Sashe 107
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka Imrana yai ta tsokano shi wasu lokutan shi kuma yace" Wallahi sai in fasa"
Da yaji haka zakiji yace" Sorry Boss na daina"
Da gaka har suka gama aikin.
*****
Shirye-shiryen biki ya kankankama daga dukkan 6angarorin biyu, Baban mu ana saura kwana biyu bikin ya iso Shuwarin kamar yadda tayiwa Alhaji al'kawari, haka ma Uncle Ja'afar shima tazo Anty Zee kam dama mun da'de tare da ita inda wani sha'kuwa mai 'karfi ya shiga tsakani na da ita, duk abinda tasan zai fito dani abikin tuni ta tanadar min shi.
'Bangaren Ma'u kuwa ta 'dan damu ka'dan da ta ji batun auren amma daga baya da kanta ta yiwa kanta karatun natsuwa tayi ta 'ko'kari wajen ganin ta cire a tunanin ta...sai dai abin ya faskara dan son shi takeyi ita da dukkan zuciyar ta.
Duk da haka bata 'daga hankalin ta ba ta kuma yi 'ko'karin 6oye damuwar ra musamman da take tub farko dama can rasan haukar ta kawai takeyi amma aure tsakanin su abu ne mai wahala.
Dalilin sanin hakan yasa ta 'kara watsar da batun harma ta yiwa kanta al'kawarin kasancewa cikin 'kawayen Hudah aranar bikin ko dan ta samu ta manta da shi, dama ta san da kyar ne ya aure ta tunda shi kyakkyawa ne kuma mai aji ba irinta da take girman 'kauye ba.
Ana gobe 'daurin auren aka kawo mai lalle tayi min ni da Anty Zee da Ammi, kar kiga yanda abin ya amshi jikin mu Muka fito shar abin mu.
Already dama an gama gyare min kaina, Ghana weaven Ammi tace ai min da abin 'karin gashi, kitson 'yan madaidaita ne amma tuni sun canza min kamanni na zama tamkar wata 'yar gayu, Ammi data ganni kawai sai ta rungume ni tana fa'din" Masha Allah, 'yan matan Ammi ansha kyau sosai".
Da wayar ta ta 'dauka min photo ina dariya na 'dago hannu na 'daya kaina babu ko 'dan kwali.
Pic 'din yayi kyau sosai kamar ba ni ce NOORUL HUDAH 'yar gidan Ummah mai waina 'din nan ba, tuni na juye na zama wata kyakkyawa da ni.
Da'di naji lokacin da naji Ammi na ta yabe ni sai kawai na saki murmushin jin da'di.
Da yamma su Ishaq suka iso da motar su da suka 'dauko daga gidan su Anas da yake shi dama cikin gari gidan su yake shiyasa suka saki ransu suka taso a lokacin da suka ga dama.
Haka kawai Mu'een sai yayi farin ciki da zuwan su, gefe ma ga Imrana da tawagar sa abin ba'a cewa komai.
Sai dai duk abin nan su Saif na makaranta basu dawo anyi dasu ba, ni kuwa ba 'karamin kewar su nayi ba haka na damu Ammi da batun su tace inje in samu Alhaji in gaya masa.
Ai kuwa zuwa nayi nace" Alhaji Baba yaushe za'a 'dauko su Saif?"
Murmushi yayi min tare da fa'din" Hudallah me yasa kike so a 'dauko ko saboda bikin Yayan naku?"
Kai na na 'dage alamar " Erh".
Murmushin ya sake yi sannan yace" Bar su kawai suyi karatun su...wannan bikin duk shirme ne ki bari sai wanj lokacin in da rai ayi da su kinji".
Kqfa'da na no'ke..zan yi magana sai yayi saurin fa'din" To je ki sami mai auren ki fa'da masa ya 'dakko su".
Ina jin haka na nutsu sannan na koma inda na fito dan tuni na ha'kura da zuwan nasu indai sai naje na sami Yah Deen kan maganar.
Na ha'kura nace kawai ko a wayq zan bash labari.
*****
Ranar ko bacci su Yah Deen ba su yi ba suna ta shan hira abin su kun san abinku da abokai idan an ha'du sai a hankali.
Washe gari bayan sallar asubah ne kowa ya koma bacci har kusan sha daya suna bacci babh wanda ya tashi illah Imrana, hatta breakfast ma da aka kawo musu babu wanda ya waiwaye shi sai Imranan ka'dai.
Sha 'daya suka ta shi a baccin wanda Ishaq ne ya fara tashi sannan ya tada su.
Comment
Vote nd Share.
*Salmerh ce* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *51*
Ganin kamar sun kusa makara ne ya sanya shi tada su gaba 'daya tare da fa'din kowa ya hanzarta yayi shiri kar a tafi abar
su abaya.
Sharp-sharp ya shiga wanka ya fito da yake bathroom 'din ma biyu ne sai suka rarraba suka hau shirin zuwa 'daurin aure gadan
-gadan.
Sai dai me? Mu'een 'kin motsawa yayi yai kamar baya jin me suke yi kwata-kwata.
Har Ishaq ya kammala shirin sa cikin yadi getzner Kalar ruwan madara da suka yi ankon sa tsakanin
su batare da ko shi angon ya sani ba.
Duk yadda ya so ya ja hankalin Mu'een kan cewa ya tashi ya shirya amma Yah Deen sam ya'ki kula shi balle ya bashi ha'din kai, sai ma cewa da yayi suyi gaba kawai zai taho shima yana bayan su.
Haushin sa sosai Ishaq yaji kan hakan kawai ya fice ya bar shi suka wuce can gida bayan sun ci abinci.
