Sashe 149
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan na zauna kuwa banda tunanin 'yan matan sa dake yawan min zirga-zirga cikin brain 'dina babu komai, duk wani abu idan kinga ya tsaya min arai to idan kika bincika ya shafi Yah Deen komenene kuwa abin, tun ban dangana batun da su ba har dai nazo salon tunani na ya fara canzawa akai, sai nake ganin ai da dagaske yana so na 'din kamar yadda ya fa'di da ba zai 'kara neman wasu matan ba bayan ni.
Wannan dalilin ne abu na 'karshe da yasa ni na kasa amincewa da cewa erh dagaske Yah Deen na 'kauna ta kamar yadda ya fa'di da bakin sa, a kullum sai na kasance cikin tunani da kokwanton maganar sa..abin kullum shine cikin raina ina jjujjuya shi, lokuta da dama ko da Yah Deen yazo min da sakin fuska ko da wata 'yar zolaya response 'din da yake lura da shi ta 6angare na shike sakan mai gwiwa da ni, dan ko abin dariya ne ban fiya taya shi yi ba, in hira ce kuwa sai dai in ta kallon sa duk da shima 'din ba wai gwani bane wajen hirar amma sosai yake 'ko'karin yaga ya faranta min yayin da ni a kullum nake nuna masa halin ko in kula batare da damuwar komai ba.
Tun yana 'ko'kari yana danne rashin jin da'din sa game da yanda nake nuna masan har dai ya zo ya watsar da komai, muka koma irin zaman mu na baya, abu 'daya kawai ne bai bari ba shine kula dani da kuma cikin da nake 'dauke da shi.
Gashi ta ko wani 6angare banda abokin shawara 'daya, in familyn Safwan ne ai suma Yusrah ta su ce, nasan da wuya ne su za6e ni su 'kyale ta akan koma menene, tunda ga ma misali 'daya yanzu kusan 5weeks bamu koyi waya da Fiddausi ba, ni agani na duk akan maganar Yusrah ne, duk da kuwa Mimah ta fito fili ta nuna 6acin ranta amma ai nasan naka nake ne.
Ban sani ba ashe yanzu Fiddausi kunya ta wai take ji ne shiyasa haka ma Mimah su aganin su wai zanga kamar su munafukai ne shiyasa suka 'dan rage shiga jiki na, Mummyn su kuwa dama bata da labarin komai.
*****
Ciki na 6months muka je Shuwarin ni da shi bayan tsawon lokacin da na 'dauka ban je ba, domin kuwa wannan shine zuwa na karo na biyu kenan tun bayan komawar mu Bauchi da zama, Ammi na murna sosai tayi da ganina, bakin ta sai ya kasa rufuwa, yayin da ni kuma tsananin kunyar su ya rufe min zuciya ta, sai dai nayi ta sunkuyar da kaina ina murmushi kawai.
Kunyar su nake ji tamkar bada su na taso ba, Yah Deen ma murmushi yayi ganin yanda nake yi 'din sai dai bai ce da ni komai ba.
Ammi tamkar zata goyani data ga ciki ajiki na, cikin gidan babu wanda ya 6oye farin cikin sa game da cikin balle ma da yake su Saif na gida sai nake jin wani iri.
Har ma sai naji dama ban biyo shi munzo ba.
Gashi har 1week yace zamu yi kafin mu koma, ni yanzu kowa ma sai inji kunyar sa Yah Deen ka'dai ne ban jin nawin sa a wannan lokacin.
Su Zaid angama makaranta duk sun 'kara girma shekara 'dayan da ban gansu ba sai naga sun canza min sosai.
Ganin cewa yanzu da da da banbanci yasa kowa yanzu 'dakin sa daban ne, 'dakin su na da shi Zaidu ya cigaba da zama a ciki yayin da sabon 'dakin Saif yake facing da na Yah Deen inda muka sau'ka kenan.
Washe gari da yamma ya kaini gidan Ummah ta, sai naji can 'din na 'dan fi sakewa da yake daga ita sai Ummie ne agidan na ukun sai ni da nazo.
Bana aikin komai kuwa dan ko Ammi bata bari na in tayata aiki haka ma Ummah ta, ni kam har dariya suke bani ince hala manatawa suka yi cewar aure nake da shi yanzu, ko da banyi musu aiki anan ba dan cikin ai idan ina Bauchi ni ke yin duka aiyuka na.
Abin mamaki inje gidan su Addah Saudah ma dana tambaye shi Yah Deen hanani yayi wai yanzu banda lafiya in bari sai wani lokacin ko kuma in 'kira in sanar da su nazo sai suzo mu gaisa.
Haushi ma sosai ya bani a lokacin 'kin kulasa nayi, dan banga hujja ko manufar yin hakan ba, har ya kashe wayar bance da shi komai ba.
Ace inzo har cikin garin amma zuwa gidajen su ne za'a ce bazani ba?"
Sai daga baya bayan kusan awa guda na sake 'kiran sa kamar zan yi kuka nace da shi" Ai zan iya tafiya ni babu abinda yake damuna, amma ai in banje ba bazasu ji da'di ba".
Sai yace" To ki bari zanzo in kaiki".
Da sauri nace" Ni kam a a".
Jikin sa sanyi yayi cikin natsuwa yace
" Saboda me?"
