← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 211

Sashe 178

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bisa gwiwoyin sa ya sulale yana hawaye ya dafe kansa da dukkan hannuwan sa biyu kuka yake yi mai matu'kar tsuma zuciya da 'kyar ya samu bakin sa ya bu'du ya furta" Haba Ammi!...ke xe fa kika haife ni, me yasa bazaki tausaya min ba, 'yata fa na rasa Ammi.kuma sannan.ki sake raba ni Noor ina zan sa kaina?".
" Inda ka saba sawa mana...".
Ta bashi amsa a hassale.
Bai damu ba ya cigaba da fa'din" Please! please ba dan ni ba, dan Ubangijin mu Ammi ki ji 'kaina ki bani wani chance, i promise u bazan sake yin wannan kuskiren ba, zan canza wallahi zan zame mata d best husband ever morethan u can imaging, nasan ban kyauta ba nasan nayi kuskure amma dan Allah ku yafe min Ammi i promise u bazan sake maimaita irin wancan rayuwar ba...Ammi ki tausaya min ki yadda da tuba na, believe me bazan miki 'karya ba.. wallahi ina son Matata, i luv Noor with all my heart that rabamu zai iya zame mana matsala Ammi, ki tambaye ta kiji ita kanta nasan..."
Hannu Ammi tayi saurin 'daga masa alamun ya isheta haka nan sannan tace" Kalaman kan nan 'kona ni suke yi Mu'een sam basu da amfani yanzu lokacin da ya kamata ka basu muhimmanci.watsi kayi da su, i don't care weather son mutuwa kake yi mata is alla useless tun da kayi wasa da damamma kin ka abaya...now komai ya wuce buri na kawai inga babu wata ala'ka tsakanin ka da 'yata, buri na inga bata tare da mutun irin ka, ka rubuta min abinda na bu'kata kawai yanzun nan..."
" Ammi ta ya kike tunanin zan iya rubuta wa Nuree saki da hannu na, matar da nasan idan na rasa ta tamkar rasa farin cikin rayuwa ta ne, Ammi Noor itace rufin asiri na, itace Hasken rayuwa ta, ada da kaina nayi al'kawarin zan bar rayuwan su saboda ta bu'kaci in daina zuwa inda take, nd nayi i promise zan bar su saboda su sami farin cikin rayuwa ita da Baby, but Ammi yanzu babu Baby, ta tafi...ina jin tausayin Noor sosai, sam bazan iya rabuwa da ita ba a wannan halin bacin nasan cikin 'kunci take ayanzu, Ammi ki fahimce ni ki bani daman gyara kuskire na, ta ya Noor zata samu wani  farin ciki bacin babu kowa tare da ita...?"
" Dan ubanka kuma sai akace maka kaine ka'dai farin cikin ta?..
Ammi ta jefa masa tambaya a hassale cike da 'kosawa da maganganun sa.
'Kasa yayi da idanun sa yana mai share hawayen fuskar sa da hannun sa 'daya tamkar yaro 'karami.
Ammi kam bata damu ba ta cigaba da fa'din" Ai koka'dan banga alamun tausayi tattare da kai ba, shekaru nawa kake tare da ita? kwanaki nawa ka 'dauka kana cutar min da ita? ko angaya ma bana damuwa da rashin ganin walwala a fuskar ta da banayi ne...ko dan kaga ban ta6a tuhumar ka akai ba ko?
Idan soyayyar da kake ikirarin kana yi mata na gaskiya ne to ka sakar min ita domin na tabbata rayuwa babu kai shine farin cikin Hudah na har abada...."
Zai yi magana tayi saurin taran sa da fa'din" Matu'kar kana so ka cigaba da rayuwa matsayin haifaffen 'dan halak to ka je ka 'dauki pen ka rubuta min sakin 'yata..."

Noor na jin Ammi ta fa'di hakan tayi saurin.matse hannun ta dake cikin.na Ammi, hawaye ne sosai yake zubo mata kan kuncin ta, bata so irin hakan ya dinga shiga tsakanin sa da iyayen sa amma ya zatayi? harga Allah bata jin zata sake jin da'din rayuwa tare da shi...burin ta ayanzu kawai shine taga bata 'karkashin inuwar auren sa.

A hankali Deen ya mi'ke  ya isa inda pen in yake ya dur'kusa hannun sa na rawa yana share hawaye yayi rubutu layi 'daya tak daga hakan ya mi'ke ya fice yana share hawaye bai ko sake kallon inda Ammi take ba balle Noor in.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *81*

Bin bayan sa da idanu Ammi tayi har ya 6acewa ganin ta, sannan ta dawo da hankalin ta ga rubutun da yayi, a hankali ta 'dago takaddan ta sada shi da idanun ta...

Wani tu'kukin bakin ciki taji ya mamaye mata zuciya...sakamakon ganin rubutun da yayi.
Saman la66a ta furta" Mu'een ya raina ni da yawa".

Abinda ya rubuta 'din yawo ya dinga yi mata aka, sake 'dago wa tayi ta karanta karo na biyu tana mai cize le6en ta na 'kasa.

