Sashe 193
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yah Deen da yanzu a ankare yake da sabbin numbers so yana ganin 'kira da sabon number yake gaggawan 'dauka da tunanin ko Noor in sa ce.
A wannan ga6ar kam sabbin numbobi ka'dai ne ke da gatan da zai daga 'kiran su batare da sun samu jinkirin ganawa da shi ba, baya ga haka kuwa indai har yana da number saving a wayar sa kuma ya sanka to kuwa sai ya gadama yake 'dagawa, a ganin sa babu abinda zasu rage masa daga damuwa illah shirme...wayar Ishaq da Safwan ka'dai yake 'dagawa.
Ko yau 'din ma 'kiran Abban Jiddah na shigowa wayar sa ringing 'daya na biyu ya 'daga wayar.
'Daga 'dayan 6angaren akayi masa sallama ciki-ciki ya amsa jin muryar namiji ne.
" Hope da Muhammad nake magana...".
" who ar u?".
Shine tambayar da Yah Deen yayi masa cikin dakewa.
" Kwantar da hankalin ka man soon zaka sanni, wurin ka na tunkaro fatan kana da chance 'din ganawa da mutane...".
"...Banda shi...zaka iya yi min bayani yanzu..ina jin ka.".
Yayi maganar yana me gyara zaman da kyau.
Shiru Abvan Jiddah yayi yana mamaki, tuni zuciyar sa ta cika da wasiwasi, yanda yake zaton yaron ma ashe abin ba haka yake ba.
Gudun kar ya bada kansa gaban yaran sa ne ya sanya shi datse wayar kawai yana jinjina kansa...Yaro 'karami na nenan raina masa hankali.."Jiddah baki kyauta min ba..."
Shine abinda ya fa'di cikin ransa yana jin babu da'di.
Tun ma kafin su isa garin ya fara jin zuciyar sa na tsinkewa, har haushin kansa ya fara ji domin gani yake kamar zuciyar sa na fargaban ha'duwa da Mu'een.
Yaron da ma yake tunanin tashin 'kauye ne shine har zai sashi fargaba...lumshe idanu yayi tuno pic 'din Mu'een da yayi.
Da kansa kuma sai ya 'karyata kansa, domin sosai ya fahimci Izzs dake tattare da shi cikin maganar sa..may be ba anan shi in ya tashi ba, ko dai iyayen sa ka'dai ke rayuwa a 'kauyen..
Shi sai ma ya rasa me ya kai Jiddah fa'dawa tarkon irin wannan 'dan iskan yaron, daga ji ba hankali gare sa ba.
Ko da suka isa Shuwarin tun daga bakin hanya Dad in Jiddah yace su fara tambaya ko an sanshi cikin ransa yake ayyana bazan kuma 'kiran sa ya raina min hankali abanza ba.
Tambaya suke da pic 'din sa suna 'kara shiga cikin garin...wasu sun sanshi wasu kuwa basu sanshi ba.
Yayin da wasu ke cewa wannan ai 'dan Alhaji ne..masu ambatan sunan mahaifin sa suke kwatanta musu gidan gonar Alhaji Baba.
Amma da yake takamamme basu san wurin ba sai suke sake tanbaya...da 'kyar suka samu wani ya shiga motar ya kaisu har lambun Alhaji Baba dan kowa tsoron su yake yi da ganin.'katuwar mota haka nan, musamman ma yanda Abban Jiddah ya hakimce cikin motar sai yake bawa mutane tsoro...kunsam duniyar mu ta yanzu sai a hankali.
*Happy sallah to all Ummah..Aci nama lfy..😎*
Comment
Vote
Share
*_Salmerh ce_* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *87*
Bai fito daga motar ba sai da ya tabbatar basu yi kuskure ba tukunna...sai da aka yi musu iso wurin Alhajin ya bada Umarnin su shigo kafin ya fito daga motar.
