Sashe 208
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Watarana da ta kai masa breakfast 'dakin sai ta tarar da shi yana ta nishi da 'kyar yana dafe 'kirji...zuciyan ta tsinkewa yayi sosai bata san lokacin da ajiye abin hannun ta tayi kansa ba, shikuwa dama da yake shirya abinsa yayi jin ta kusa da shi ya sanya shi sake narkewa yana canza salon numfashin sa.
Ai tuni ta fara kuka tana ambatan sunan sa a ki'dime.
Waje tayi da sauri ta lalu6o wayar ta ta 'kira Ammi tana kuka take gaya mata halin da yake ciki.
Ammi ma da jin hakan sai ta rikice take ta fara salallami.
Da 'kyar ta kwantar wa Noor hankali ta tsagaita kukan da take yi.
Komawa tayi 'dakin nasa nan ta tarar da shi kamar yadda ta barshi...sai di zuwa yanzun numfashin sa ya daidaita amma idanun sa a lumshe suke.
Fargaban ta ita bata san yadda zatayi da shi ba koa da da suka yi zaman aure ma bata ta6a yi masa jinya irin haka ba..da muryar kuka tace da" Sannu.. ko na 'kira azo atafi da kai asbiti?"
Kai ya girgiza mata a hankali batare da ya bu'de idanun ba, cike da galabaita ya nuna mata inda magungunan sa suke yace ta 'dakko masa.
'Balla masa tayi sannan ta 'dauko cup 'din tea da ta kawo masa sai kuma taga ai a kwance yake.
Mayar da cup in tayi ta ajiye sannan ta dawo ta wurin kanshi ta 'dan 'dago shi ka'dan da 'kyar ta iya jingina kan sa da 'kirjin ta ta mi'ka hannu ta 'dago cup 'in ta sanya masa abaki sai da ya 'dan kurba kafin ta bashi maganin ya sha.
Ajiye Cup in tayi sannan ta matsa baya a hankali ta fita daga inda take nan ta maida kansan ta kuma kwantarwa a hankali.
Sannu ta ringa jera masa shi kuwa ya lumshe idanu sai sau'ke numfashi yake a hankali..ganin yanzu baya fizgan numfashin yasa ta jinjinawa 'karfin magungunan nasa da ingancin su.
Shi kam haka yayi luf kamar wani mai ciwo dagaske...da ta juya sai ya faki idanun ta ya 'kyallara ido guda yana murmushi da ya ga zata waigo sai ya komar da idanun ya rufe kamar bashi ba.
Sai daya tabbatar ta fita daga 'dakin kafin ya 'dauki wayar sa ya turawa Ammi text akan cewa kar ta wani 'daga hankali zazza6i ne kawai ke damun sa kuma ma ya sau'ka.
Yayi hakan ne kasancewar yaji lokacin da take waya a palour kuma yasan da Ammi tayi wayar...gudun kar suma su 'daga hankalin su.
Tun daga ranar ita ke 'dawainiya da shi..ita zata kawo masa abinci ta zauna ta dinga bashi abaki wanda ka'dan yake ci ya girgiza mata kai alamar ya ishe shi...kullum hannun sa dafe da 'kirjin sa yana nuna mata alamun yana jin jiki, tayi tayi da shi kuma suje asbiti ya'ki...idan ta 'kira gida ta sanar da su kuma sai dai suce mata" Allah zai kawo sau'ki ta kwantar da hankalin ta"
Bata san meyasa yanzu basa damuwa da ciwon nasa ba.
Hatta brush ita ke yi masa ta kuma taya shi wanka...bacci ma yanzu wani sa'in a wurin.sa take yi domin idan tazo gayara masa kwanciya hana ta barin jikin sa yake yi dole sai ta kwana kusa da shi..duk ta gaji ta fara fita hayyacin ta har 'yar rama tayi..shi kam fakon idanun ta yake yi lokuta da dama yana yiin murmushin mugunta...ko da wasa be taa kuskuren da zata fahimci cewa ciwon 'karya yake yi ba.
Sai in ya tabbatar bata kusa tana kitchen ko kuma 'dakin ta sannan sai ya 'kira su Ammi su sha hirar su lafiya lau, guarantee sun san babu abinda ke damun sa...shiyasa ko Noor ta fa'da musu ba basu wani 'daga hankalin su domin kusan kullum sai sunyi waya da shi.
Anty Zainab ce ma taja masa kunne akan rikitar da Noor da yake yai yace " Rabu da ita Anty yarinyar nan ta raina ni da yawa, itama ta ta6a wahalar da na tayi akanta taji abinda ake ji".
Kwafa Anty tace" abin ya ishe ni kuwa kasan gaskiya zan gaya mata ko?"
" Sorry Anty ki barni da ita dan Allah bata gama yin hankali bane har yanzu...".
Daya ji motsin ta sai yayi saurin kife wayar ya koma luf kamar mai bacci.
Ko da wasa baya bari taga wani wargi tattare da shi...haka zasu shiga bayi suyi wanka tare tayi masa su fito amma baya ko nuna alamun yaji sha'awar ta ma balle ya kuskurewa shirin sa.
Ita kam ta 6angaren ta wani lokacin sosai yakan bata mamaki, sau da dama ta kan lura da shi kamar yana iya yiwa kansa wani abin musamman idan bata kusa, ta kan yawaita tarar da shi ya canza kaya ko kuma ta tarar da shi yana sallah lafiya lau amma da zaran ya idar shikenan zaki ga ya sake narkewa babu abinda zai sake aikatawa matu'kar tana nan.
Sai ta fara tunanin ko dai sallar ne ka'dai Allah ke bashi 'karfin yin ta...ita fa duk tausayin sa ya gama cika mata zuciya.
