← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 211

Sashe 94

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana barin su shiga kuwa Husnah da gudu ta isa ta fa'da jikin mahaifin ta tana kuka, yayin da mahaifiyar ta ma ta dur'kushe nan 'kasan tiles 'din 'dakin tana kukan itama ganin sa kwance shame-shame kamar ba shi ba, duk da tayi zaton ganin sa jina-jina ne saboda tunanin ko 'yan kidnappers 'din ne suka illata shi da tayi, musamman da ta tuna yanayin da Nasiru driver ya dawo musu gida rannan, amma ga mamakin ta sai ta gansa haka babu wani alamun ciwo tattare da shi..duk da haka bata fasa yin kukan ba cikin ranta take ayyana Allah yasa ba na'kasa ta ciki aka yi masa ba..domin sau 'daya idan ka dibe shi zaka fahimci cewa yana jin jiki sosai.

Jin muryar Husnah cikin kunnuwan sa ne ya sanya shi bu'de idanu ya sau'ke su akanta yana 'dan murmushi da daga gani kasan na 'karfin hali ne..." Daddy please ka tashi gani na dawo,l..ka ganni ko Allah Daddy bazan sake tafiya in barka ba.. wake up Daddu please".

Haka kawai take ta maimatawa cikin kuka, yayin da mahaifinta ke binta da takaitaccen murmushi da shi ka'dai ya san ma'anar sa.

A hankali ya kai idanun sa kan mummyn Husnah dake 'dan nesa ka'dan da shi sai ya tsura mata idanu kamar me shirin bata sa'ko ko kuma wanda yake so ta karanci wani abu cikin 'kwayar idanun sa.

Lokacin da yake kallon nata sai idanun sa suka cicciko da 'kwalla, ganin hakan yasa take sai ta matso kusa da shi ta kama hannun sa tana yi mai sannu Alhaji.

Tari ya fara a hankali amma akai-akai wanda da kaga yanayin yanda yake tarin zaka fahimci cewa cikin azaban ciwo da ra'da'di yake yin ta.

A rikice Mummyn Husnah ta umarci Husnah da taje ta 'kira likita suzo a sake duba shi in bazai yiwu ba sai su wuce Zaria kawai dan bazata iya juran ganin Alhaji cikin wannan yanayin ba.

Da gudu Husnah ta fita yayin da mahaifin ta ya cigaba da tarin da yake yi amma a hakan ma sai da ya bi bayan ta da idanu...da 'kyar cikin tarin ya iya furta sunan..." Fa..tee..ma" bayan ganin fitar Husnah wanda tun kwanciyar sa bai iya furta komai ba sai yanzun Allah ya bashi ikon yin magana karo na farko.

Ita da bata san asalin abinda ya faru ba kawai sai tace" Na'am Alhaji ka kwantar da hankalin ka ga Husnahn ka ta dawo ai ka ganta da idanun ka ko?"

Bai bi takan maganar da tayi masa ba, burin sa kawai ya fidsa abinda ke cikin ransa, dan haka cikin dauriya yace
"...Fateema ki kula min da rayuwar Asma'u...dan Allah, kar ki bawa kowa ri'kon ta ki ri'ke min ita da kanki ki bata tarbiya mai kyau kinji?"
Mummyn Husanh take tace
" Insha Allahu Alhaji ka kwantar da hankalin ka kai ne zaka kula da rayuwar 'yar ka daina fa'din hakan".
Idanu ya lumshe sannan yace
"...Ki yafe min Fateemah...ki ce da Husnah ma ta yafe min kinji..da...da"
Sai kuma ya kasa 'karasawa saboda tsananin ciwo.

Shiru yayi na 'yan sekanni kafin ya sake furta" Fateemah!"

Wannan karan itama cikin sanyin murya ta amsa shi cuz jikin ta duk yayi sanyi sosai".

"....Duk yanda zaki yi Fateema ki 'ko'kar ta kiga kinsa an saki Nasiru kinji, Nasiru bashi da hannu akan wannan abin...ya gafarce ni nayi komai ne cikin rashin sani...gida na dake...ya fa'di sunan unguwar yace na bashi halak malak ki mallaka masa dan Allah...".

Baki bu'de take dubam sa tambaoyi ne fal cike a bakin ta amma sai dai kafin ta yi magana likita ya shigo da Husnah a bayan sa, nan ya nemi su basu wuri zai yi aikin sa, hakan yasa duk sukayi waje badan ransu na son hakan ba.

Wannan shine 'karshen ganawar mahaifin Husnah da iyalan sa, awa guda bai 'kara a duniya ba bayan fitar sun Allah ya kar6i ransa...batare da ya sanar da kowa abinda wansa ya aikata masa ba...haka ya tafi ya bar Mummyn Husnah da tarin tambayoyin da shi ka'dai ya kamata ya amsa mata su, amma ina ba dama..domin wanda ya fi ta son shi ya 'dauke abin sa.

Husnah tasha kuka da jin rasuwar mahaifin ta hakama mahaifiyar ta, da sauran yan uwa...duk wadanda ya kamata ace an sanar da su duk labari ya riske su, Hisham dake Abuja ma shirin tahowa yake hakama step mothern shi da ta kaiwa iyayen ta ziyara cam garin Kano itama shirin tahowa take hakama sauran dangin su..kowa mutuwar ta ta6a shi sosai...farko 6acewar Husnah sai gashi daga bayyanar ta kuma mahaifin ta yace ga garin ku nan, mutum mai nagarta da halin girma, sanin ya kamatan sa ya shahara ga shi da kyautatawa musamman ga wa'danda suke kasa da shi.shiyasa kowa yaji labarin mutuwar sa sai yaji babu da'di..da yawan mutane tausayin Mummyn Husnah suke yi...

