Sashe 14
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" K'yale ni da wannan matar mana ai ba tun na lura da ita ba sam bata 'kaunar kasancewa ta a gidan shiyasa ta lalu6o wani tsohon hujja dan ta 'daure ni dashi, Allah ma yasa mijin nata ba irin ta bane in ba haka ba ai da tuni nayi gaba".
Baki mai gadi ya ta6e tare da fa'din " ikon Allah!, to laifin me kayi mata har haka?"
Sani zaman sa ya gyara sannan yace " wai fa tun lokacin kafin na tafi jinyar Baba kasan ni ke kai wannan yarinyar makaranta shine wai tace ina 6ata lokaci bana kawo ta gida da wuri......,menene...menene, kasan mata da shegen gulma da munafurci ai"
Ta ma fa ta6a yi min magana kuma na daina amma hakan bai ishe ta ba sai da ta ha'da ni da shi dan ya koreni".
Kallon sa kawai mai gadi ke yi yanda yake maganar a yatsine, shine ka'dai a gidan yasan cewa fuska biyu ce da Sani, baya ga haka babu kowa da ya sani.
Kai ya jijjiga tare da fa'din " kaima ai Sani da laifin ka, me yasa baka kawo musu yarinya gida da wuri tunda kasan ba amincewa zasu yi da wani abu sa6anin hakan ba?".
Goshi Sani ya ha'de sannan yace " ai nace zan daina ko?, kuma ma idan ta kwantar da hankalin ta zama na na 'dan lokaci ne yanzu tare da su, ku'din mota kawai nake so in ha'da in ware Lagos".
Da zararren ido mai gadi yake kallon sa da mamaki musamman da yaga yanda yake nuna halin ko in kula da maganar.
" ka dai bi a hankali Sani".
Mai gadi yace masa.
Sani kuwa sai cewa yayi " in an'ki fa?"
" Ba fa'da bane ai Sani, sai in bika da fatan alkhairi".
Cewar mai gadi.
Sani ma sai yace " da yafi maka".
Mai gadi bai yi mamaki ba koka'dan dan dama sun saba irin hakan da shi, shima sai
bai sake magana ba kawai ya kauda kai gefe a fili ya furta " Allah shi kyauta".
*Members 'din group 'dina wad'anda da kuka ga ban amsa* *muku comments 'din ku na previous page ba kuyi ha'kuri please........chat* *d'ina ne ya goge gaba d'aya* .
Comment
Vote
Share
*Salmerh ce*😍
[11/19/2019, 12:31 PM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *8*
*****
Ko bayan da akayi maganar ma sai da Noor ta 'kara kusan kwana hu'du a kai batare da ta bawa Sani daman yin aikin sa ba.
Idan aka ha'da da shigowar kwanakin weekend kuwa zai bada kusan sati guda da yin maganar.
Ranar wata monday ne Sani ya fara fita da Jasmine, cikin sa'a kuwa babu complaint 'din komai da ya biyo baya har suka yi kusan sati uku.
Wanda sai a lokacin hankalin Noor ya 'dan fara kwanciya ba laifi, dan ko Hauwa ma da yake matsawa ada duk yanzu baya takura ta.
Wani lokaci Deen da kansa yake 'kara bata kyakkyawan tabbaci akan Sani, inda yake cewa ai ko da 'din ma bata fahimce shi bane shiyasa amma yanzu ba gashi komai ya dai-dai ta ba.
" Hmm"
Kawai take ce dashi batare da wata doguwar amsa ba akan hakan, ita fa kawai ta barshi yaci gaba da aikin sa ne, amma yanda take jin tsanar sa Allah ne ka'dai ya san iyakar hakan cikin zuciyar ta, rashin kyakkyawar hujja da kuma hanin da addini yayi akan tsanar 'dan uwa musulmi ne ya sanyata zuba musu idanu kawai.
Itama 'din tana zuwa nata makarantar cikin natsuwa ta dawo, bata da damuwar komai yanzu sai na abinda ke zane cikin ranta wanda ya kasance sirrin ta ne.
Haka ma soyayyar su da Deen sai abinda yayi gaba, bata ta6a jin tsanar sa ko wani abu daban ba cikin zuciyar ta illah soyayyar shi duk kuwa abinda zai mata ko kuma ya faru tsakanin su soyayyar su da 'kaunar su sosai tayi 'karfi a zu'katan su gaba 'daya.
Wani irin so take yi masa mai zafin gaske da ita kanta bazata iya misalta shi ba balle tasan iyakar sa.
Shima 'din ba laifi dan yanzu duk wani abu da yasan zai kawo sa6ani a tsakanin su duk ya kawar dasu, ciki kuwa harda batun Jiddah, tun lokacin da ta ta6a 'kiran Noor take tambayar ta wai akan wani dalili Mu'een zai ce ba zai sake aure ba, wani irin ri'ko tayi masa da har zai ce da ita matar sa ta ishe sa rayuwa har mutuwar sa.
Noor sai tace da ita " nima ban sani ba 'yan mata, amma zaki iya tambayar sa tunda naga ai saurayin ki ne shi may be ki samu amsar tambayar ki"
Tana gama fa'din hakan ta yanke 'kiran tare da kashe wayar ma gaba daya.
Bata ta6a ko gwada sanar da Deen cewa sunyi haka da wata ba balle yasan da faruwar lamarin.