Noor da bata san abinda ya rubuta ba a hankali ta 'karaso gaban Ammi ta dur'kusa tana kuka take ro'kan Ammi akan ta yafe masa kar tayi fushi da shi, tace ita ba nufin ta tsakanin su ya 6aci ba da shi bane, rayuwa da shine ka'dai bata so ayanzu...
Amma bata ce da ita 'kala ba kawai ta saki takkadan ya fa'do 'kasa dai-dai 'kafafun Noor, a hankali Ammi ta 'daga kafar ta tayi waje tana mai jin wani abu na taso mata, tausayin Noor gami da Danasanin bawa Mu'een auren ta da suka yi, ba kowa ce mace ba zata iya irin hakan, ace duk irin abinda yayi mata amma still burinta taga bai samu sa6ani da mahaifan saba, sa6anin matan yanzu da wasun su da kansu ma suke raba tsakanin mijin su da iyayen sa saboda son zuciyar su.

Kuka sosai Noor ta sha har kanta nayi mata ciwo mai tsanani, tana hawaye ta 'dago takkadan da Ammi ta jefar da niyyan ganin yawan sakin da yayi mata amma abinda idanun suka gani sosai ya bata mamaki take kakan ta ya tsaya cak, 'kurawa rubutun idanu tayi tana karamtawa tana 'karawa" _Kiyi ha'kuri.. bazan iya sakin ta ba Ammi_ ".
Abinda kawai ya rubuta kenan...cikin zuciyar ta ta furta _Allahumma ajirni fi musibati_ ...yayin da a fili ta furta" Wallahi ko babu saki tafiya ta zanyi bazan sake zama da kai ba".
Haka ta 'karashi kukan ta tayi shiru...zuciyar ta cike da haushin Yah Deen ji take tamkar ta sha'kesa.

Deen kuwa tunda da barin sa wurun Ammi direct 'dakin sa ya wuce ya 'dauki key kawai yayi waje.

Can wani gida can wani gidan sa da yake ginawa bai 'karasa aikin ba ya tafi da yake babu wani nisa sosai da gidan nasa na asali.

Babu komai a gidan na amfani, amma haka yake tahowa yayi zaman a duk lokacin da yaji abubuwa sun sha mai kai.

Safwan ka'dai ne kuma yasan da cewa yana ke6e kansa a wannan gidan.
Kuka ya dinga rizga kamar yaro 'karami gashi babu mai lallashi, tausayin Noor yake ji sosai, mai yasa Ammi bazata fahimce shi ba? tayaya zai iya rabuwa da Noor cikin wannan halin bacin yasan cewa komai da ya faru sanadin sa ne, meyasa bazasu bashi dama ya cika al'kawarin da ya 'dauka ba?...yasan sakin Noor a wannan ga6ar na iya haddasa mata wani matsananciyar damuwa ne saboda yasan dole tunanin Baby zai dame ta sosai ga kuma ace shima ya sake ta da wanne da zataji?

" Ammi ki yafe min amma bazan iya rabutawa Noor saki ba sam, nasan ni mai laifi ne sosai na sani, kuma ban cancanci afuwar Noor ba, bama ni da idanun.da zan iya duban ta in nemi afuwar ta.
Amma ya zanyi Ammi? Rabuwar mu da Noor bazai gyara komai ba, al'kawari nayi yanzu Ammi zan bar dukakkn abubuwan da nake aikatawa, wallahi ko garin Bauchi Noor tace mu bari zan bari saboda ita ina son sake ganin farin cikin ta..ina son matata ina 'kaunar zama da ita, iyace farin ciki na hasken raina...".
Haka yayi ta sumbatu kamar mahaukaci, duk ya fita hayyacin sa gaba 'daya, gashi yana jin ciwo amma ya basar saboda tsananin damuwar da ke cinsa...a hakan har bacci ya yi gaba da shi.

Sai cikin dare ya tashi ya alwala ya 'dauro sai da ya koma motar sa ya 'dauko dadduma sannan yazo ya sallaci sallar da bai yi ba.

Sai da ya 'kara da nafilfili haka ya dinga istighfari yana ro'kon yafiyar ubangijin sa da fatan ya daidaita masa rayuwar gidan sa yasa mahaifan sa su yafe masa fusgin da suka yi da shi.

Akan daddumar ya koma ya kwanta wani baccin ya sake 'daukan sa.

*****
Washegari su Ammi suka firfito da kayan su gaba 'daya har da na Noor dake ta faman share hawaye lokaci zuwa lokaci, Ammi sam bata damu da 'kin sakin Noor da Mu'een yayi ba ta riga tasa cikin ranta cewar ko bai sake ta ba bazata barta tare da shi ba.

Tun jiya Safwan ke ta 'kiran layin sa amma baya 'dagawa, abin ya 'daure masa kai sosai dan ko da safiyar yau ma sai da ya 'kira amma still bai 'daga ba, sanin da yayi cewa lafiya bata ishe shi bane yasa shi kamo hanyar gidan nasa da sassafe da zummar jin ko lafiya.

Yana zuwa sai ya tarar da kayan su Ammi a harabar gida, shiga yayi suka gaisa da su ganin su cikin shirin kuwa bai sashi mamaki ba cuz yasan da batun tafiyar, fahimtar da yayi harda Noor a tafiyan ne yaso sashi mamaki har ma ya kasa yin shiru sai da ya tambayi Ammi cewa tafiyar harda Noor ne?"
Kallon sa Ammi tayi tana 'dan ha'de rai tace da shi" Umm da ita zan tafi Safwan..ko so kake in barta ku 'karasa min ita a banza?"
Chapter 178 · 0% Book details