Zama suka yi suna jiran zuwan sa dan a lokacin yana tare ne da wasu costumers 'din sa, zaman jiran sa suka yi a inda aka tanadar musamman saboda saboda ba'ki...P.A in sa na tsaye ne daga gefen sa wanda ganin hakan yasa Abban Jiddah bashi umarnin su jira shi wurin mota dan wannan personal issue ne.
Hakan kuwa akayi P.A komawa yayi ya bu'de mota ya shiga yana jiran fitowar Ubangidan nasa.
Gyara zaman Abban Jiddah yayi ha'di da murmushi tuno yawan 'kiran da Jiddah tayi masa daga lokacin da ya bar gida zuwa yanzu..ko bayan shigowar su garin nan ma sai da ta yi 'kiran sa burin ta kawai shine taji cewa an amince da batun aura mata shi.
Yana murmushin yake bin cikin wurin da idanu... sosai lambun ya birge shi saboda akwai ni'ima sosai, 'kasan wajen luf-luf yake da korayen ciyayi masu birgewa awani 'bangaren ma har design aka cire da shi ya kuma bada ma'ana mai kyau abin sai wanda ya gani.
Murmushi maahifin Jiddah ya sake yi, cikin ransa yake tuno rigima irin ta Jiddah" 'Dan gidan mai lambu...".
Ya furta a fili inda ya 'karasa da murmushin mugunta.
Gyara zaman sa yayi yana sake bin ko'ina da idanu.
Wannan karan cikin ransa ya furta" Da alamu Naira zata yi amfani tunda naga akwai 'dan kashi..."
Ya 'karashe da jinjina kansa.
Cigaba yayi da sa'ka abubuwa cikin ransa yana me sake bin lambun da idanu.
"Jin sa kawai yafi ganin sa, 'kila da hakan ya yaudari zuciyar Jiddah har ta fa'da tarkon sa... gashi nima yasa na taso ba shiri saboda fitinar ta...ai da nasan hakane da aike kawai zanyi a gama komai ba sai nazo ba".
Ya 'karashe wannan tunanin da canza yanayin zaman sa ya karkace gefe guda, 'kafar sa 'daya ya mi'kar bayan ya cire takalmin sa ya maida 'kafar akai yayin da ya 'dayar ke tan'kwashe.
Hannun sa 'daya ya 'dago ya tallafi gefen fuskar sa da shi..a hakan sai yafi jin da'din 'karewa lambun kallo da kyau.
Baki ya ta6e lokacin da yaga manyan motoci guda biyu dake 'ko'karin fita daga lambun da alamu muhimmin abu ke gaban su duba da yanayin da yaga suka figi motocin.
Sam bai kula da tahowar Alhaji Baba ba dake tahowa kansa 'kasa yana gyara zaman babbar rigar dake jikin sa...Sanye yake da shadda wagambari mai kalar madara wanda duban.farko zaka fahimci maku'dan ku'daden da aka kashe kafin samuwar kayan.
Idanun sa na wani wuri can da ya 'dauki hankalin sa ga kuma haushin.6ata lokacin sa da yayi wurin zuwa wannan garin da yayi... har Alhaji Baba ya 'karaso kusa da shi har ma yayi masa sallama amma bai ji sa ba.
Sai da Alhaji Baba yayi gyaran murya kafin Abban Jiddah yayi saurin ankarewa.
Waigowa yayi domin.ganin.wanda ke masa sallamar nan take sai suka ha'da idanu da juna.
Cak Alhaji Baba ya tsaya yana duban sa cikin idanu yayin da mahaifin Jiddah yayi saurin mi'kewa tsaye har yana 'ko'karin fa'duwa amma ya yi sa'a be fa'din ba.
Alhaji Baba duban sa yake yi da tunanin in da ya sanshi, domin fuskar sa sosai tayi masa kama da wanda ya sani amma ya kasa tunawa.
