← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 211

Sashe 38

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Bangaren Tahir kuwa lokacin da ya dawo daga tunanin a lokacin ya fahimci cewa Manager ya jima da barin wajen dan haka a hankali shima ya taka ya isa gaban motar sa da niyyar komawa Kaduna, har zai bu'de motar ya shiga sai kuma ya fasa.

Rufe ta yayi ya koma bakin titi ya tari taxi zuwa unguwar tasu inda ya ringa nuna wa mai taxi 'din hanya har kan layin nasu.

Nesa da gidan ka'dan ya tsaya ya dubi yanda gidan duk ya lalace bai 'kara mintina biyar masu kyau ba ya umarci mai taxi 'din fa'din su tafi kawai bai samu numbern wanda yazo gurin sa ba, ko mai taxi 'din Tahir bai yi saken da har ya gane abinda ya kawo shi layin ba kuma koda suka koma daga can bakin titi ya sau'ka inda ya gangaro da 'kafar sa ya dawo ya shiga motar sa take ya wuce Kaduna, Sallar la'asar ma a Zaria ya tsaya yayi ta daga nan ya wuce abinsa.

Yanzun kam da ya koma bai 6oyewa Ammi komai ba duk ya bata labari inda take ta sanya kuka tana dafe kai jin cewa ana neman su ne kunsan mata da tsoro.

Sai da yayi ta kwantar mata da hankali kafin ya samu tayi shiru amma ta kasa sakewa dan ko da dare ma kasa bacci tayi saboda tsoro.

Washegari ya fita bayan sun gama yaje ya saida motar dake hannun sa, sannan ya biya Bank ya ciro ku'da'den da Manager ya bashi check jiya na dubu 'dari 'daya daga ya koma masau'kin su kusan la'asar a lokacin inda yaje ya samu Ammi zazza6i sosai ya rufe ta.

Batare da 6ata lokaci ba suka wuce asbiti.
Inda bayan gwaje-gwaje da 'yan tambayoyin da likita yayi mata sai ya bisu da albishir 'din cewa tana 'dauke da juna biyu na kusan wata uku.

Murnar da sukayi har sai da ya kusan mantar da su damuwar da suke ciki.

Da komawar su sai Tahir ya 'kira Ja'far ta landline 'din dake gidan sa ganin lokacin ba lokacin aiki bane, anan ya sanar dashi komai duk abinda ke faruwa.

Shima Ja'afar 'din sosai ya damu da jin abinda ya farun....ganin kamar zai ja maganar cikin tashin hankali ne ya sanya Tahir dakatar dashi da albishir 'din cikin da Ammi ke 'dauke da shi.....ai kuwa take yanayin sa ya canza amma duk da haka farin cikin bai hana shi tambayar inda suke ba.

Jin cewa suna Kaduna a dai-dai lokacin ya sanya hankalin sa kwantawa gami da yiwa mahalicci godiya.

Bayan kwana uku da faruwar hakan suka tattara suka wuce can jihar Bauchi batare da sun sake tsayuwa cikin gari Kano ba.

Sai da suka sau'ka a gurin Ja'afar suka 'dan huta kafin suka 'karaso garin Shuwarin mahaifar su ta asali.....inda Ja'afar yayi-yayi da shi akan ya bari kawai su zauna tare amma Tahir ya'ki amincewa sam dole tasa Ja'afar ya ha'kura badan ya so ba da kansa ya shigo dasu suka sau'ka gidan mahaifin su dake can bayan makaranta.
Su biyu kawai suka taho batare da su Ammi ba sobada gidan na matu'kar bu'katan gyara dan an jima ba'ayi amfani da shi ba.

Nan Ummah taja dogon numfashi tace " to kunji dalilin dawowar Alhaji Baba garin nan da zama, bakomai bane face sharrin ma'kiya".

Dukkan mu shiru mukayi ni kam harda tagumi duk muna kallon Ummah yayin da fuskokin mu ya cika da tausayin su jin irin yadda suka sha fama da rayuwa.

