Sashe 198
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin ko maganar kirki Mu'een baya iyawa, da idanu kawai yake bin komai.
Bayan 'kiran da Saif yayiwa Uncle da kwana biyu sai ga shi ya dira Abuja dan hankalin sa ya kasa kwanciya, a zihiri lokacin da Saif 'din ya 'kira shi bai ce da shi uffan ba but daga baya abin sai ya dame shi sosai domin ya fahimci akwai abinda ke faruwa dole sai da ya yanke shawarar tahowa.
Lokacin da ya iso ma Mu'een bacci yake yi, ba'a barin kowa zuwa inda yake saboda ciwon san ba mai son hayaniya sosai bane hatta Saif 'din ma ba koda yaushe ake barin sa shiga inda yake ba, amma yanda Uncle Ja'far in ya matsa dole sai da suka barshi ya shiga wajen sa.
Gaba ya sashi ya na kallo, tausayin sa duk ya mamaye masa zuciya duk yayi ba'ki ya rame daga inda yake yana iya hango 'kasusuwan dake 'kirjin sa da wuyan sa in ma irgawa akace masa yayi tsaf zai uya irga su, uwar rama yayi fiye da zaton mai karatu, ji yayi tamkar ya zubda mai hawaye, gaba 'daya jikin sa sai yayi sanyi, wannan idan ba dan farin sani da yayiwa Mu'een ba idan akace masa shine sam ba zai yadda ba.
Ido kawai ya tsura masa yana sake 'kare masa kallo.
......Alhaji Baba ma sau biyu yana zuwa duba shi amma baya wani 'daga hankali da ciwon nasa sosai, gara ma wani lokaci da yayi wata doguwar suma Saif duk sai ya rirkice he thought mutuwa Yayan nasa zaiyi, sai da ya 'dauki sa'oi ashirin da bakwai kafin ya farfa'do wannan lokacin ne me Alhaji Baba ya nuna damuwa sosai cuz hadda Ammi suka zo suka duba shi, itama kuka ta ringa yi tana 'karawa, bata san ina zata sanya tausayin 'dan nata ba.
A hakan bata ta6a kuskuren sanar da Hudah abinda ke faruwa ba, ko waya zatayi da ita tana 'ko'kari sosai wajen ganin ta daidaita muryar ta...ko da Anty Zainab ma sai dai taji labarin ciwon.nasa a wani wuri amma Ammi bata ta6a sanar da su saboda tasan tare suke koda wanai lokaci dole idan 'daya yaji 'dayan zai ji.
Hikimar ta anan kuwa shine wai m kar Noor taga tamkar tana son dawo da ita cikin rayuwar Mu'een ne shiyasa bata yadda ko zancen sa ya ha'da su.
Shima Uncle Ja'afar in sai yanzu da yake zaune gaban sa sannan ya ke jin haushin kansa ma, ai kuskure ya kan zama kuskure ne idan mai aikata shi ya kasa canzawa, yanada ya'kinin yanzu Mu'een ya canza rayuwar sa gaba 'daya, ha'ki'ka bai ji da'din abinda Deen 'din ya aikata ba shiysa ransa ya 6aci sosai cuz ko a mafarki be ta6a tunanin har Mu'een na iya 6ata rayuwar sa ta hanyar biyewa matan banza ba, shiyasa ya kasa bashi fuskan da zasu fahimci juna...
Yanzun kuwa da yake jin 'kaunar yaron sa gami da tausayin sa na sake ratsa shi hannun sa ya kamo cikin nashi yana shafawa a hankali zuciyar sa duk tayi rauni ya karaya gaba 'daya.
A hankali Mu'een ya bu'de idanun sa, jin hannun sa cikin na mutun sam bai sashi mamaki ba dan yasan Saif na nan tare da shi...bai bu'de idanun sa ba dan ra'dadi suke yi masa sosai...sai da ya 'dauki tsawon lokaci kafin ya bu'de idanun a hankali.
