← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 211

Sashe 47

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin ma da yafi 'daga mata hankali shine dakatar mata da makaranta da akayi, dan Hayat cewa yayi ko an koma ba zata je ba ita, ranan ma tasha kuka ranar da ya gaya mata hakan, " duk menene dalili wai ?
Ta tambayi kanta...wani 6angare daga cikin zuciyar ta ne ya bata amsa da fa'din " kawai yana gudun kar rayuwar ki ta lalace ne Rahma.....wani sabon kukan ta sanya ta 'kudura a ranta cewar da zaran ya dawo zata je ta bashi ha'kuri ta kuma ro'ki alfarmar ya barta ta 'kare ko secondary ma, in yaso sai ta killace zuciyar ta daga soyayya musamman irin ta su Mu'inuddeen da bata da ribar komai daga 'karshe sai asara da tulin abin kunya ma.......tayi al'kawari matu'kar ya barta to bazata sake kula kowa ba hatta Mu'een 'din ma yanzu rabuea zatayi dashi tunda ya barta fiye da sati guda bai 'kara waiwayen inda take ba ko ma yaji halin da take ciki ba f
duk ya shareta...sai daga baya ma da tayi tunani sannan ta fahimci cewa ha'kurin nan da ya tura mata mai reshe ne....manufar sa ba 'daya bane.

Hayat kuwa duk wasu 'kananun iskanci da rashin kunyar sa ya zubar da su tun ranar da idon sa ya gane masa 'kanwar sa da ake shirin lalatawa da a tunanin sa sanadin sa ne, dan babu mamaki yasan Mu'een da gangan ya aikata hakan...... tun ranar da yaga hakan ya nutsar da hankalin sa wuri guda, ya nemo matakan hankali ya cusa cikin rayuwar sa, balle dama gashi mahaifin su babu lafiya yanzu abubuwa sun sha kansa sosai, komai shi ke jagoranta na daga dukiyar mahaifin nasu jinyar sa, ga kuma sha'anin gida ma.

Yanzu ne ya san cewa shi babba ne a gidan, ko waccan takaddun ma da yaje ansa wurin Rahma....takaddun wani test ne da aka yiwa mahaifin nasu sai daga baya kuma ya ga inda ta ajiye cikin 'dakin nasa ashe ranar bai nutsu ya duba da kayu bane....wanda baya raba 'dayan biyu hakan ya faru ne saboda Allah ya so nuna masa rayuwar da Rahma take ciki.

Shiyasa ya dage yayi ruwa yayi tsaki wurin ganin ya aurar da ita ga wanda ya tabbatar yake yi mata son gaskiya tun bata san kanta ba....wata 'kila auren ne ka'dai zai zama katanga tsakanin ta da Mu'een.
~Wannan kenan~

*****
Yanzu Rahma bata da burin da ya wuce taga an daina batun wannan auren nan...burin ta taji cewa an fasa aurar da ita, ko kuma taji ance mafarki ne take yi kawai ba gaskiya ba.

Sai dai cikin rashin sa'a koda ta yiwa Hayat magana bayan ya dawo gida sai ya tabbatar mata da cewa batun auren ta gaskiya ne da fa'din " bazai ta6a iya sake barin ta a hakan ba...yace haba Rahma...kar ki manta fa da idanu na naga halin da kike ciki ba gaya min akayi ba, ta ya kike tunanin zan zuba ido inga lalacewar rayuwar ki?
Mu'een ba aure zaiyi yanzu ba balle ace shi ya fito ya aure ki na tabbata ba auren ki zai yi ba burin sa kawai ya ta6ar da rayuwar ki ne....ko kin fi son in barku ku cigaba da rayuwar dabbobin yafi miki?"

Rahma 'kasa ta sake yi da kanta sosai bata iya ta bashi amsa ba.

Shima sai ya jijjiga kansa sannan ya cigaba da fa'din ....." Darajar 'ya mace shine kafuwar mutuncin ta Rahma ki ringa tunani kafin ki aikata wani abin domin wani lokaci mutun kan manta da dacewar abu sai bayan ya aikata shi wanda in yayi wasa zai 'kare kaf 'din rayuwar sa ne yana me dana sani wacce bata da amfani sam, kuma kinga
Daddy bashi da isasshen lafiya a yanzu so bazan so in 'kara masa wani ciwon akan wannan ba gaskiya shiyasa kawai na yanke wannan shawarar dan bana so watarana yayi kuka dani cewar ban kula da ke ba lokacin da babu idanun sa.....sannan kuma na 6oyewa kowa dalilin taso maganar auren gaba 'daya saboda in kare miki mutuncin ki Rahma.....ko kaka da su kawu shafi'u ma basu san ainahin dalilin ba, dan haka kije kawai ki cigaba da shiri...Amin na sonki sosai kuma na san zai kula da ke da amana".
Yana gama fa'din hakan yayi gaba abinsa....ya barta tana zubda hawaye.

Rahma ji tayi tamkar tayi ta ihu saboda takaici, ga kunya ga haushin sharetan da Mu'een yayi ga shi kuma ance ba za'a fasa auren ba kuka take jin yi sosai amma babu amfani sam...bazata iya watsawa Yayan ta 'kasa a ido ba dan ya rufa mata asiri shima, dan haka dole ta sanyawa ranta salama gami da bawa kanta ha'kuri da 'ko'karin cusawa zuciyar ta kar6an 'kaddarar auren da hannu bibbiyu...kodan ta faranta ransa ta kuma nuna masa cewa wancen abinda ya farun 'kaddara ne ba halin ta bane.