Har 'yar rama tayi dan kusan kwanaki goma kenan suna abu 'daya da shi 'karfi da yaji ya sanya ta sabawa da jikin sa da zama kusa da shi badan tana so ba.
Da abin yayi yawa kuma sai ta fara lura da wasu abu, domin ko bata yi masa abu ba da kansa ma zaiyi abin sa hakan yasa ta rage damuwa domin ta fahimci kamar sau'ki ya fara zuwa masa ne.
Ita dai Addu'ar ta a kullum be wuci Allah ya bashi lafiya su koma gida bane, burin ta kawai kenan shiyasa bata yi masa wasa da shan magungunan sa.
Da abin ya ishe ta
wata rana agaba ta sa shi ta dinga kuka kamar ranta zai fita domin idan taga kamar sau'ki na samuwa sai kuma ta ga abu ya sake dagulewa.
Kanta 'kasa tana ta kuka gwanin ban tausayi, shi kansa dake kwancen tausayin ta ya gama cika shi idan bata kallon sa sai ya bu'de idanu 'kir yana duban ta yana ganin yanda take kukan yana ji kamar ya rungumo ta ya lallashi abin sa amma bai gama hora ta ba tukunna.
Sosai taci kukan ta ta gaji gashi Anty Zainab ma kusan kullum ha'kuri take bata tace da ita ta daina damun kanta ai zai warke ne...ita kam zancen Antyn sam baya shiga kanta ma, tana ganin Yah Deen na kwance rai a hannun Allah ta ya hankalin ta zai kwanta...rashin nuna damuwa da suke yi yanzu akan sa ya sanya itama ta rage sanar da su...domin bata ga amfanin hakan ba.
Tana cikin kukan taji wayar ta na ruri amma ta kasa 'dagawa.
Sai da ta yi missedcall biyu kafin taji ta Yah Deen ma na 'kara...shima 'din har ta gama ringing ba'a 'daga ba dan kwance yake yana jinyar kansa na 'karya.🤪
Akaro na uku nata wayar ya sake 'kara da sauri ta kai hannu ta 'daga ko tsayawa taga waye ma bata yi ba ta rushe da kuka, Ammi ce amma bata kula ba kawai ta fara fa'din" Anty dan Allah ki taimake bansan ya zanyi da shi ba, Anty dan Allah ki dawo wallahi kullum 'kirjin Yayah ciwo yake yi masa ban san yanda zan yi ba, Anty tausayin shi nake ji sosai dan Allah ku taimake ni in samu a kai shi asbiti ni nayi-nayi da shi ko anan ne ma amma ya'ki, idan wani abin ya faru da shi ban san yanda zan yi ba...".
Tashi tayi ta fita ta koma palour wai dan kar ta dame shi...Still da wayar a kunnen ta tana me cigaba da ro'kon Anty.
Ammi kam shiru tayi sai da ta gama jin abinda Noor 'din ke fa'di kafin ta 'kira sunan ta da raunin murya...dan duk jikin ta yayi sanyi da jin abinda Noor 'din ta fa'da.
Noor na jin muryar Ammi cikin wayar sai kukan ta ya 'karu tana yi tana kai 'dayan hannun ta saman la66anta tana rufe bakin da shi..hawaye duk sun wanke mata fuskar ta tas.
Shi kansa Yah Deen tun fitar ta ya tashi zaune, daga inda yake yana iya jiyo duk maganganun ta yasan kuma duk saboda shine take kukan bai ta6a jin tausayin ta irin na yau ba, ya riga ya sanyawa ransa cewar daga yau wasan nasu zai 'kare ba zai sake wahalar da ita ba.
Tambayar ta Ammi tayi abinda ke damun sa nan ta fara fa'da mata tana kuka tace" Ammi dan Allah kar kice min bakya son shi yanzu kullum idan na gaya muku bakwa nuna damuwa a kansa Ammi 'dan ki ne fa shi, kin manta wancan lokacin da na ga kin damu akan sa..Ammi yanzun ma fa ko motsi baya iyawa da kyau...baya iya yiwa kansa komai me yasa bazaku tausaya masa ba....?".
Da 'kyar Ammi ta lallashe ta tayi ta yi shiru da fa'din ta kwantar da hankalin ta za'a san abinyi..ba wai son shi ne suka daina ba.. ita dai Ammi tasan babu abinda ke damun sa amma ta rasa dalilin da yasa Mu'een yake wahalar mata yarinya.
Murmushi yayi bayan gama.jin abinda ta fa'di yanzun ga Ammi..hannun sa yake 'dan mammatsawa yana murmushi, shi kansa fa ya gaji da kwanciyar nan kawai 'karfin hali yake yi...ba'a jima ba sai yaji wayar sa ta 'dauki 'kara.
Hannu ya kai ya 'dago wayar sai ya saki wani sabon murmushin ganin sunan Ammi..gyara muryar sa yayi tarwai sannan yayi mata sallama daka ji muryar sa zaka san lafiya cikakka gare shi ba wani alamun jinya tattare da shi, abinda yasa kullum Ammi bata damuwa kenan domin haka kullum take jin sa idan suna waya da shi.
A lokacin Noor ta tsagaita da kukan ta illah ajiyan numfashi dan haka itama taji 'karan wayar tasa.
Tana amsa sallamar yace" Ammi na..!"
" Kayi min shiru! me ke damun ka tell me?"
" Ni bakomai Ammi".
Ya bata amsa yana murmushi.
" Yanzun nan fa matar ka ke ce min ko motsi baka iyawa shine nake jin muryar ka haka nd u ar still telling me bakomai...wai meke faruwa ne dan Allah Mu'een?"