Dishi-dishin da yake gani ne ya sashi sake maida idanun ya rufe amma a hankalin sa sai ya tafi kan wanda ya gani zaune kusa da shi, sam girman jikin sa ba irin na Saif bane.
Bayan wasu da'ki'ku ya sake bu'de idanun tare da 'dan motsa hannun sa dake cikin na mutumin...nan take ya 'dago kansa, ha'da ido yayi da Uncle 'din sa da ya jima bai ganshi kusa da shi kamar hakan ba, ido ya tsura masa tsawon lokaci yana duban sa, sai yake ganin tamkar a mafarki...kasa gaskata idanun sa yayi dan haka sai ya maida su ya kuma kullewa siraran hawaye suka gangaro masa ta gefe da gefen fuskar sa.
Uncle J goge masa hawayen ya fara da sauri yana yi masa magana cin murya mai kwantar da hankali.." Kayi ha'kuri Baba na insha Allahu bazan sake yin fushi da kai ba..ni da kaina nasan nayi kuskure may be ma fin wanda kayi...na dawo gare ka yanzu kaji ka kwantar da hankalin ka insha Allahu farin cikin ka zai dawo soon..."
Gefe yayi da kansa batare da ya sake kallon inda Uncle in yake ba yayin da hawayen sa ke cigaba da gangarawa...Uncle bai damu da hakan da Mu'een yayi masa ba dan yasan shima sam bai kyauta masa ba...wayar sa ya ciro ya 'kira Matar sa wanda tana 'dauka yayi saurin fa'din" Meet ur Mu'een.."
Bai jira jin komai daga gare ta ba ya sanya wayar a speaker ya kai kuda sa da shi.
Anty Zainab tsabar farin ciki bata san lokacin da ta zauna daga tsayen da take ba...'kirjin ta ta dafe ta wani sau'ke ajiyan zuciya tana murmushin jin da'di, bayan wani tsawon lokaci yau ga Mu'een da Uncle 'din sa zaune wuri guda ga dukkan alamu komai ya daidaita tsakanin su kenan abinda ta jima tana fatan faruwar sa sai yau Allah ya cika mata burin ta.
....a hankali take jin hucin numfashin sa na sau'ka ta cikin wayar amma bai ce da ita komai ba... Sunan sa ta 'kira da sanyin murya amma bai amsa ta ba...." Talk to me pls Mu'een kar kayi fushi da ni, kasan haka kawai bazan share ka tsawon wannan lokacin ba ko/ dan Allah kace min wani abu...".
Noor da ke cikin 'daki fitowar ta kenan sai taji Anty na ro'ko a waya ido ta 'dan zaro tace" Anty ke da waye haka?"
Tayi maganar tana nufo inda Anty Zainab take ganiana yanda ta tattara dukkan hankalin ta kan wayar harda hannu biyu ma ta ri'ke wayar tamkar wacce akace mata za'a 'kwace ne.
Anty Zainab kam ma hankalin ta sam bai je ga maganar Noor ba, dagsken duk ta bada hankalin ta wajen sa amma still ya'ki cewa komai.
Shi kam jin murya kamar ta Noor 'din sa cikin wayar ne ya sanya shi nutsar da zuciyar sa wuri guda, ido ya 'dan zaro ya kalli wayar sannan ya kalli Uncle Ja'afar da lumsassun idanun nasa.
Uncle Ja'afar da ya san abinda ya sashi hakan kawai sai yayi masa murmushi cuz wayar a speaker take kuma shima yana jin dukkan motsin da aka yi daga wancan 6angaren ballantana muryar Noor da ya fito tarwai.
Kunne ya sake kafewa amma bai ji muryar ta 'kara magana ba illah muryar Anty Zainab ka'dai.
Idon sa ya sake lumshewa yayi shiru yanayin fitar numfashin sa na 'kara hauhauwa yana canza salo.