Sai kuma shi da kansa yazo mata da batun cikin yanayi na ban ha'kuri tare da sanar da ita cewa shi bai san da faruwar hakan ba, Pics 'din Jasmine ya gani cikin wayar Jiddah sai ya tambayi inda ta samu dan ko shi bai da wancen photon a wayar sa balle yace daga cikin wayar sa ta samu.
Koda ya tambayi Jiddah in da samu shine sai tace dashi " a DP 'din matar ka na 'dauka dan Babyn tamin kyau naga tana kama da kai sosai yarinyar".
Ha'de rai Deen yayi yace da ita " a ina kika samu digit 'din ta Jiddah... bana son fitina fa".
Itan ma 6ata rai tayi tace da shi " ni nace maka fitina ne ya sani na 'dauka ko kuma ita tace maka dana 'kirata na yi mata fitina?"
" Yah salam!....
Ya fa'di tare da dafe goshi, cikin 6acin rai yace" haba Jiddah.... kar dai kice min har 'kiran Nuree kinyi?"
Cikin nuna halin ko in kula tace
" in ma menene dai ni kam na 'kira ta, kuma ai ba fa'da muka yi da ita ba, tambayar ta kawai fa nayi naga ne da ita ka'dai kake da burin 'karashe rayuwar ka shine na 'kira inji dalili daga gare ta".
" sai aka gaya miki kuma itace ta tilastani ko?"
Cike da haushi ya fa'di hakan.
" Ah to ni na sani ne? kasan matan yanzu basa zama sai uban shige-shige dan ganin sun mallake miji su ka'dai, itan ma waya sani ko tana zagawa dan bana tsammanin haka kawai ta bar ka".
Kafin ta rufe baki taji sau'kan lafiyayyan mari akan kuncin ta da ya kusan gigitata mata lissafi.
Tsaye ta mi'ke dafe da fuskar ta idanun ta har sun tara ruwa cikin muryar kuka tace " akan waccan bushash-shiyar ka mare ni Mu'een?"
Wani marin ya kuma sau'ke mata a 'dayan gefen fuskar tata shima 'din tuni jijiyoyin kansa sun mi'ke.
Jiddah sai ta kurma ihu tayi zaman dirshan 'kasan tiles tana kuka.
Deen kam tuni idanun sa sun riki'da zuwa ja, a masifance ya nuna ta da yatsa tare da furta" how dare u zaki rin'ka furta wannan irin mugun abin kan iyalina?, kin san ta kuwa? kinsan matsayin ta cikin raina?.....Wallahi Jiddah kika kuskura kika sake gigin 'kiran layin ta dan 'daga mata hankali ko fa'dar wani abu makaman cin 6atanci akan ta....ina tabbatar miki da cewa a lokacin zaki gane the other side of me.....idiots kawai.....get out of my house....".
Ya 'karashe da tsawa tare da nuna mata hanyar waje.
Da gudu Jiddah ta tashi ta fita cuz sosai ya bata tsoro ayau 'din, bata ta6a zaton haka halin sa yake ba, ashe masifaffe ne na gaske.
Tun daga ranan bai 'kara sauraren Jiddah ba, ita kuwa haushin abinda yayi mata kan matar sa ya sanya ta takaici sosai, barin ma da taga yanda ya nuna alamun bai ma san da batun 'kiran ba, kenan matar tasa bata sanar da shi ba ne ko me yake nufi?.
Ita Jiddah ba haka ta so ba, taso ne a yanda tasan mata da kishin mazajen su to dole idan ta 'kira abin zai dame ta har ma hakan ya sanya matar tasa yi masa bori sai su zama cikin rashin natsuwa kullum wala alla ko ta sanadin hakan ta samu shiga gidan sa, amma sai matar Mu'een ta nuna mata cewar ita bata isa ta shiga tsakanin su ba, sai ta ri'ke maganar ita ka'dai a zuciyar ta.
Sam Jiddah ta rasa me hakan ke nufi, tunani ta zurfafa sai ta tsaya akan kawai Mu'een ke haukan son ta, 'kila ita bata son shi shiyasa ma bata kishin sa, dan kuwa da tana kishin sa da bazata yi shiru kan wancan maganar ba.
'Kwafa tayi tana tunani tare da cije bakin ta haushin dukkan su take ji.
Murmushi tayi lokacin da wani tunanin yazo ranta, cikin gaggawa ta lalu6o wayar ta tare da shiga gallery, ganin abinda take so 'din na nan ya sanyata har da buga tsallen murna take fara'ar fuskar ta ta dawo.
A fili ta furta" yarinya kenan, ai in kinsan wata baki san wata ba, zan gani idan dagaske bakya kishin nasa, sai dai ba yanzu zan yi ba nasan a dai-dai wannan lokacin banda 'ko'karin faranta mata babu abinda zai sa agaba tunda shike son ta kuma yana ganin shi mai laifi ne agareta, dole kusancin su zai 'karu fiye da baya...."
"Yes" ta sake fa'di cikin tsananin murna kuma a fili tamkar zautacciya, sai tacigaba da fa'din hakan zanyi nasan a lokacin dole zata ji zafin koma me zan aikata".
Wannan dalilin na Jiddah ne ya sanya ta itama ta ja jiki sosai daga gareshi, ta sake bashi daman 'kara kusanci da matar sa sosai, shima 'din bai sake waiwayar inda take ba.........
Wannan kenan.
( Toh fa Jiddoriya na shirin yin wani 'kulli fa, Team Jiddah pls a taushi zuciyar ta)