin sa yayi kwana biyu ko uku shikenan ya koma.
*****
'Bangaren Yah Deen ma sun sake samun hutu kuma yazo da yake idan ya tafi baya ko le'ko gida har sai semester ta 'kare, hakan ya sa har mantawa nake yi da shi, dan ko awaya ban ta6a gaisawa da shi ba...and kuma still a wancen gidan nasa ya zauna ni kam hakan yafi komai yi min da'di.....sai dai wannan karan Ammi ce masa tayi bazata tura kowa dan yi masa aiki ba, ai gida yanzu babu kowa tunda su Saif basu nan illah ni ka'daice me ze hana shi dawowa ya zauna tunda ba 'yan hayaniyar...da 'kyar Ammi ta amince ta yadda masa bayan uban ro'kon da yayi mata ranar farko ma a gida ya kwana amma washe gari muka je da shi na taya shi gyara gidan inata tura baki na gashi mai aikin Ammi bata zo ranar ba.
Ranar nasha wahala sosai dan ma bai zauna ba shima tare muka yi aikin da yake yana so ya zauna a
gidan sai ya zage damtse ya manta da batun fi'ili, nima kuma gudun kar inje inyi abinda zaisa ya ta6a lafiya ta ya sa na saki jiki muka yi aikin tsaf.
Ko bayan da muka 'kare na riga shi komawa gida, sai kuma na sa Ammi a gaba na rin'ka yi mata kukan ciwon kai da gajiya, ita kuwa ta ringa masifan wai ya wahalar dani, haka yazo ya sami Ammi na ta sababi ita ka'dai ni kuma ina kuka.
Tsaki yayi zai shige ciki cike da 6acin rai dan yasan iskanci ne kawai ke damuna.
" Dan uban ka zo nan Muhammad".
Ammi tace da shi a fusace cikin harshen su na Igbo.
Sai ya dawo yana tattare goshi da 6acin rai yace..." Allah Ammi iskanci kawai ke damun yarinyar nan...ki tambaye ta mana ita 'daya tayi aikin ne?"
Gira Ammi ta 'dage sama tana duban sa da mamaki tace " Ashe ma ka san abinda ka aitaka kenan?"
Sai ya kauda kansa gefe ji yake tamkar ya rarumo ni ya jibge ni.
" Wato dan ka samu na barta taje shine zaka min iskanci anan ko Mu'een? Ba ma zakace sannu ba sai ka hau yi mata masifa kaima ko? ba lafin ka bane ai na san isar ka ce ta sa hakan, shikenan je ka abinka....gobe ma ai rana ce zanga wa zai sake yi ma sharar ai".
A fusace ya shige 'dakin sa batare da ya 'kara furta komai ba.
Wanka yayi sannan ya fito ya sake fita abin sa bai ko sake kallon in da muke ga dukkan alamu fishi yayi da masifar Ammin.
Ni kuwa Ammi rarrashi na ta dinga yi tana lalla6ani, da kanta ta rakani 'daki tace in je in watsa ruwa bayan na fito ta bani magani nasha na kwanta sai bacci.
Ban 'kara ganin Yah Deen ba har sai dare lokacin sallahr isha'i suna shirin fita masallaci yake ce da Ammi wai sai da safe
" Saida safe zaka ce ko, ka wahal min da yarinya sannan ko ya take ko ya gajiya bazaka yi mata ba zaka wani ce sai da safe?"
Juya idanu yayi gami da rintsewa ya kuma bu'de su nan take cike da 'kosawa yace " Allah Ammi kina 6ata yarinyar nan da yawa ita ba mace bace...dan tayi aikin shara shikenan ya zama wani abin sakalci?"
Zata sake magana yace " Zanje masallaci please Ammi sai da safe zanzo in duba ta".
" Hmm"
Kawai Ammi tace da shi daga haka bata 'kara fa'din komai ba.
Washe garin kuwa da yazo ko bi ta kaina bai yi ba ni ma dama kuma banso, haka ma Ammi bata 'kara tada maganar ba da yake dama da gangan take yi masa saboda gaba dan ya ji shakkan sake bani aiki mai wahala.
*****
Bai nemi a sake yi mai aikin ba dan gudun masifar Ammi har kusan kwana uku, kuma sosai ya rage zuwa gidan yanzu, sau 'daya tak yake zuwa wanda ni kam ma wani lokacin bana sanin yazo balle in san lokacin tafiyar sa.
Har akaci sati guda yana lalla6a rayuwar sa acan, da kansa yake yin sharar sa, yana so ai masa mopping amma fargabar abinda Ammi zata ce ya hana shi furtawa gashi kuma shi bai iya ba.
