Sashe 121
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk maganganun Imrana ko guda daga ciki bai ji ta sau'kar masa da natsuwa ba...hakan yasa ma daga 'karshe ya daina fahimtar sa...sallama kawai sukayi ya ajiye wayar yana tunanin 'kiran Antyn sa Zainab dan yasan zata bashi shawarar da ta dace...sai dai ko giyar wake yasha ba zai ta6a 'kiran ta cikin wannan halin ba...dan yasan idan taji labarin kamar Uncle Ja'far yaji ne.
Shi fa tun bayan tafiyar sa makaranta bai sake tunawa da batun wata Ma'u ba balle abinda ya shiga tsakanin su..bai sani ba ashe harda ajiya yayi ajikin ta...abinda yafi 'daga masa hankali ma shine jin labarin cikin...sai kuma maganar da Alhaji Baba yayi kan cewa ya shirya da zaran Allah ya sau'ki yarinyar lafiya dolen sa ya aure ta ya ha'da ta da matar sa su zama biyu...In yaso yaje can shi ya sani...kuma ko da wasa ya kuskura ya cutar da guda daga cikin su bazai ta6a yafe masa ba...." _Yah Allah ka yafe min_ "
Ya furta a fili.
*****
Mamakin sa bai tashi 'karuwa ba sai da iyayen sa suka zaunar da shi bayan kusan 1 week da dawowar sa kan batun matar sa wai...karo na farko da magana ta ha'da shi da Ammin sa tun dawowar sa, inda tayi masa garga'di mai zafi kan 'yar ta ta kuma nuna masa cewa ba son ranta bane zaman sa da Hudah...kawai dai dan mahaifin ta ya matsa akan akai ta 'dakin mijinta ne bayaga haka da bata san mai zai sa ta ha'da jini da shi ba.
" _Da gaske auren ne da ni kenan?_ Ya tambayi zuciyar sa...kansa 'kasa lokacin da yji sunan Hudah ya fito cikin maganar iyayen nasa, ya so ya 'daga kansa saboda mamaki amma sam ya kasa bayyana mamakin sa a fili cuz har yanzu nawin mahaifan nasa yake ji...fatan sa Allah yasa ba wannan 6eran Hudahn da ke gidan su bane.
Kamar wasa abin shi dai kawai shiru yayi yana bin komai da idanu tare da sauraron kalaman nasu...duk da halin da yake ciki a lokacin amma hakan bai hana shi murmushin takaici ba da yaga zahiri cewa wai Hudahn Ammi ce matar sa...yaushe hakan ya faru sam bai sani ba.
Akan yarinyar nan ne shine Ammi ke cewa in ba dole ba bazata ha'da jini da ni ba?
Me Ammi ke nufi kenan?
Tana nufin yarinyar ce jinin ta ba ni ba?
Kansa 'kasa ya lumshe idanu take fuskar Nanne ya bayyana cikin brain 'din sa..." _Allah yayi miki Rahma ya sa hutun ki kenan_ "...Cikin zuciyar sa ya furta hakan yayin da a fili babu wani yanayi da zaka iya fassara shi saman fuskar sa.
Sam ya rasa dalilin da ya sa bai ji haushin komai ba koda labarin cewa Hudah matar sa ce isa kunnuwan sa...shi kansa ya kasa tantance ainahin halin da zuciyar sa take ciki kan hakan.
Harcya isa gidan sa yana tunanin yausgechakan ya faru? Yaushe aka 'daura auren sa da ita bai sani ba.
Tuno maganar da abokan sa suka yi masa ranar da suka dawo daga Azare wurin 'daurin auren sa ya sa ya zargi wani abu..." _Ai shi yasa nace maka mai abin mamaki domin har gobe ango kake mijin amarya kuma..."_
Maganar Anas ya tuno wanda ya fa'da masa ranar 'daurin auren saxda Husnah bayan suna da tabbacin cewa an riga an fasa auren sa da Husnah ...to mecyasa shi fa'din hakan kuma....?
