← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 211

Sashe 76

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bu'dan bakin Husnah sai tace da shi " Zanzo anjima ka jira ni".
..with so much exitment yace " da gaske....Husnah bansan zolaya ni".
Yana mganar ya koma ya kishingi'da.
" Allah kuwa zanzo nima fa na damu..ba jiya na gaya maka ba..kai de ka jirani zaka ga ikon Allah".
Ta gama fa'din hakan da dan dariya tare da yanke 'kiran.

Shiri tayi ta fito tace da mahaifiyar ta zata je shopping..." Adawo lafiya"
mummyn tan tace tare da gyara zaman ta kan kujera.

Key 'din mota ta 'dauka ta fita, tana fita kuwa sai ta kamo hanya ita ka'dai ba tare da tsoro ko damuwar komai ba.

Tafiyar 'yan mintina ce ta kawo ta saboda yanda take sharara uban gudu ya sanya bata 'dauki tsawon lokaci kan hanya ba.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻 *Dadicated my In-law( Umm Amatullah) Luv u irin sosai 'din nan* 😍 *..Allah ya raya mana Zuri'a 🙏AMEEN* 🙏

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *38*

Tana isowa ta 'kira shi yayi mata kwatance amma da 'kya ta gane gidan da yake farkon zuwan ta kenan, sai da ta ha'da da tambaya kafin nan, gashi kuma ya'ki fitowa balle ya sau'ka'ka mata abin.

Mutanen kuwa idan ta tambaye su kawai sai su bita da kallon mamaki kafin a nuna mata hanyar da zata bi...dan sun san ba 'yar garin bace zuwa tayi.

Da 'kyar ta isa gidan bayan ta ha'du da Imrana wanda ya kasance shine mutun na 'karshe da ta ha'du dashi shine kuma yayi mata jagora...Yah Deen ne ya tura shi.

Ko lokacin da zata fita daga motar sai da ya sau'ke ajiyan zuciya yana mai yabawa da halittar da Allah yayi mata...dan sosai Husnah ta ha'du iyaka ga kyan jiki gashi ko'ina zam-zam masha Allah.

Tare suka shiga Imrana da ita amma ganin yanda ta tafi ta rungume Yah Deen a gaban idanun sa ya sa shi fahimtar cewa ala'kar tasu babba ce, balle da yaga irin kallon da Yah Deen ke binta dashi..ai hikenan.

Imrana murmushi ya saki sannan ya juya ya fita yana fa'din " sai ka fito malam...ni kam nayi nan".
Yah Deen ko kula sa bai yi ba har ya 'karasa barin gidan.

Imrana kuwa fita yayi cikin ransa yake fa'din " gayen nan zai kwashi gara anan gaskiya".

Husnah bata yadda azahar ta gota tana cikin garin ba, gudun kar tayi laifi agida bacin shopping tace zataje.

A hanzarce ta kintsa ta fito taja motar ta tayi gaba zuciyar ta fes dan ta faranta ran masoyin ta.

〰〰〰
        Bayan sati biyu....abubuwa duk sun cunkushe ta 6angare na, abin duniya ne yabi ya ishe ni....musamman da ya kasance su Saif na shirin komawa makaranta, gashi kuma ayau 'din zanje shara can gidan sa, a duniya babu abinda nafi tsana kamar zuwa gidan Yah Deen sam banso koka'dan, gashi hatta Saif ban bari ya san abinda ke faruwa ba gudun kar ya sanar da Ammi Yah Deen ya yanka wuya na.

Gashi sam ba kara ce da shi ba, duk yadda ka zage kayi masa aikin abu 'kalilan sai yasa ka gaba da masifa musamman ma ni, ban kuma san dalili ba..gashi ya hana ni yi mai kuka a gida yace ko da wasa hawaye na drop 'daya nayi kuskuren da ya 'diga mai a gida to sai ya 6allani.

Idan yace 6allanin nan kuwa gani nake tamkar yadda ake 6alla kara haka zai min shiyasa tsoro ya yiwa zuciya ta 'kawanya, koda wani lokaci tsoron sa nin kuwa yake 'karayi cikin zuciya ta, saukin ma da nake samu shine da yake Ma'u na raka ni, zaki yi mamakin duk wannan tsoron nasa fa da nake ji bai ta6a 'daga hannu ya dake ni ba kalaman sa ka'dai ke firgita ni.

Duk na koma wata iri da ni, walwala ta ta ragu sosai, ko a makaranta ban fahimtar komai tsabar damuwar dake cunkushe cikin raina, gaba 'daya na fige na 'kara ramewa gani daman ba jikin kirki gare ni ba, hatta Ammi sai da ta lura da ramar tawa da kuma ta tambaye ni ko wani abu ke damuna sai nace da ita bakomai hakan yasa kawai ta 'kyale ni, yayin da Ummah ta ke tunanin ko girma ne ya sanya ni ramar.

    Yau ma kamar kullum, ta kasance ranar Lahadi ne so babu makaranta, hakan kuma yasa tun tashi na da safe abin ke ta min yawo a zuci, inata 'dawainiya da tunani, fargabar ta inda zan fara  tambayar Ammi cewa zan fita nake yi, bansan 'karyar da ya kamata inyi mata da zai sa ta barni in fita ba dan bata so in cika yawo da yawa acewar ta...shiyasa ma ta fara complaint da yawan ce mata zani gaida Ummah ta da nake yi..duk kaina sai ya kulle na rasa mafita.