Shikam Alhaji Mamman kusan wannan shine abin da yafi komai yi masa da'di a rayuwar duniyar nan (kamar shi 'din gadi zai tsaya yi) musamman ma da ya fahimci cewa babu wanda yasan asalin abinda ke faruwa da sanadin jinyar Alhaji Hamza da har ta kai shi da barin duniya.

Cire jakar ku'din dake bayan motar Alhaji 'karamin yayi ya 6oye sannan ya shiga aka kammala komai na hidimar rasuwar dashi.

Bayan komai ya lafa ne ya 'dauki motar su ya dan'ka musu, bai damu ba cuz ya san ku'din da ya mallaka zasu iya sayan ashirin 'din motar idan yana so.

Babu wani dogon bayanin da yayi musu kamar yadda babu tunanin da mahaifiyar Husnah tayi kan kasancewar motar a gidan sa balle aje ga batun maku'dan ku'din da marigayin ya fita da su, cuz duk zaton ta already ya riga ya kai ku'din ne sannan aka sako Husnah.

Bayan kwana arba'in akayi rabon gado aka cire hakkin kowa aka bashi ciki harda na Nasiru driver da Mummyn Husnah ta fa'di wasiyar Alhajin kafin rasuwar sa.

Nasiru ya sha kuka sannan yai ta zuba godiya kamar zai ari baki..hankalin sa ya da, kwanta yanzu da yake yaji ance masa Alhaji yace a sake ahi saboda ya fahimci ba shi da hannu kan lamarin.

Hatta Mummyn Husnah da ta kawo bayanin sai da aka kusan tuhumar ta akan ta fa'di su wanene to tunda bashi bane..tunani su ko Alhajin ya sanar da ita.

Da 'kyar suka yadda cewa bata san komai ba amma sai da ta cike wani form...daga nan ta cigaba da takabar ta har ta 'kare gaba 'daya..Husnah ma ta cigaba da zuwa makarantar ta..nan ne Alhaji Mamman ya nemi ri'kon Husnah ya dawo Hannun sa amma mahaifiyar ta 'ki amincewa musamman ma saboda wasiyyar da mahaifin ta ya bar mata.

Tace zata zauna da Husnah koda wani auren zatayi babu abinda zai raba su da ita...balle ma bata tunanin zata sake yin aure har 'karshen rayuwar ta.

Da jin hakan sai ya nuna ra'ayin sa na son auren ta...Mummyn Husnah ta nuna 'kin amincewar ta amma sai ya kai zancen gin iyayen ta, mahaifanta sune suka bata 'kwarin gwiwa akan auren sa wai ko ma dan saboda kar Husnah tayi maraicin uba a gaba, hakan ne yasa ta amince da batun auren sa duk kuwa da cewa har cikin ranta ba so take yi ba amma kawai dan farin cikin Husnah...ya aure ta ne a matsayin mace ta uku sai dai basu bar gidan da suke ba suka cigaba da zama agidan da 'yar ta Husnah.

Yayin da kansa kullum yake kara bawa Husnah 'kwarin gwiwa akan ta daina damun kanta babu wanda ya isa ya sake yi mata irin na baya, da iznin Allah babu wanda zai sake cutar da ita, ya kanyi mata karyar ai ya zuba securities masu kula da ita dan haka ta daina damun kanta da tsoron zuwa makaranta.

Da haka Husnah ta saki ranta ta cigaba da zuwa makarantar ta.

Yayin da cikin lokaci 'kan'kani Alhaji Mamman ya zama wani hamsha'ki mai ji da 'ya'yan banki fiye da baya, sosai yake taka naira son ransa, babu wanda yasan inda ya samu ku'da'de sai dai kawai aka ganshi cikin sabon yanayi, hakan ne yasa da yawan mutane ke zargin cewa dukiyar 'kanin sa yake facaka da shi...musamman da aka san cewa matar kanin ma ta zama tashi..... ( Wannan shine ta'kaitaccen tarihin rayuwar Husnah)

*****
......Jin labarin halayyar asalin mahaifin Husnah shi yafi komai yiwa Alhaji Baba da'di, yanzu bashi da damuwar komai illa jiran isowar Uncle Ja'afar, dan yasan ko babu komai ai yasan tushan yarinyar nada kyakkyawan tarihi so bazai yi Allah wadai da kasancewar ta cikin ahalin sa ba, duk dama ya fahimci kan ita yarinyar ke rawa amma ai aure yasha gaban komai, da aje a tafka abin kunya ai gara ace da aure tsakanin su.

Take a wurin batare da 6ata lokaci ba ya ciro wayar sa ya yiwa Yah Deen transfer 50k da yake dama bai bashi komai ba lokacin da zai koma school...sai yau yayi ra'ayin da kansa da ya kasance yana cikin kwanaki na hu'du kenan da komawa makarantar.

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*_Marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS_*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *46*

*Bayan wasu kwana ki da komawar su makarantar*
       Komai ya gama dai-dai ta tsakanin su, rayuwar su suka cigaba da shimfi'dawa son ransu duk sun manta da damuwoyin da suke ciki kowa ya saki ransa..musamman ma Deen da dama shi abin yafi tsaya masa a rai.

*****
    Ranar ya kama ranar Monday ne kuma lecture 'daya yake da shi na safe...yayin da Husnah sai 12 take da lecture, hakan yasa ta tattaro kayayyakin ta masu bu'katar wanki kafin cikar lokacin danta 'dauraye su, tana kan haka Mu'een yayi mata sallama ya fita makaranta cikin shirin sa mai 'daukar hankali kamar yadda ya saba.
Chapter 94 · 0% Book details