Kenan duk 6oye minvsuka yi alhalin sun san gaskiya, sun san cewa da Hudah aka 'daura min aure kuma suka 6oye min.
Laifin Ishaq ka'dai yafi gani kan hakan saboda duk cikin su ya fi kusanci da shi....take ya 'kira shi a waya ya tambaye shi gaskiyar lamari.
Tunanin Ishaq ko a wai-wai yaji zancen shiyasa yaso 6oye masa but take Mu'een ya nuna masa cewa yasan komai amma miye dalilin su na 6oye masa iya tsawon lokacin nan..?"
" Kayi ha'kuri Mu'een..umarnin Alhaji Baba ne kuma kasan yafi 'karfin hakan a wurin mu shiyasa bamu sanar da kai ba.."
Tsaki yaja tare da yanke wayar ya ajiye gefen sa..kishingi'da ya koma yayi yana jin ba da'di...tun dawowar sa garin nan bai samu natsuwa ba...har 'yar rama yayi saboda ko abincin kirki baya samun lokacin ci ga damuwa da yayi masa yawa.
Ni kuwa gidan mu wurin Ummata aka maidani wai zanyi 2weeks acan kafin akaini gidan miji na...ban sa damuwar komai cikin raina ba...ni dai kawai abinda ba naso shine zama da shi, kuma ma tun kafin na baro wurin Ammi kullum sai ta kwantar min da hankali tana bani baki akan in daina tsoron sa kuma duk abinda ya min inzo in sanar da ita zatayi maganin sa.
Ban ta6a sanin cewa Yah Deen na da ala'ka da cikin jikin Ma'u ba har sai da na koma gidan Ummah ta...anan da muka ke6e da Addah ta Saudah take min gulmar wai ai su Ammi sun san cewa manemin mata ne shiyasa suka aura masa ni dan mugunta...yanzu kuwa da halin sa ya bayyana kowa ya sani cewa shine yayiwa Ma'un Malam Barau ciki shine kuma za'a wani ce za'a kaini gidan sa matsayin matar sa..."
Abin ya matu'kar kulle min kaina jin batun Addah Saudah...amma duk da hakan ban wani damu sosai ba...sai dai har yanzu cikin zuciya ta banjin cewa ina son zama da shi.
Nasan ma in ba dan Addah Saudan ba in dai dan Ummah ta ne bazata ta6a yimin zancen ba...banda ma nasihar zaman ha'kuri kullum babu abinda ke shiga tsakani na da ita.
Yayah Usman baya gari haka ma Baban mu...sai dai duk sun 'kira munyi waya da su kuma sun turo ku'din da za'a min siyayyar kayan 'daki na da shi...har Ammi taso hanawa wai ai wannan hakkin tane amma iyaye na suka 'kiya dole ta ha'kura amma tace ita zata min komai na kitchen ta ro'ki kar asayi komai.
Wannan 'din kuwa aka bar mata hakan ma da 'kyar Ummah ta ta amince..kusan kullum sai munyi waya da Baban mu inda da kansa cikin natsuwa batare da ya dubi 'karancin shekaru na ba ya bani kaf 'din labarin tun farkon dalilin kafuwar aure na da Yah Deen...saboda acewar sa abin ya shafe rayuwa ta ne kuma kar inga kamar ba'a yimin adalci ba.
Yace lokacin da Alhaji Mamman yaci amanar su ya bayar da auren 'yar sa ga wani sai dukkan su ransu ya 6aci gashi ba laifi sun gayyaci mutane da dama kuma kowa zaman sauraron jin 'daurin auren yake yi...yanayin da yaga Alhaji Baba abin sam bai masa da'di ba..yace to a lokacin sai yayi tunanin me ze hana a 'daura dani tunda duk matsayin 'ya'ya muke a wurin Alhaji Baban kuma ba haramcin auren tsakanin mu.