Duk 'ko'karin da matar baban su tai tayi wajen gano babban dalilin da ya tado batun auren Rahma tayi amma bata samu abinda take so ba dan kuwa Hayat bai gayawa kowa ba daga shi sai zuciyar sa ne ka'dai suka sani, sai dai a kullun yana sake ro'kon Ubangiji akan Allah yasa daga iya abinda ya gani 'din babu wani abu daban, Allah yasa bai riga ya illata rayuwar ta ba abaya... kamar yanda yace bai aikata ba 'din Allah ya sa ya kasance hakan 'din ne gaskiya....Allah ka 'kara karemu da iyalan mu daga sharrin dukkanin masu sharri....AMEEN"

Wani sa'in ya kanji haushin Mu'een sosai a zuciyar sa yayin da wani lokaci haushin kansa ke kama shi, sai dai lokuta da dama yafi bawa Rahma laifin kacokam, dan duk ta inda ka kewaya zaka samu itace da laifi...ta sake mai da yawa, ta bashi fuskar shiga gidan su kai tsaye, har ta iya fitowa gaban sa da irin wancan shigan, abu mafi muni ma shine da har ta barshi ya ta6a mata jiki, idan ya tuna hakan abin na bashi takaici sosai fiye da zaton mutun Hafsat...."

Girgiza kai Hafsat tayi cikin tausaya tace " ai babu da'di irin wannan abin Hudah, bazaka ta6a sanin ciwon sa ba sai abin ya same ka".

" gaskiya ne "
cewar Nuree sannan ta cigaba da fa'din....." shiyasa Hayatu yake jin bai ga wani dalilin da zai hana shi aurar da ita ba adai dai wannan lokacin sai dai in ikon Allah.

Tsakanin sa da Mu'een kuwa bai ma san me ze ce ba, kawai ji yake tamkar ha'duwar su da shi na gaba ba zai yi kyau ba, me yasa ze bi 'kanwar sa? ai in fansa yake son 'dauka ni ya kamata ya tunkara ba Rahma ba.... me yasa sai ita?
Ai namiji sai namiji matsoraci ne ka'dai ke maida fansar sa ta koma kan mata...a fa'dan Hayatu kenan.

*****
Kwanaki na 'kara matsowa yayin da duk kwanan duniya idan Rahma ta tuna bikin ta ya kusa sai taji haushin Deen ya lullu6e ta, da abin yayi yawa har sai ya riki'da ya koma tsana, ko sunan shi bata son tunawa, da gaske ne ashe da ake cewa akwai 'yan used nd dump cikin maza, ita dama ba a riga anyi using 'din ba ma gashi anyi dumping 'din ta, kenan da a wancan ranar ya samu dama ya shige ta ma da shikenan shi kam gaba ta kaisa....me yasa ma na biye masa ne, me yasa ban hana shi ta6a jikina ba? Banza harda ta 6a min...."
bata 'karasa ba taja tsaki " mtheew" cike da takaici gami da mi'kewa, haushi sosai take ji har cikin ranta musamman idan tana tuna touches 'din sa she can deny it abin ya kasa barin kwanyar ta....yana abu a nutse cikin sanyi ga dukkan alamu ya 'kware ta wannan fannin dan akwai shi da tsayawa a zuci....ba 'karya tasan gayen ya ha'du... "
" Allah ya isana ma wallahi" tace afili....irin su ne wa'danda ake cewa shiru-shiru munafukai ai...'dan iska mayaudarin banza mai fuska biyu".
Tana cire kaya take wannan tunanin wanda tana gamawa ta fa'da wanka.

*****
Shima 'din ta 6angaren sa abin ba sau'ki, domin damuwar sa 'kara yawaita takeyi a ko wani lokaci musamman idan ya tuna abinda ya shiga tsakanin su da Rahma, hoton surar jikin ta ya kasa barin idanun sa, tunanin sa da zuciyar sa gaba 'daya.

Sai abin ya zame masa tamkar cuta, a kowani lokaci sabon yanayi ke sake ratsa shi a duk lokacin da ya tuno da surar jikin ta, bai ta6a sanin haka yanayin sa yake ba sai da wannan lamarin ya faru.

Duk iya 'ko'karin da zai yi na ganin ya raba kansa da wannan damuwar abin ya faskara, gashi dai yayi wa kansa katanga da Rahma tunda ya karya sim card 'din sa, ya san ko ta nemeshi bazata same shi ba kuma ba komai ta sani akan sa ba bayaga suna da lambar wayar shi....shi kuwa yayi al'kawarin ba zai sake kai kansa wurin ta ba, ba zai sake shiga rayuwar ta ba dan baya so ya sake yin wasa da hankalin ta karo na biyu.

Batun yau ya san irin girman soyayyar da take yi masa ba, shiyasa ma wasu lokutan yake 'ko'karin bata kulawa koda kuwa zuciyar sa ba hakan take so ba, ko ha'kurin da ya tura mata a text ma yayi ne mai manufa biyu duk da yasan zai yi wahala ta fahimce shi amma shi yasan bai kyauta mata ba ta 6angare da dama shiyasa ya bata ha'kuri....
Ya yaudari zuciyar ta da soyayyar 'karya daga 'karshe kuma yaso lalata rayuwar ta a lokacin da yasan cewa bazata ta6a 'kin amince mishi ba...dan tana wa soyayyar ta fadanci ne a lokacin, yana da ya'kinin ko me zai yi da Rahma a wancan lokacin bazata 'ki amince masa ba.....ya kan godewa Allah ma da ya jefo masa Hayat a dai-dai lokacin kafin yayi aika-aika...wata 'kila Allah yayi hakan ne dan ya kare su daga aikata ba dai-dai ba.

Amma duk da haka moment 'din ya kasa barin tunanin sa har ma yana barazanar hana shi sukuni.
Chapter 47 · 0% Book details