Sashe 102
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana cikin kuka sai taji 'karan wayar ta, bata yi tunanin shi bane cuz ta san da wuya yayi 'kiran ta dan haka share wayar tayi ta cigaba da kuka abin ta, sai taji kuma ta kasa daurewa, daf da wayar zai yanke tayi saurin kai hannun ta ta 'dago, da wuri ta gyara zama da rawar jiki taja recieve dan ganin sunan da ke yawo kan fuskar wayar tata.
Tana kukan ta 'kara wayar a kunnan ta batare da tayi magana ba, jikin ta har rawa yake yi haka ma bakin ta.
Hannu ta kai ta rufe bakin da shi yayin da 'dayan hannun ke ri'ke da wayar manne da kunnen ta sai ta kasa magana illah kuwa da ta cigaba da yi mai ha'de da sheshshe'ka, da ka ganta zaka san zuciyar ta ta wahala, tausayin ta ne sosai zai kama ka.
Mu'een na jin ta tana kukan amma ya share tamkar bai ji ta ba, sai ma ta6e baki da yayi ya'ki furta komai.
Ya bata a 'kalla kimanin mintina biyu da rabi yana tsaye yana jin ta tana ta sheshshe'kan kuka, bai ce da ita komai ba tsawon wasu mintina suna a hakan.
Yah Deen dai-dai da 'kwayar zarra daga cikin 'digon tausayin Husnah bai ji a zuciyar sa ba, yayin da Husnah kuwa ke son tayi magana amma kukan sai sake taso mata yake yi, abubuwa ne duk suka yiwa rayuwar ta yawa suka mata rumfa...sunan sa kawai take iya 'kira sai kuma ta cigaba da kukan ta idan tace.."..Mu...'een" kamar zata sake magana amma sai kuka ya 'kwace mata...tausayin rayuwar ta take yi ganin cewa daga mahaifiyar ta babu wanda ya damu da farin cikin ta, ko shi Mu'een 'din ma zuwa yanzun ta lura da kwai abu a 'kasan ransa.
Gajiya yayi da kukan nata at same time kuma ya gaji da ri'ke waya a saman kunnan sa, yayi tunanin sanya wayar a speaker ya ajiye amma kuma sai yaga kamar in yayi hakan ma tamkar ya bata wani dama ne na musamman da zata ji a zuciyar ta cewar he cares, hakan ya sanya a nutse cikin sanyin hali yace da ita" Quite please Husnah kunne na".
Fa'dar hakan da yayi ne ya sa kukan nata ya 'dan tsagaita a hankali bayan wasu sekanni, ji yake kamar ya yanke 'kiran ma kwata-kwata ganin kamar bazata natsu da kyau ta saurare shi ba, sai dai baya jin daga yau 'din akwai wata ala'ka ta daban da zata sake ha'da su, abu mai muhimmanci yake son sanar da ita da zai taimaki rayuwar ta da farin cikin ta, wanda idan ta yadda tayi na'am da shi to tamkar ta ceci zuciyar ta ne, ta wani 6angaren kuwa harda shi, fatan sa daga yanzu ala'kar su yanke koma ba haka b shi baya jin akwai wani abin da zai sa ya sake sauraran ta har ayi auren shiyasa kawai ya saka dauriya cikin ransa har ta rage sautin kukan da take yi.
Jin ta fara sau'ke numafashi ne ya sashi fa'din" Ki nutsu da kyau ki saurare ni... kina jina?"
Da " Umm" ta amsa shi tana goge hawayen dake fitowa ta 'kasan idanun ta.
Sai ya sake fa'din" Magana nake so muyi dake na 'karshe kina ji?"
Yanzun kam bata amsa shi ba illah bada hankali da tayi sosai tana sauraron sa...yayin da ya cigaba da fa'din" Wani labari kika tarar a gida bayan komawar ki? ki gaya min inji..".
Yayi mata tambaya irin wacce ya ta6a yi mata abaya.
Da muryar kuka ta bashi amsa da fa'din" Ance wai an bada aure na ga wani a garin ku mai suna Muhammad..."
Idanu ya lumshe yana shafo suman kansa da 'dayan hannun sa yace da ita" Ya kika ji batun to?"
Tace" Hankali na ya kasa kwanciya".
Murmushin mugunta yayi yana fa'din" Really? Ni fa aka bawa auren ki Husnah?"
Shiru Husnah tayi tana jin yanda zuciyar ta dokawa, wani sashi na damuwar ta taji ya na silalewa nan take, sosai taji da'din jin cewa shine aka bawa auran ta, kenn shi zata aura su 'karasa rayuwar su da shi.
Take ta saki murmushi mara sauti na farin ciki da jin da'di wanda in ba kana gabanta ba baza ka ta6a sanin tayi shi ba.
Shima Yah Deen shiru yayi tun bayan abinda ya fa'di, a 'ko'karin sa na son jin amsar da zai fito bakin ta shiyasa ya bata lokaci.
Ganin kamar shirun yayi yawa ne ya sashi sake fa'din..." Tell me to kina son auren da ni ko baki so na?"
Yanda yayi maganar bazaka ta6a zaton he is up to something ba, muryar sa wasai yayi maganar bazaka ta6a fahimtar yanayin sa ba.
Husnah kam cikin jin da'di ta tana share hawayen farin cikin dake zubo mata ta bashi amsa da fa'din" Mu'een kaima ai kasan ina matu'kar son ka...me yasa zan'ki amincewa da auren ka? wallahi indai da kai ne inaso kuma na amince har zuciya ta....".