Yace Ja'afar 'kani ga Alhaji Baban ya ja gefe yayi masa bayani badan komai yayi hakan ba kuma sai dan rufin asirin juna...take kuwa Uncle Ja'afar ya amince kuma shine ya kai labarin kunnan Alhaji.
Take batare da 6ata lokaci ba aka 'daura mana aure kan sadaki dubu 'dari cif Alhaji Baba shine matsayin wakilin amarya yayin da Uncle Ja'afar ya wakilci ango...abin mamaki kuwa sai ya fahimci aure na da Yah Deen 'din yafi kwantawa Alhaji Baba arai fiye da wanda aka so yi a farko.
Ya fahimci hakan ne lokacin da Alhaji Baba yazo gaban sa ya rin'ka zuba masa godiya kamar wanda yayi masa wani gagarumin abu...tun a wurin ma ya fara bayyana masa abinda shi bai ta6a sani ba, wato soyayyar Deen ga Marigayiya Nannen mu...a lokacin ba 'karamin mamaki yayi ba da yaji wannan labarin sai dai ya fahimci komai Allah ne da shi kuma shike tsara komai...shiyasa ya yi sanadin ha'duwar aure tsakani na da Deen, kenan dama can ba Nanne bace matar sa ni 'din ce...tun daga ranar ya san cewa aure na Da Yah Deen ha'din Allah ne.
Alhajin da kansa ya nemi a rufe zancen saboda wani dalilin sa a lokacin yace da kansa zai bayyana idan yaga dacewar lokacin....wannan dalilin ne ya sa ba kowa yaji zancen ba har yanzu...sai dai duk da haka 'yan bani na iya na nan ma'kale suna juya zancen.
Yace kwatsam yana zaune sai yaga ana ta 'kiran sa awaya ana sanar da shi abinda ke faruwa...da farko ma bai yadda ba amma daga baya daya da yaga kusan mutane hu'du sun 'kira shi da batun kuma iri 'daya sai jikin sa yayi sanyi gankalin sa ya fara tashi, daga 'karshe ma kashe wayar sa yayi na tsawon kwanaki biyu yana nazari kan lamarin.
Yace yasan wasu daga ciki ba wai haka kawai suke 'kira dan su sanar da shi ba, ya fahimci harda munafukai masu nuna cewa kwa'dayin su yayi kai harda 'kafafu tunda gashi halin yaron ya bayyana a fili kowa ya sani...ransa ya 6aci sosai amma duk da haka bai ga wata mafita ba illah ya nemi a mi'ka ni 'dakin mijina wata'kila hakan ka'dai shine mafita shiyasa ya yanke wannan hukuncin.
Yace da ace ma wani daban da bai sani ba ne da babu yadda za'ayi bayan sanin mummunan halayyar sa still ya sake 'daukan aure ya bashi...amma Alhaji Baba yafi 'karfin haka a wurin sa darajar sa kuma Muhamnad ya ci saboda karamcin sa a wurin jama'ah da kuma mahalicci...yace Allah ne ka'dai shaidar sa kan haka bai ta6a yin niyya ko aikata wani abu saboda kwa'dayi ko son abin hannun su ba duk da yasan ba kowa ne zai fahimci hakan ba amma Allah ya sani... yana so kuma nima inyi ha'kuri...inyi ha'kuri inyi masa biyayya..in zauna da mijina lafiya yace duk abinda zai faru tsakanin mu kafin in kai 'karar sa wurin wani in fara kaiwa wurin mahalicci saboda shine babban gata na...Allah ya sani shi kansa a yanzu ba son zama na da yaron yake ba dayake lokacin da ya bada auren bai san cewa haka halayyar sa take ba sai daga baya, so ba yadda zaiyi domin raba aure bashi ne mafita ba...ya yi tawakalli ne kawai saboda Allah kuma fatan sa Allah ya dubi niyyar sa...idan ya so sai yasa sanadin aurena da shi ya shirya shi ya daina abinda yake yi...Addu'ar saxgare mu kawai itace ubangiji Allah ya bamu zaman lafiya ya saka fahimta tsakanin mu....".