Sashe 20
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mafi yawan lokuta wasu dake wucewa na binta da kallon mamaki wanda wasun ma sam bata san suna yi ba, yayin da wa'dan su masu 'karfin gwiwar har na tsaya wa da nufin jin damuwar ta amma sai ta rasa mai zata ce dasu, kusan mutane uku suka yi mata magana amma mutun biyu daga ciki bata tanka su ba wucewa kawai take yi ta barsu tsaye a wurin, me zasu yi mata take tambayar kanta, idan har mai gadin makarantar ma bai san inda Jasmine tayi ba to waue zai iya sani banda Sani, hakan data sanya cikin ranta ne ya sanya ko kula su bata yi ba kuma bata damu da halin da zata shiga ba in dai saboda yar ta ne.
Mutum na farko cewa yayi " Allah ya kyauta yayin da na biyun ya bita da kallon tausayi kawai gami da jijjiga kansa inda cikin ransa ya furta " Allah ya rufa asiri".
Mata ta uku da tayi mata magana kuwa itace ta 'danyi sa'an samin amsa daga bakin ta inda tayi mata bayanin rashin ganin Jasmine 'din a takaice.
Cike da tausaya wa kuwa matar tace Allah sarki, Allah ya bayyana ta....amma kiyi ha'kuri ki koma gida kinji, ki sanar da mahaifin ta sai ku kai report wurin 'yan sanda, in akayi sa'a za'a dace tun da kinsan aikin su ne, amma ai hakan kam wahalar da kanki kawai zakiyi"
" Idan batada mahaifi fa".
Ta tambayi matar tana kallon cikin idanun ta wanda tsintar kanta kawai tayi da fadin hakan.
Sosai fuskar matar ya nuna alamun tsananin tausayawa tace " Allah sarki....idan na fahimce ki dai-dai kenan kina nufin marainiya ce ko....Allah ya bayyana miki ita, duk da haka kiyi ha'kuri ki je ga jami'an tsaro babu mamaki a dace, ki daina wahal da kanki please".
Noor tsaban yanda take jin ranta yasa ta kasa fahimtar gaskiyan da matar ta sanar da ita ballantana ta fahimci tsananin tausayin ta da ya mamaye ilahirin fuskar matan.
Cikin ranta tace " ai dama nasani, mutane bazasu ta6a fahimtar halin da kake ciki ba, komai ya faru da kai sai dai a cema " kayi hakuri.....ban damu da dan na wahal da kaina ba matu'kar akan yarinya ta ne zan juri komai koda kuwa menene shi"
A fili kuwa share hawayen ta tayi sannan tace da matar "....nagode"
tare da juyawa taci gaba da tafiyar ta tana tunanin yaushe zataje ga 'yan sanda ta kai report har su fita su nemo mata y'ar ta, gani take duk 6ata lokacin ta zatayi.
Matar kam sosai ta tausaya mata dan kana ganin ta zaka fahimci tsananin tashin hankalin da take ciki..........a fili ta furta " Allah ya bayyana miki ita". Sannan itama ta juya ta wuce abinta.
*****
Misalin 2:28pm jirgin su Deen ya sau'ka garin Bauchi, da 'dan sauri shima ya fita daga airport ya tari abin hawa direct zuwa asbitin batare da 6ata lokaci ba ya zarce inda Dr. Safwan yayi masa baya nin suna ciki ko da yaje gado 'daya ya tarar a 'dakin kuma Baby ne ka'dai take kansa.
Jakar dake hannun sa ya sake tayi 'kasa lokacin da yayi arba da Babyn sa kwance idanun ta a rufe, hannun ta, goshin ta, kafa'dar ta da 'kafafun ta duk da farin abu dangin fari, ga dukkan alamu sitirta ciwuka akayi da su.
A hankali ya 'karasa gaban gadon ya zauna daga gefen ta ya kamo hannun ta mai 'dan lafiyan ya sanya cikin nashi hannun, yayin da 'dayan hannun nasa ke shafa kanta a hankali.
" Baby"
Ka'dai ya iya cewa wanda daga hakan kasa furta komai yayi tsabar yanda tausayin Jasmine 'din ya cika masa zuciya, kuka yake jin yi amma baya so yayi kuka gaban ta dan kar ya karya mata 'karfin gwiwar ta na sake rayuwa a doron 'kasa.
Yanda tausayin ta ya girmama a zuciyar sa har ji yake tamkar 'kirjin sa zai tsage, daga gefen ta ya kwantar da kansa a hankali cikin ransa ya furta " Allah ya baki lafiya Mamana, Allah ubangiji ya tashi kafa'dun ki".
Dr. Safwan dake tsaye daga bayan sa ne ya 'kara so tare dafa kafa'dun sa ganin yanda jikin sa duk yayi sanyi, sosai yake tausaya masa shima.
Yana dafa shi kuwa sai Deen ya 'dago jajayen idanun sa ya kalli hannun sannan ya kalli fuskar Dr. Safwan.
Ganin shine sai ya sake sau'ke kanshi ya ci gaba da kallon fuskar Baby Jas dake kwance jikin ta bako riga tayi fayau duk ta ko'de ta 'kara haske.
Saman la66a ya furta " Safwan Jasmine 'dina soon zata warke ko?"
" Insha Allahu zata warke Mu'een karka damu, addu'ah zakayi mata kaji".
Fa'din Dr. Safwan cikin tausayawa.
Shiru Deen yayi kawai ya tsura mata rinannun idanun sa masu 'dauke da zafafan hawayen da sam baya son su sau'ko masa.
A hankali ya sake fa'din
" Bakin Baby ya kumbura Safwan kuma naga ba'a saka komai ba"
Yayi maganar tare da kaiwa hannu yana shafa bakin a hankali.