Nace" Haka kawai".
dan nasan in shine ya kaini atsatstsaye zai ce mu dawo kamar yadda yake min idan kuma je gidan Safwan ko gidan Mummyn sa, kuma gashi yau 'din har gidan Yah Usman da Binta 'kawata nake son naje.
Jin amsar da na bashi ne ya sashi fa'din" To shikenam.Allah ya tsare".
Na amsa da" Ameen"
Ni da Ummie muka tafi, in kinga yanda nake tafiyar ma da 'kyar dan ba laifi cikin na min nawi ka'dan ga kuma 'kafafuna da suke min ciwo amma a hakan na dage dole sai na fita.
Kowa idan ya ganni sai yayi farin ciki da zuwa na, kowa na murna da yanayin da suka ganni, yayye na ka'dai ne amma ke jajanta min halayyar miji na sai inyi dariya in 'kara da yi musu 'karyar ai yanzu da sau'ki komai ya wuce, kuma muna cigaba da addu'ah har kullum.
Kwana na biyu agidan Ummah ta Yah Deen yazo muka koma gida, ban tashi sanin manufar dawo da ni ayau 'din da yayi ba sai da naga yana neman ra6ar jiki na, nan kuwa nace bansan zancen ba, duk da nasan tun kafin zuwan mu Shuwarin ya 'daga min 'kafa kusan kwanaki goma kenan yanzu amma still na kauda kaina na'ki amince masa nace ni kunya nake ji agidan Ammi, ganin cewa gidan Ammi muke sai na fake da hakan, kuma har ga Allah ni banaso irin haka ya shiga tsakani na da shi a irin wajen nan bana iya sakin jiki na.
Duk yadda yaso ya fahimtar da ni halin da yake ciki kuwa 'kin sauraran sa nayi na kawar da kaina, Yah Deen baya ta6a matsamin kan bu'katar sa matu'kar na nuna 'kin amincewa ta, dan haka sai ya 'kyale ni yayi kwanciyar sa.
Da kaina nasan zunubi babba nake 'dibarwa kaina matu'kar na'ki yadda da bu'katar san hakan yasa da gari ya waye idan nayi sallah na gaishe shi sai kiga na marairaice fuska nace da shi" Ka yafe min ko?"
Da yake ya saba ba sai ya tambayi dalilin yafiyar ba zaki ga yayi murmushi shi kenan abin ya wuce nima sai in saki raina, ko da wasa bai ta6a fitowa fili ya nuna min 6acin ransa kan haka ba, kuma ko a gidan mu can Bauchi haka nake yi masa a duk ranar da nasan ya kwana da 6acin raina da yayi murmushin nan kuwa nasan me yake nufi.
Washe gari da misalin 'karfe goma na safe yace wai in shirya in raka shi wancan gidan zamu dubo wasu kaya, duk da a tsare da fuskar sa ta asali ya min maganar amma hakan bai sa naji ko 'dar cikin zuciya ta ba, shiru nayi ina tunani sai da ya sake maimaitawa sannan na bashi amsa da fa'din" Ni dai bazani ba sai Saif ko Zaidu wani raka ka".
Da mamaki ya kalle ni yana 'kan'kance idanu, taurin kanki 'karuwa yake yi kullum Nuree, yanzun duk kina yin hakan ne dan ki guje min ko me?"
Girgiza kaina nayi idanu na na tara ruwa.
Sai yace" To menene?"
Nace
" Ni kawai banson zuwa gidan ne, ko sunan unguwar banaso inji raina 6aci yake yi idan naje kuwa mutuwa zanyi...".
Shiru yayi yana kallo na cike da mamaki, sannan yace min wai saboda me?"
Nace "Kai ne ai...".
Sai na kasa 'karasawa kuka ya 'kwace min.
Idanu ya lumshe ya dafe kansa cike da damuwa, shi kansa baya so in yawaita tunawa amma ya zaiyi da bu'katar sa, da kansa yasan bai kyauta ba amma zuwa yanzu ai kamata yayi ace na manta na kuma yafe masa...tunda ko giya cecruwan shansa a yanzu bazai ta6a iya sake kawo wata macen cikin gidan auren sa ba indai ba aure ya 'kara ba.
A hankali ya tako ya iso inda nake, kaina ya ya kwantar kan 'kirjin sa batare da ya furta komai ba idanun sa a lumshe, sosai yake danasanin wancan scene 'din, shi kansa bai san me kaishi har yayi haukan 'kiran Husnah gidan ba bayan ya tabbatar ba shi ka'dai ke rayuwa cikin gidan ba.
Ada kam yayi hul'da da Husnah sunyivrayuwa mafi muni kuma yasan duk laifin sa ne shi ka'dai amma yanzu bazai raba 'daya 'dayan biyu ba cewa ko da ya kuma neman wata to laifin har da na Noor aciki, ko neman Yusrah da yayi yasan harda nata laifin ma domin ba kullum take yadda da bu'katun sa ba.
Shi kuwa har kullum al'kawarin da yayiwa Ammi akan Noor shi yake son cikawa, shiyasa tun zaman su da ita baya ta6a matsa mata akan komai, koda kuwa abin zai iya cutar da shi ne yakan mata yanda take so.
Amma yana ganin wannan tafiyar tana cutar da shi ka'dan-ka'dan dole saj yayi wani yun'kuri bawai dan ya sa6a al'kawarin Ammi ba, a a sai dan kawai ya gyara rayuwar gidan sa.