Ummah bata bi ta kan mu kawai ta ci gaba da labarin ta.

" Sai da suka nemi masu aiki suka bada aikin gyaran gidan bisa jagorancin mahaifin ku sannan suka koma Azare.

Cikin sati guda aka gyare gidan tsab kamar bashi ba da yake ma 'karamin gida ne ba babba ba shiyasa gyaran bai 'dauki lokaci ba, ai kun gane gidan ko....wancen gida mai fenti dake nesa ka'dan da makaranta?"
Ta 'karashe maganar da sigar tambaya.

Nanne kai ta 'daga yayin da ni.kuma nace " ehh Ummah nagane shi kullum idan zani makaranta ai ina ganin sa a rufe".

Ummah sai tace " Yauwa to wannan shine gidan da Alhaji Baba ya fara zama bayan dawowar sa garin nan, kuma anan Ammi ta haifi 'yan biyun ta wato....Saifullahi da Zaidullahi".
Murmushi Ummah tayi tace min " abokan wasan Hudallahi".

Nima 'din murmushin nayi jin sunan da ta 'kira ni dashi.....kuma ya min da'di...dan bata cemin hakan ba sai yau.

"......Sai dai koda Alhaji Baba ya dawo nan bai taho da 'dan sa dake gurin 'kanin sa Ja'afar ba, dan Ja'afar hana musu shi yayi musamman saboda karatun sa shiyasa har yanzu baku san shi ba....."
kallo na Ummah tayi tace " ko ke dake zuwa gidan kin ta6a ganin sa?"

Da sauri na girgiza kaina gami da fa'din " ah ah".

Sai ta cigaba da fa'din ko hutu ma ba'a kawo shi idan sunzo tare suke komawa da iyayen nasa basa barin sa anan koda ana hutu sai suce akwai makarantar islamiya....Alhaji Baba ma bai damu ba dan yasan ilimi shine hasken rayuwar 'dan Adam, Ammi kuwa da take ganin 'yan biyun shikenan sai suka 'dauki hankalin ta bata damu sosai da shi babban ba, musamman ma da yake tana tausaya musu saboda rashin samun haihuwar su shiyasa take ganin dama a bar musu shi kawai su ri'ke shi.

Tun zuwan Alhaji Baba garin nan bashi da abokin da ya wuce Baban ku, shine ka'dai suke zama suyi hira wanda har hakan yasa da kansa ya bashi labarin duk abinda ke faruwa da rayuwar sa, Baban ku ya tausaya masa sosai.

Koda ya nemi shawarar abinda zai rin'ka yi yana juya ku'd'den sa sai Baban ku yace bari yayi tunani.

Ganin ba zai iya noma kamar yadda su suke yi ba ya sanya washegari da suka ha'du ya bashi shawarar yayi gidan gona tunda shi rani da damina ana cin moriyar sa in yaso sai yayi na dukkan 6angarorin biyu, wato lambu da kuma kiwo za'a fa'da'da gurin sosai ta yadda babu wanda zai cutar da wani acikin su.

Sosai Alhaji Baba ya ji da'di shawarar Baban ku, dan kuwa kafin sati uku su cika har an nemi filin gona mai girman gaske an siya har an katange shi sauran aikin cikin.

A hankali ake yin komai kafin 3month kuwa komai ya kammala an raba filin 6angare biyu.

Kaji kala suka zuba farko guda dubu biyu...sannan suka yi shuke-shuke aka dasa wasu kama daga kan albasa, carrots sweets potato, abubiwa da dama suka fara dasu, gefe guda kuma aka daddasa su ayaba da sauran su wa'danda zuwa yanzun sun girma sun zama bishiyoyi masu masifar ni'ima a wurin.

Ma'aikata kusan talatin aka zuba kowa da 6angaren sa.

Karon farko da Alhaji Baba ya fitar da kajin sa ba 'karamin riba ya samu ba wanda hakan ya sanya shi 'karo wasu masu yawan gaske kamar da wasa sai gashi yana samun alkhairi da dama.

