← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 211

Sashe 188

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya shafe a 'kalla sati uku yana kwance ba lafiya kafin ya samu sau'ki sosai, kuma still Safwan ne ka'dai akansa, shike yi masa komai...Isahq kansa ba 'karamin.jinjinawa Safwan yake yi ba, kusan kullum sai sun yi waya da shi yana sake jin halin da Mu'een 'din ke ciki.

Alhaji Baba kam shiru 'kila har yanzun bai kammala tunanin da yace da Safwan zai yi ba ne, Safwan ba 'karamin rashin jin da'din haushin nuna halin ko'in kula da suka yi da Mu'een 'din yake yi ba hakan yasa bai kuma 'kiran su kan batun sa ba har yanzu.

Last week ma abokan sa suka zo duba shi su Anas wanda Isahq ya sasu zuwa duba shi dan shi baya kusa, sosai suka tausayawa halin da yake ciki.

Siahq na 'ko'kari sosai wajen.'kiran.Alhaki yana sake ro'kon alfarma ko Alhajin zai sassauta amma ga mamakin sa a kullum kalaman Alhajin basu canzawa.
Sake maimaita masa yake cewa shi bai wani ri'ke shi a zuciya ba, abinda yake aikatawa ai rayuwar sa zata ta illatawa ba wani ba, iyaka kawai ace 'dan wane ne so shi bai dame sa ba, abinda yake so da shi yanzu kawai shine takaddar 'yar sa da ya'ki bayar wa, yace matu'kar ya sakam masa 'yar sa shikenan komai ya wuce bashi da wata damuwa da shi.

Har zuwa ya sake yi musamman kan maganar amma still Alhaji na nan kan bakan sa bai canza ba.
Duk yanda ya so yasan inda Noor take daga bakin su kuwa 'kin sanar da shi suka yi, daga gidan sai ya wuce gidan Umman Noor, nan ma 'din duk bata sauya zani ba tamkar ha'din baki itama bata sanar da shi ba.

Layin Noor da yake da shi kuwa sam baya gaijayawa da gwada 'kiran ta, a ranar ma ya 'kira yafi sau hamsin amma baya shiga abin ya 'daure masa kai sosai.

Burin sa dama da ace ya same ta da nasiha zai mata sosai, bai kamata ace ta guji mijin ta ta bar shi cikin wannan halin ba..ita ce ya kamata ta fara tausaya masa ba wani ba, kuma ai abinda ya riga ya faru ya riga ya wuce so babu amfanin dawo da shi musamman da yake ya nuna nadamar sa a ganin sa in dai ba 'karshen sa suke son gani ba kam ai abin ya isa haka nan.

Safwan ya 'kira yayi masa bayanin komai inda ya 'kara da fa'din" Idan zai yiwu dan Allah ka fahimtar da shi, fushin iyayen sa a kullum baya zai rin'ka maida shi ta fannin rayuwa abin na damu na sosai Safwan bai kamata ya ja tsawon lokaci mahaifan sa na fushi da shi ba, tunda sun ce sakin Noor suke bu'kata kawai ya daure ya sake ta, may be dama Allah bai tsara musu 'karshen rayuwar su tare ba dan haka kawai ya ha'kura da ita ya nemi albarkar iyayen sa.

Shi kansa Safwan ya jima da yin wannan tunanin amma fargaban yanda Mu'een zai 'dauki abin ya sa shi kasa furtawa.

Wannan karon kam Ishaq 'kwarin gwiwa ya bashi yace idan kuma ba zai iya gaya masa ba kawai ya ha'da su awaya shi zai masa bayani.

Hakan kuwa akayi, Ishaq ne cikin natsuwa ya fahimtar da shi komai, a fili ya bayyana masa muhimmancin da iyayen sa ke da shi a wurin sa, ya tuna masa cewa su ne aljannar sa, ya kuma nuna masa illar biyewa son zuciya, yace idan Noor matar kace babu wanda ya isa ya raba ka da ita Mu'een, amma ayanzu ka bi iyayen ka ka aikata abinda suke so insha Allahu bazaka yi hasara ba, Alhaji ya nuna yafiyan on condition zai maka, sakin Noor ne zai sa ka samu yafiyar sa dan haka dan Allah Mu'een ka sake ta ko ma saki nawa suka bu'kata kayi mata, kaga idan suka yafe ka sai ka koma ga Ubangijin ka kuma ro'ki abinda yake alkhairi ne, tsakanin Hudah ko wata daban..ina ganin hakan zai fi maka, da ka zauna da fushin iyayen ka akan ka gwamma ka rayu babu Noor a kaf in rayuwar ka wallahi ko awurin Allah bazaka yi laifi ba...."

Idanu ya rintse da 'karfi yana jin zafi cikin zuciyar sa a hankali ya furta" Insha Allah zan yi yanda kace Ishaq, na gode sosai, nagode da 'ko'karin.da kuka yi a kaina Ubangiji Allah ya bar zumunci".

Tun kafin ya 'kara samun sau'ki ma ya matsa wa Safwan ya fitar da shi daga asbitin..wanda sosai ya 'kagara yaga ya shirya da mahaifan sa har ji yake tamkar basu ta6a shiri da su mai kyau ba...ya riga ya saduda a yanzun a ganin sa Noor tayi masa nisan da be san ta ina zai fara lalu6o ta ba...ya sawa ransa dangana ba dan ransa na so ba a ganin sa rabuwa da itan dole ta zame masa kawai.