Sanin da yayi cewar Alhaji ko Uncle dole ne cikin su 'daya sai ya neme shi, dalilin hakan ya sanya shi bayan fitar sun yayi hanzarin shiryawa cikin 'daya daga cikin kayan da Uncle ya kawo masa tsadadden yadi mint green ya sanya wanda akayi 'dinkin harda babban riga.
Sosai kuwa ya yi kyau ya fito shar da shi...turaruka ya dinga fesawa kala-kala ajikin sa bayan ya kafe hula akan sa ta zauna 'das, yana baza 'kamshi Imrana na zuba masa kirari suka fito sai wani shan 'kamshi yake yana takun isa da 'kasaita cikin babbar riga tamkar ba shi ba, Imrana bai barshi ganin kyan da yayi ya sa shi yin gaba ya ringa haska masa pic da wayar sa inda yana tahowa Imrana na haska photunan sai ya wani ha'de gira, mota suka shiga a tare wanda shine yayi driven motar ya bisu da yake akwai wata motar Alhaji a hannun sa sai suka isa gidan ba tare da wani 6ata lokaci ba.
Ai kuwa ba 'karamar sa'a yayi ba dan kuwa har Uncle Ja'afar ya fara tambayar sa wurin su Ishaq sai gashi ya 6ullo...da ganin sa cikin shiri kuwa sai fara'sr sa ta fa'da'da sosai bai yi rowar baki ba sai da ya yabawa kwalliyar tasa.
Gaishe su yayi da duk jama'ar da ya gani 6angaren Alhajin fuskar sa ba yabo ba fallasa ba zaka ta6a cewa baya 'kaunar auren ba ko kuma kayi zaton da akwai wani 6oyayyen sirri cikin ransa ba.
Suna kammalawa da. gaisuwar Imrana yace suyi photo..." Kafa dame ni Imran".Yace a dake ya wani 6ata ransa.
Imran kuwa yace sai kuma an 'dauka ba...bai jira jin komai daga Mu'een ba ya juya ga su Ishaq da Uncle Ja'afar sannan ya cigaba da fa'din" Uncle muyi photo mana da su Alhaji.."
Murmushi Uncle J yayi nan ya matso batare da musu ba aka 'dauke su,
Yah Deen kam dan ba yadda zaiyi ne shiyasa ya tsaya, haka aka 'dauke su harda Alhaji Baba da su Baban mu cikin waya ce amma sunyi kyau sosai...da yake babu wanda ya tuna 'dauko camera man...duk haushin Imran kuwa ya bi ya cika shi kafin a 'kare 'dauka dan acewar sa ai duj tsirin sa ne, haka yana ciccin magani har aka 'kare.
Sai da ya tabbatar ya ha'da idanu da kowa cikin iyayen nasa sun tabbatar ya shirya ya fito hatta cikin gida sai da ya shiga ya gaida su Ammi kafin ya fito...sannan ya faki idanun su Uncle ya shige mota shi da Imrana suka koma can gidan sa bai sake komawa ba...kaf kayan da yasa 'din kuwa da dawowar sa duk ya cire su ya zauna abinsa da singlate da dogon wandon jumpan kawai.
Duk yadda Ishaq ya so su tafi tare amma Mu'een ya 'ki sam ya ringa kakkaucewa, har gidan suka dawo yayi ta nuna masa abinda yake yi 'din bai dace ba amma Yah Deen kam sai yace su je yana bayan su, hakan yasa yayi zuciya ya tafi abin sa...cuz taurin kai irin na Mu'een ya fara isan sa...musamman ma yanda yaga har ya cire kayan jikin sa ya mi'ke a kujera yasan da 'kyar ne ma idan yana da niyyan halattar 'daurin auren.
Su hu'du kacal suka tafi daga 6angaren sa, yayin da aka bar shi daga shi sai Imrana a gida da sunan zasu taho daga baya, sai da yaga sun fita kafin ya tashi ya zauna yana wani mi'ka kamar wanda ya shekara guda yana bacci...yana cikin hakan kuwa yaji wayar sa ta fara Vibrating, zaton sa ma ko Ishaq ne.
Sai dai yana dubawa yaga Uncle Ja'afar ne ya 'kira, zuciyar sa na dokawa ya 'dauki 'kiran gami da ha'da wayar da kunnan sa, nan yaci karo da muryar Uncle J na fa'din" Mu munyi gaba kasan sallar jumma'ah na gaban mu kuma ban ganka ba, so ku hanzarta tahowa kar ku makara....ya 'karashe da sanar da shi sunan masallacin da za'a 'daura auren.
Da " To" kawai ya amsa shi, bawai dan yana da da niyyan halatta ba a a, sai dan kawai baya son wani dogon bayani kwata-kwata.
Hirar su suka cigaba da yi cikin kwanciyar hankali shi da Imrana, har lokaci ya 'kure sosai sannan suka ankara, da gaggawa ya tashi ya fa'da bayi da fitowar sa kuwa ya sake shiryawa dan Imrana kam dama kayan sa na jikin sa tun da ya shirya 'dazu riga kawai ya cire kuma har ya maida abinsa ma.
Cikin kayan da Anty Zee ta bashi ya sake za6an wani mai kyau wanda babu babbar riga ya saka ajikin sa, ba wai dan yau 'daurin auren sa ba ne ya sashi sanya kayan a a sai dai dan kawai yana so ya sallaci Jumma'ah da shi kamar yadda ya saba yin shiga ta musamman duk ranar kowacce Friday.
Suna isa masallaci aka tada sallah kamar dama su ake jira su iso.