Lokacin da kajin sa na 'kwai suka fara 'kwai abin ba'a cewa komai....'diba kawai suke yi safe da yamma babu 'ka'k'kautawa.

Dalilin hakan ne ya sanya shi yiwa mahaifin ku alkhairi na zunzurutun ku'di har dubu hamsin, wanda da 'kyar Baban ku ya amshi ku'din....dubu goma ka'dai ya 'dauka ciki ya dam'ka sauran hannun yayan ku Usman yace ya 'kara akan sana'ar sa.

Wani filin Alhaji Baba ya 'kara siya ya tada ginin na zamani kafin a shekara kuwa ya gini ya kammala gaba 'daya.....sai da ya gama zuba komai aciki na amfani kafin suka tattaro suka dawo ciki inda aka kulle wancan gidan shiyasa har yau kuke ganin sa a kulle babu kowa ciki.

A dai-dai lokacin ne kuma Alhaji Baba ya samu labarin rasuwar Manager inda a lokacin ma ya kai kusan wata shida da rasuwa, Ja'afar ne da yaje Kano ya samo labarin.

Alhaji Baba ya tausaya masa musamman da yaji cewa wai cikin sa aka soka da wu'ka har cikin gidan sa yasan babu mamaki aikin *Kido* ne wannan, addu'ar dacewa ya bisa dashi sannan ya ro'ki Allah ya tsare masa marayun 'ya'yan sa dama shi kansa da abin ya kasance sanadin sa ne.

Sai dai bai gayawa
Ammi ba dan baya son hankalin ta ya tashi, ganin yanzu ta kwantar da hankalin ta baya son sabuwar damuwa kuma...dan haka sai ya ri'ke abin cikin ransa bai 'kara sanar da kowa ba.

Gidan gonar Alhaji Babba sosai albarkar Allah ya sau'ka a kansa shiyasa a kullum take 'kara habbaka da yin suna a fa'din garin Bauchi.

Bai yi 'kasa a gwiba wurin siyan manyan motoci guda biyu ya bayar ana zirga-zirga da su jahohin kudanci shiyasa a kullum ka ganshi bazakace mazaunin 'karamin gari kamar nan bane.....gashi da karamci da son mutane ga kyautatawa jama'ah gaskiya halin Alhaji Baba sai godiyar Allah........."
Ummah na kaiwa nan sai ta dubeni tace " kinji ko Hudah, ai yanzu kam kin fahimci dalilin da ya sanya rayuwar Alhaji Baba da iyalan sa ta banbanta da ta mu ko?"

" ehh Ummah na fahimta yanzu".
Nace cikin sanyi.

Sai tace kunga ba dan wani ikon Allah ba ma da nasan babu abinda zai sa shi dawowa nan garin da zama amma rayuwa ta kan juyawa mutum ne a duk lokacin da taso shiyasa ake son bawa ya ri'ki imani da 'kaddara cikin kowani hali na rayuwa".

Nanne ce tace hakane Ummah Allah yasa mu dace".

Dukkan mu muka amsa da " Amin".

Baban mu dake tsaye tun da jimawa wada bamu san ma da tsayuwar shi wurin ba murmushi yayi shima gami da jijjiga kansa sannan ya 'karaso ciki da sigar wasa yace da Ummah " kinyi mantuwa".

Kallon shi mukayi gaba 'daya da mamaki yayin da Ummah cikin sauri tace
" Me na manta kuma?"

Sai Baban mu yace " Riba ta mana.....kin manta nike kula da 6angaren Kajin ne?"

Dariya mukayi dukkan mu har Ummah sannan muka mi'ke muka bar wurin.

*****
Ban san me yasa ba amma tun ranar da naji tarihin Alhaji Baba sai na 'kara jin mutumin ya shiga raina sosai, duk da 'karamcin shekaru na amma hakan bai hanani fahimtar labarin nasu ba.
Chapter 38 · 0% Book details