Kwance yake yana tunani a wani dare da bacci ya gagare shi gaba daya feelings ya takura shi haka ya dinga taso masa kamar abin masifa, ba ranar ya fara ji ba amma sai na yau 'din ya bambanta da sauran ranakun da yake ji.
Cuz ya kasa jurewa har cikin sa sai da ya ri'ke shi, bai san me ze yi ba hakan yasa ya ri'ke cikin kawai ya mi'ka rayuwar sa ga Allah mahalicci.....kafin cikar awa biyu kuwa zazza6i mai zafi ya rufe shi jikin sa na kakkarwa.
Haka ya kwana yana fama da rayuwar sa, ranar hatta sallar asubah ma a makare yayi ta dan bai samu bacci ya 'dauke shi da wuri ba shiyasa ya makara.
Duk jikin sa bai jin da'din sa sosai dan haka sai ya 'kira Ammi a waya ya sanar da ita cewa bai jin da'di ta aiko masa tea kawai.
Bai ambaci sunan kowa da ai kawo ba dan gudun masifar Ammi kawai ya yanke 'kiran.
Ai kuwa Ammi sai tabi wayar da kallo a fili ta furta kalmar " munafuki".
Sake dialling number tasa tayi kafin yayi magana tace " saura kuma idan na aiko ta ka sa ta aiki a gidan ka gani"
Ya riga ya san wa Ammi take nufi dan haka sai yace " Ammi ni na nace sai ita ne...ni ma ba san zuwan nata nake yi ba ai"
ya 'karasa maganar 'kasa-'kasa...dan har lokacin bai gane kan jikin sa ba.
A masifance Ammi tace " Sai ka fa'di wanda ka ajiye da zai ringa yima aika agidan ai, idan ba itan ba wa kaga nake dashi yanzu?"
" Kuma dai"
Ya furta a hankali yadda Ammi ba zata jiyo shi ba ha'di da sakin murmushin takaici...sannan a hankali cikin natsuwa yace
" Ammi wai dan Allah yaushe kika daina so na ne? Fisabilillahi cewa fa nayi banjin da'di amma kike ta min irin wannan masifar Ammi, idan babu mai kawo wa kawai abar shi shikenan na fasa ma".
Daga haka ya yanke 'kiran harda kashe wayar shi gaba 'daya.
~Ina gaida masoyanah Allah ubangiji yayi ta faranta muku cikin kowani irin yanayi...Salmerh na 'kaunar ku irin sosai 'din nan~ 🥰😘
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerhn ku ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
🤞🏻
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *37*
Bansan yanda suka yi dashi ba ni dai kawai tace dani in shirya in kaiwa Yah Deen tea a gidan can wai baya jin da'di.
Ban damu ba da na ji tace baya jin da'di dan haka raina fari tas na kar6a na kama hanyar gidan da yake.
Koda naje 'kofan a rufe take sai dana ta bubbugawa kafin yazo ya bu'de bayan na shafe a'kalla kusan mintina goma sha uku ina tsaye.
Ina jin an bu'de 'kofar sai na nutsu kamar wawuya daga bu'dewa nace " Ina kwana". Nayi maganar ina sunkuyar da kaina, bai amsa ba haka kuma bai ce da ni komai ba maimakon ma ya kar6i abin hannu na a a sai kawai ya bani hanya ya koma ciki abinsa batare da ya sake kallon inda nake ba.
A hankali nabi bayan sa bayan sa na shigo sannan na maida 'kofar na rufe ina 'kuk'kuni cikin zuciya ta.
Har parlour na shiga na same shi zaune yayi 'da'd'daya bisa kujera take na kauda kaina gefe bayan kallo 'daya da na mishi a hakan ma banko yi gigin kallan fuskar sa ba...ina shirin ajiyewa naji kakkausar muryar sa dake cike da 6acin rai yace" wai ke dan uwar ki miye ala'kar ki da Ammi?"
Jikina rawa ya fara take idanu na ya cika da hawaye jin tsawan da ya daka min.
Sai na fara in ina ina fa'din " Ni...ni"
Yace " a a uban ki"!
Take kuka sai hawayen tsoro suka taru cikin idanu na.
Ganin nayi masa shiru ne ya sanya shi tashi ya dai-dai ta zaman sa yayin da ni kuma motsin da yayin ya sake firgita ni zato na ko hi zai yi ya dake ni hakan ya sa na saki sheshsh'ka ina jan baya ka'dan.
A tsawace yace.
" ki min shiru da Allah ni..."
Tsit nayi na maida kukan gami da toshe baki na da hannu na duk biyu illah hawayen dake zuba min kaina 'kasa.