Har hakan yasa na makara har kusan sha 'daya ban fita ba, haka shima Yah Deen 'dib bai zo gida ba...ban san me ya ri'ke shi ba kuma.

     Ina zaune a 'daki na kasa zaune na kasa tsaye kawai sai jin muryar Ma'u nayi tana gaida Ammi daga can parlour.

Ai da sauri na tashi na fito fuska ta cike da fara'a nace " Ma'u"!
Murmushi tayi min tare da 'karasowa inda nake.

Ammi ma murmushi kawai tayi ganin yanda mukayi farin ciki da ganin juna, daga haka ta juya ta shige kitchen....mintina biyar Ma'u batayi agidan ba tace zata tafi, mayafi na zara sannan naje na sami Ammi dake kitchen nace" zan rakata Ammi".
" Har zata tafi ne?"
Nace " Erh"
Sai tace" To kar kiyi nisa fa kinji?".
nace mata"
To" Tare da juyawa na bar bakin kitchen 'din da murnar bata hana ni fita ba.

Daga nan naje na same Ma'u muka wuce da sauri..da yake nasan dama abinda ya kawo ta.

Muna zuwa gidan ma sai muka tarar da shi ya fito yana shirin kulle gidan da ganin mu sai ya fasa yace " Ina dawowa yanzu".
Ko gaida shi bamu yi ba muka shige ciki.

Mintina sha biyar mai kyau bamu cika cikin gidan ba muka fito, dama aikin wani lokaci na gulma ne kawai, babu wani dattin kirki amma a hakan idan mutun be zo yayi ba sai aga laifin sa..tamkar wanda ya aikata babban zunubi.

Kamar de yau 'din daga shara ma babu abinda muka sake yi amma a hakan je ki gani tamkar mun mopping komai..tsabar walwalin da ko'ina ke yi.

Nice na matsawa Ma'u muka fito da sauri dan bana so in da'de saboda Ammi..amma da cewar Mau wai mu dan huta tunda baya nan.

Bamu ko rufe 'kofan gidan ba mukayi gaba abin mu....sai dai muna barin jikin gidan muka ci karo da Imrana ga dukkan alamu kuwa gidan zashi, 'dan iskan sai ya saki murmushi ya tari gaban mu..." daga ina kuke, kuma zuwa ina?"
Yace damu yana karkata wuya yana kallon Ma'u.

Da yake ni na saba ganin sa wurin Yah Deen tun ba yau ba hakan yasa nace da shi" daga gidan can ".
Na bashi amsa ina kallon sa.
" To ya sunan ku?"
Ya sake tambayar mu amma idanun sa na kan fuskar Ma'u.

Da yake na matsu in wuce gida so kafin Ma'u tayi magana sai na riga ta da fa'din "...Sunana NOORUL HUDAH ita kuma Ma'u...Asma'u.."
Na 'kara fa'da daga 'karshe.

Sau 'daya kawai ya kalle ni sai ya maida idanun sa kanta yace " Asma'u...ina son ki".

Jin maganar nayi tamkar sau'kar ruwan sama gatsau wani iri hakan ya sa na kalle shi sannan na kalli Ma'u.

Sai yanzun Ma'u tayi magana bayan ha'de goshi da tayi da jin wai yana son ta a yatsine tace da shi" Hum-um ni dai bana son ka waccan na gidan nake so"!
Ido Imrana ya zaro yana duban ta yace
" Wa wai kike nufi?...Deeni?"
Sai ta 'dage kanta.

Murmushin gefen baki yayi ya cusa hannun sa cikin aljihun wandon jeans dake jikin sa gami da fa'din " wahallalliya, angaya miki shi 'din zai so irin ki ne? Da manyan yara yake tarayya ba da 'yan mata irinki ba, gara ma ki tsaya ki fuskanci rayuwar ki...ni nan nine kalar ki....".

Bai kaiga rufe bakin sa ba nace " Ma'u ni kam zan tafi kar Ammi tace na da'de".

" A a mu tafi nima gida zani".
Ma'u tayi maganar gami da kaucewa daga gaban sa.
Daga haka muka ra6i gefen sa muka yi wucewar mu.

Imrana kam juyowa yayi ya biyo mu da idanu yana smiling, saboda wani tunani da ya 'darsu cikin ransa.

Kafin mu rabu ne da mamaki nace da Ma'u " Wai ke Yah Deen kike so?"
Sai tamin shiru tana kallo cikin idanu na...Baki na ta6e sannan nace " Indai wannan ne marin sa ka'dai ma zai kashe ki Ma'u...mugu ne fa shi sosai".

" Ni dai inason shi"!
Abinda Ma'u tace ka'dai kenan kanta a 'kasa.
Baki na 'kara ta6ewa nace " Allah ya yaye miki".
Bata 'kara tanka ni ba har muka rabu.

Ni kuwa har na isa gida ina mamakin  ta a zuciya ta, wai ita tarasa wa za tace tana so sai Yah Deen " Ta6"...har sai ma naji tana bani tausayi.
Chapter 76 · 0% Book details