Ganin hakan ya sa Uncle Ja'afar 'daukan wayar ya cire a speaker sannan ya kai kunnan sa domin ya fahimci Mu'een sam bai da niyyan cewa komai...." Ba shi da lafiya ne shiyasa bai yi miki magana ba but anjima zan 'kira ki".
Haka kawai yacecda Anty Zee wanda da gama fa'din hakan sai ya kashe wayar tasa ya sanya ta cikin aljihu.
Cigaba yayi da lalla6an Mu'een wanda har a lokacin ya'ki sake bu'de idanun sa ballantana ya bu'di bakin sa ya furta wani abu, cikin zuciyar sa yake ta ayyana" Uncle...kaima ka daina so na...ba ka tausayi na....ji nake kamar in mutu idan na tuna fushin da kake yi da ni Uncle..me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa kuka 6oye Noor daga idanu na, me yasa kuka 'ki bayyanar min da ita bayan kunsan ina matu'kar son mata ta?..."
Haka har likatan sa ya dawo Uncle Jafar ya fita magana guda bata ha'da su ba.
Shi kam abin yawa suka yi masa, muryar Noor da yaji cikin wayar yafi komai 'daga masa hankali...ga kuma Uncle 'din sa da ya kama da laifin 6oye ta navtsawon lokaci, da wanne zai ji, da murnar dawowar Uncle rayuwar sa ko kuwa da ba'kin cikin rashin Noor zai ji.
Uncle Ja'afar na fita daga ward 'din sai yaci karo da Saif sai suka koma suka zaune tare.
Shiru na 'yan sakanni kowa na jimami cikin ransa, nan ma wayar Uncle Ja'afar ce ta fara ruri ko da ya ciro ya duba sai yaga sunan Anty Zainab ne...dama yasan sai ita, yasan tunda taji batun yaron ta ai babu sau'ki.
'Daukan wayar yayi ya kai kunnan sa..." Nextweek zan dawo".
Shine abinda ta fara furtawa cike da 'dauki wanda yake fita tun daga cikin zuciyar ta.
Goshin sa ya 'dan tattare sannan ya tambaye ta dalili.
Instead ta bashi amsa a a sai tace" Dan Allah kar ka hana ni...ina so in ga jikin Yaro vna.."
" Toh ita kuma Hudahn da wa zaki barta?"
" Tare zamu zo zan mata bayani ai".
" Toh shikenan Allah ya kaimu".
Da gama fa'din hakan sai ya cire wayar a kunnan sa daidai lokacin da Saif ya jefa masa tambayar" Unlce wace Hudah kake magana akai kuma? kar dai Noor 'in Yaya?"
Kallon sa kawai Uncle Ja'afar yayi yai shiru Saif kam haushi kamar yayi kuka, dama duk wannan abin baki suka ha'dewa Mu'een, dama sun san inda matar sa take shine suka bar shi yake faman kokuwa da rayuwar sa?".
" Hmm.."
kawai ya iya furtawa a fili gami da sunkuyar da kansa, ji yake badan kawun sa bane Uncle Ja'afar da sai ya tara masa mutane anan wurin, wannan ai rashin tausayi ne a ganin sa.
Zuwan Uncle Ja'afar sosai ya bada himma wajen ganin an tsananta kulawa da lafiyar Mu'een yadda ta dace, maku'dan ku'da'de ya dire kafin ya samu aka 'dauko wani likita na musamman domin ya duba shi.
Kwanan Uncle Ja'afar biyu ya koma kafin hakan kuwa sai da ya sanar da Mu'een cewa Antyn sa ma zata zo kwanan nan ta duba shi, har lokacin tafiyar tasa kuwa basu yi wani maganar kirki ba da idanu kawai Yah Deen ke kallon sa cikin zuciyar sa yake ayyana irin rashin kyautawar da yayi masa.