A 'dan fusace ya tare ta da fa'din
" To ni ban so!..Husnah ni ban amince da auren ki ba...kuma ki sani har abada tsakani na da ke Husnab
h babu wannan batun, rayuwar aure na ba rayuwa ce da zan yi shi batare da tsari ba, bada irin ki nake so in shimfi'da ta ba ma, ke kanki kinsan bamu dace da juna ba, bai kamata mu kasance ma'aurata ba Husnah ko kin ta6a ganin inda mutum mai hankali ya kwashi datti dake bola ya akai cikin gidan sa ya adana? Infact ma kin ta6a jin ni na furta cewa zan aure ki ne..ko da wasa?"
Ya 'karashe maganar yana huci da zararren idanu...da ace Husnah na kusa da shine na tabbata tsoron ganin yanayin da shiga a lokacin ma ka'dai ya isa yasa ta furta cewa ta fasa auran sa.
A 'dan gigice tana 'kan'kance idanun mamaki ta furta" Mu'een..."! Tana karkace wuya.
Saurin dakatar da ita yayi da fa'din" Just listen...ba amsar ki nake son ji ba." yayi maganar tare da 'dago yatsan shi 'daya kamar tana gaban sa sannan ya cigaba da fa'din" ...
Zan miki garga'di ne sau 'daya tak and that's na farko kuma na 'karshe..I won't ever repeat my self again..fatan kin fahimce ni?"
Bai damu da rashin amsar ta ba kawai ya cigaba da fa'din" Husnah idan kina son kanki da arzi'ki, farin ciki da walwala to is better ki rufawa kanki asiri ki nemi hanyar raba auren nan, dan ubanki zaki ci a hannu na matu'kar kika kuskura kika yadda igiyoyin aure na na farko masu matu'kar daraja suka fara dake, wallahi sai kin gane waye asalin Muhammad Tahir...abinda kawai zan iya gaya miki ayanzu kenan sauran kuma ki bari in kika yi kuskuran zuwa hannu na zaki fahimta da kanki..."
Daga haka ya cire wayar daga kunnan sa yana shirin yanke 'kiran sai kuma ya tuna da wani abu, saurin maida wayar yayi kunnan sa Husnah kam dama mutuwar zaune tayi bata ko motsa da hannun ta ba balle ta raba wayar da kunnan ta...wuri 'daya ta zubawa idanu ko hawayen ma yanzun bai fito ba banda aikin bugu da zuciyar take yi, gani take tamkar a mafarki ne Mu'een ke shirin nuna mata zallar tsana ta zahiri wacce babu ko kara aciki, fatan ta inma mafarkin rake yi to kar Allah yasa ya kasance gaskiya.
Tana cikin hakan taji yana sake fa'din"...uhumm kina jina ko? Wallahi kuma kika sake yin kuskuran da 'kiran ki ya ratso min cikin waya ko ki sani ni da ke ne, matu'kar ba cewa zakiyi na fasa auren ba kar ki sake ki 'kira layi na...don't tell me kin fasa but an fasa gaba 'daya as in harda 6angaren mahaifi na da hakan ne ka'dai na baki damar 'kiran wayata in ba haka ba...dont ever call my line ever again fatan kin fahimce ni?"
Bata iya ta bashi amsa
ba ko yanzun ma sai wani kuka da ya 'kwace mata mai matu'kar cin zuciya, haka ta ringa kuka babu mai lallashin ta, ita ka'dai ta san yanda take ji, ji take rayuwar na neman juya mata baya gaba 'daya.
Mu'een da ta sani ne wannan 'din ko kuwa wanin sa, Mu'een ne zai iya duban tsabar idanun ta ya fa'da mata wa'dannan maganganun bacin ma ta san ba wani girman ta sosai yayi ba, in ba ma soyayya ba da ina ta ina shi? Da me ze ha'da shi da ita da har zai mata la'kabi da dattin bola...wannan abu da me yayi kama..wallahi Nu'een ka cuce ni ka gama da rayuwa ta"
Ta fa'di cike da takaici tana dukan katifa da duk hannuwan ta biyu...yau ne rana na farko a rayuwar ta da ta ta6a yin Allah wadarai da soyayya gaba 'daya, musamman ma irin soyayyar da ta masa irin wacce ke cutar da 6angare 'daya 'dinnan, Mu'een da ke haukace wa ya zauce a jikin ta wurin morar halittar da Allah yayi mata shine yau yake mata garga'di akan aure tsakanin su, bata ta6a zaton jin haka daga gare shi ba ko da wasa.
Ta tsinewa ranar da ta mallaka masa budurcin ta yafi sau hamsin, ko san tunawa bata yi, yanzu ne take da
na sanin sanin sa a rayuwa..kuma ra tabbatar da cewa kalaman da tayi matan babu wasa cikin su sam, atanda ta sanshi ra san cewa daga cikin zuciyar sa maganar ke fitowa kuma iya gaskiyar sa kenan, da gaske dama haka maza suke?...ba su da amana bayan sun gama da rayuwar ka da yan cinka...'karshe gudun ka suke cike da alfaharin sun fi 'karfin zaman aure tare da ke?
Yah ilahi...
Inannalillahi wa inna ilaiahi raji'un" Haka kawai ta ringa nanatawa tana kuka.