Washe gari ya shirya ya taho Shuwarin, wannan karon shi ka'dai ya tafi, Safwan ma yayi-yayi da shi akan ya bari sai ya 'dan natsu jikin sa ya 'kara 'karfi kafin yayi tafiyar amma Mu'een ya'ki, haka ya tafi bai ko 'dauki kaya bama daga su Atm 'din sa da Magungunan sai 'dan abinda ba'a rasa ba,
ku'di masu nawi ya bawa mai gadin sa dan shi kansa bai san ranar daowar sa ba, ko da ya sake ta baze bar Shuwarin ba har sai ya samu labarin inda take...domin a ganin sa har yanzun akwai nawin ta akansa cuz bai nemi yafiyar ta ba, haka ya bi motar kasuwa kamar ba shi ba ya kama hanyan gida.

Cikin mota kuwa da ya rufe idanu sai yaga Jasmine 'din sa tana yi mai murmushi, in ya bu'de idanu kuma sai bazai ganta ba.

Sake lumshe idanu yayi
Cikin ransa yake ayyana hala dai kin zo tuna min da batun zuwa makka da Madinan ki ne Mama na...na riga nayi al'kawari amma Allah bai nufi zaki je ba...sai dai insha Allahu nayi maki al'kawarin Mummyn ki zata je zata cika miki burin ki..ko da bama tare...Mummyn ki ta guje ni tace bata so na yanzu".

Murmushi kawai take yi masa amma bata fa'din komai...i missed u Maman Daddy..".
Ya sake furtawa 'kasan ma'koshin...yana jin tamkar hawaye zai zubo masa.

Allah ma ya taimake sa ba sosai yake maganar ba da ba babu abinda zai hana sauran fasinjojin jiyo abinda yake fa'di.

May be suyi tunanin ko ba lafiya yake ba ganin.shi ka'dai yana surutai.

Da wannan tunanin har ya kai gida tunanin Baby fal a ransa..Allah ya ji 'kanki mama na..".
Shine abu na 'karshe da ya furta bayan ya shigo garin Shuwarin...domin tunanin Jasmine ne ya dawo masa sabo fil.

Tun daren ranar da ya iso ya 'dauki takadda ya rubuta sakin Noor kamar haka..." _Assalamu alaikum ...ni Muhammad Mu'inuddeen na saki mata ta Noorul Hudah Mamman Jaji saki 'daya tak batare da tai min laifin komai ba.._ ."
Ninke wa yayi yana jin suka azuciyar sa har ruwa ruwa idanun sa ke yi saboda tsananin damuwar da yake ciki...wai yau shine da kansa da hannun sa ya saki Noor 'din sa? Jin abin yake tamkar cikin mafarki.

Bai sake fita daga 'dakin sa ba ya zauna yana alhinin sakin Noor da yayi, da yake tun maghrib suka ha'du da Alhaji so ba bu'katan komawa wurin sa ayanzu.

Yana zaune akan kujera hannun sa ri'ke da takaddan sakin Noor in sai yaga wayar sa na haske alamun 'kira ya shigo masa wanda a yanzu sosai ya tsani yaji 'karan abu ma kusa da shi, shiyasa ko wayar sa ma silent take koda yaushe.

Sunan Jiddah da yaga yana yawo kan fuskar wayar ne ya sashi jin wani tukukin bakin ciki ya kamashi...'dan 'karamin tsaki ya sake yana mai sake maida idanun sa ya lumshe.

'Kiran na yankewa a take wani ya sake biyo baya.
A zuciye Mu'een ya kai hannu ya 'daga wayar ya kai kunnan sa, bai ko jira yaji abinda zata ce da shi ba yace mata"...Idan kika sake kuskuren 'kiran wayata wallahi Uban ki zanci, useless kawai marar hankali..."

Daga haka ya yanke 'kiran yana huci kamar dole aka sanya shi.
Ni dai nace an kwan biyu ba ayi ba yau kuma kan Jiddah aka rage wutan masifar.

Jiddah kam daga can 6angaren kuka ta sanya, sosai Allah ya jarrabi zuciyar ta da 'kaunar sa fiye da zaton mai karatu, gani take kamar in ba shi bazata iya rayuwa ba, hakan yasa yanzun ma da ya zage ta har bata san lokacin da ta saki kuka ba saboda takaici, tun ba yau ba tayi danasanin turawa Noor wa'dancan Video da pic in, domin tun ranar har yau bata sake samun kansa ba, bata sake samun magana mai da'di daga gare shi ba...abin na damun ta sosai.

Da tasan abin kanta zai dawo ma da tun farko bazata fara ba, tana son shi sosai ta yadda ta tsani komai da zai iya shiga tsakanin ta da shi...zuwa yanzun kuwa ta fahimci tsananin soyayyar da yake yiwa matar sa, cuz a tunanin ta tun case 'din wancan Videon da ta tura in ne ya sa har yanzu bai dawo Abuja ba, kusan 3months kenan yanzu, sannan wayoyin sa ma ba a ko wani lokaci take samu ba, sau tari kuma ko ta 'kira ma ba 'dagawa ake yi ba, yau ne ta samu ya 'daga shima 'din sai ya bita da hargagi batare da ya ko saurari abinda ke tafe da ita ba.

Mummyn tane tayi saurin shigowa 'dakin jin tashin kukan ta lokaci guda wanda take yin sa cike da takaici.
Chapter 188 · 0% Book details