Safwan sai yace
" Nayi mata allura kuma zai warware da iznin Allah, inajin buguwa tayi a bakin domin a 'kasan sit aka 'dauko ta a sume......sai dai kuma a mi'ke ta fa'da wurin ga dukkan alamu tun farkon faruwar lamarin tsoro da firgici ya sanya ta suma wanda sanadin fa'dawan nata ne ma ya sanya blocks 'din basu illata ta sosai kamar Sani ba".
Shiru Deen yayi bai ce komai game da maganar Dr. Safwan ba kawai yaci gaba da kallon gurbin ciwukan dake jikin nata har zuwa 'kafafun ta wanda dai-dai feet 'din ta yaga nan manne da bandage, jikin ta babu komai sai tarin fararen bandage da auduga.
Muryar Dr. Safwan ne ya ratsa masa kunnuwan sa inda yake fa'din " akwai wani abinda ya kamata mu tattauna da kai Mu'een, dama zuwan ka nake jira tun 'dazun da kuma farka war yarinyar 'kila zata san me ya faru, sai dai ba yanzu zamu yi maganar ba dan naga baka cikin natsuwa a halin yanzun gashi muna bu'katar jini".
Sakin hannun Jas Deen yayi da sauri ya juyo ya kalli Safwan yace " me kake nufi Safwan, me ke faruwa da Baby....don't tell me that yarinya ta mutuwa tayi".
" Haba Mu'een ka manta matsayin kane wai? dan Allah ka daina fa'din hakan, in kuma ma mutuwa Baby tayi har ni sai na gaya maka ne, ai gata nan a gabanka you can check her da kanka in baka yadda ba".
Kai Deen ya dafe da dukkan hannayen sa tare da sakin zazzafan huci daga bakin sa batare da ya furta komai ba.
Safwan ne ya cigaba da fa'din " magana zamuyi amma sai in Allah ya tashi kafa'dun yarinyar na tabbatar tukunna".
" Kallon mamaki Deen yayi masa tare da furta " what's going on ne Safwan me yasa kake son min wasa da hankali ne, da wanne kake so inji please".
Maimakon ya bashi amsar maganar shi ah ah cikin salon kauda waccen maganar yace dashi
" Muna bu'katan jini Mu'een dama zuwan ka nake jira dan bana so a sanya mata wani daban sai naka kuma naga duk baka cikin hayyacin ka....ya za'a yi?"
Tsaye Deen ya mi'ke yace " muje lab karka damu dani".
Wata sister suka bari a cikin 'dakin suka fita.
Suna zuwa ba a wani 6ata lokaci ba aka gama duk abubwan da ya kamata sannan aka 'dibi jinin Deen 'din leda 'daya.
Safwan yayi-yayi dashi ya 'dan zauna ya huta amma sam ya'ki dole suka fito tare.
Safwan da kansa ya jona mata jinin, ganin da yayi Deen bashi da niyyan zuwa ya huta ne yasa shi fa'din
" kayi magana da mahaifiyar tan ne?"
Kai Deen ya jijjga masa tare da kawar da kansa daga barin kallon Safwan 'din.
" No wonder shiyasa har yanzu banga tazo ba....amma kasan duk inda take hankalin ta a tashe yake ko? Kuma itama Jasmine idan ta farka dole zata bu'kata ganin mahaifiyar ta ka sani...so ka daure ka 'karasa gidan sai ka sanar da ita kaga kaima ka 'dan huta kayi freshing up kafin ka dawo, babu mamaki ma Baby ta farka kafin dawowar taku..........".
Deen kam sai yanzu na ma Noor ta fa'do ranshi, yanzu ne tunanin asalin ma'kasudin tahowar sa Bauchi yazo ransa, shi kansa yana so ya ganta yaji dalilin 'kin amsa wayar sa da bata yi a yau 'din ba"
Batare da 6ata lokaci ba ya tashi sannan ya sunkuya dai-dai kan Jas yayi pecking 'din ta agoshi tare da furta " speedy recovery my angel".
Kafin ya 'karaso har Dr. Safwan ya 'dago masa jakar sa da ya jefar tun farkon shigowan sa sai ya mi'ka masa.
Hannu ya mi'ka ya kar6a tare da furta " ina Sani fa".
Safwan amsashi yayi da fa'din
" an kaishi male surgical".
" Ok muje in ganshi kafin in wuce".
Koda suka je yaga halin da Sani yake ciki ba 'karamin tausaya masa yayi ba, bai bar cikin asbitin ba kuwa sai da ya bada nasa ha'din kan, domin hannun Sani ba 'kara amfanar sa zatayi ba.
Yana gamawa da wannan batun ya nufi hanyar gidan sa zuciyar sa cike fal da tausayin wa'dan nan rayuka guda biyu, wato Jasmine da Sani, wanda yake tunanin duk abinda ya same shi shine sila tunda shine ya bashi makullin mota ya kuma bashi suna DRIVER, duk dama yasan bawa bai ta6a wuce 'kaddarar sa amma yakasa raba zuciyar sa da 'daukan wannan laifin.
*****
B'angaren Noor kuwa tafiya ta cigaba da yi idanun ka kan titi wai ko zata ga motar ta gifta amma bata gani ba, bata san iya tsawon tafiyar da tayi ba sai da ta tsinci kanta daf da round about, anan ta tsaya da tafiyar batare da mamakin doguwar tafiyar da tayi ba, wanda bata tunanin iya tsawon rayuwar ta ta6a yin koda makamanciyar ta.
A daidai ta sake tara ta hau zuwa gida da tunanin Allah yasa ta same su a gida, yanzu kam in har ta koma gida taga basu dawo ba to dole ne ta 'kira Deen ta sanar dashi sai ya dawo asan abinyi tun kafin lokaci ya 'kure musu.