Mahaifin Jiddah jikin sa rawa ya fara da tunanin Allah yasa mafarki yake ba gaskiya ba, gaba 'daya ya rikice ya rikita zuciyar sa, kallon da Alhaji Baba ke yi masa na a ina ya sanshi ne..yayin da shi kuma da ke tsarge yake sai yake ganin tamkar kallon tuhuna yake yi masa.
Da rawan baki ya furta sunan" Ta...heer".
Da disashshiyar muryar sa da ko fita da kyau bata yi ba.
Mamaki sake kama Alhaji Baba yayi wanda hakan ya shi 'dan waro idanun sa, domin kuwa yanzun ya fahimci zuciyar sa ba 'karya take yi masa akan wannan mutumin ba, tunda gashi da kansa ma ya sanshi hadda sunan sa ya 'kira, duk yadda akayi sun san juna ne da jimawa...amma shi ya manta.
Nuna shi da yatsa Abban Jiddah yayi muryar sa na rarrabewa ya furta
" Ta..heer..kaine nan da gaske... dama kana raye Taheer?"
Wani bugu zuciyar Alhaji Baba tayi mai mugun firgitarwa sakamakon wani abu da ya fara fahimta game da wannan ba'kon nasa...kallon.'kurilla da suke yiwa juna shi ya sake bashi babban gudummuwa wajen.saurin.fahimtar waye wannan agaban sa.
Ko daga bacci ya tashi ba zai kasa gane wannan halittar ba, ballantana muryar sa..da farkon yanayin girma da ya kama shi ne ya hana shi saurin fahimtar waye shi...
Alhaji Baba duban sa kawai yake yana tariyo muguwar cin amanar da yayi musu abaya...sosai yaji tashin hankali a zuciyar sa gami da tunanin.yau kuma me ke tafe da shi wa ma ya sanar da shi inda muhallin sa yake sai Allah.
Basarwa Alhaji Baba yayi ya sawa zuciyar sa dauriya duk kuwa da cewa ganin mutumin ya ka'da shi, a hankali ya 'karaso ya zauna bisa kujerar dake kuma har a lokacin bai furta komai gare shi ba.
Cikin dakiya irin ta Alhaji Baba harda 'daura 'kafa 'daya kan 'daya, murmushi mai sanyi mai nuna alamun rashin damuwa ita ya sanyawa fuskar sa sannan ya dube shi da muryar sa mai cike da dattako ya furta" Bismillah..ranka ya 'dade...".
Yayi maganar yana nuna masa kujerar da ya tashi.
abban Jiddah komawa yayi ya zauna a 'darare dai-dai shigowan 'kira cikin wayar sa, duk ya rikice ya kuma rikita kansa, 'dagowa yayi da rawan jiki ya duba sai ya jefa wayar cikin aljihun saman rigar sa...yana rarraba idanu.
Alhaji Baba kam duk na binsa da idanu yana karantar yanayin sa, ganin ya kasa natsuwa ne ya sa shi fa'din" Barka da zuwa...".
Tun ma kafin Alhaji Baba ya rufe baki Abban Jidda yayi saurin amsawa gumi na karyo masa ta ko ina a jikin sa.
Banda danasanin zuwan sa tShuwarin babu abinda yake yi, bai ta6a zaton wannan tafiyar ga Taheer zata kawo shi ba..da ya san hakane da tuni zai bawa Jidda ha'kuri ta ha'kura da zancen yaron nan ta nemi wani.
Sam ya kasa sake duban Alhaji Baba sai gefe yake kalla yana 'kif-'kif da idanu...ashe har yanzu yana raye?.
Abinda zuciyar sa ke ta maimaita masa kenan.
Alhaji Baba ne ya yanke shirun dake tsakanin su da fara mi'ka masa masa gaisuwa.
Haka Abban Jiddah ya amsa a ta'kaice batare da ya iya duban sa ba.
Ruwa mai sanyi Alhaji Baba ya bu'kaci a akawo masa dan yaga kamar yana da bu'katan hakan amma ko da aka kawo Abban Jiddah kasa sha yayi.