← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 211

Sashe 50

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina daga cikin daki na ta6e baki na gefe da jin lalla6an da Ummah ke yiwa Nanneh da ko ni da nake auta ma bana samun hakan.
" to Ummah "
Nanne ta fa'di gami da ficewa daga gidan, Ummah ma bata 'kara bi ta kaina ba ta cigaba da abinda take yi.
Yayin da nayi kwanciya ta cikin 'daki har bacci yayi awon gaba dani, haka kawai yau na tsinci kaina da rashin son zuwa islamiyar duk kuwa da cewa ba 'karamin son makaranta ce da ni ba amma yau sai naji bana son zuwa.
         A kullum ina riga ta shirin zuwa islmiyar, na safe ne ka'dai take rigani shiryawa kasancewar ita bata yin aikin komai da safen illah tayi sallah taci abinci sai saka uniform.....shiyasa lokuta da dama ma tafiyar bata dai-dai ta kusan kullum sai ta riga ni tafiya makarantar.

〰〰〰
          Tafe take a hankali kamar yanda ta saba, tana rungume da takaddun ta a 'kirjin ta.....dai-dai kan layin gidan Alhaji Baba take a lokacin  sai dai bata riga ta iso kusa da gidan ba.

Yana tsaye a 'kofar gidan yana amsa waya, yayin da ya kwantar da hannun sa jikin 'karafunan bubler 'din dake daga wajen gidan nasu.

     Tun daga nesa  yake hango ta, kunnuwan sa na kan sauraran wayar amma idanun sa da hankalin sa gaba 'daya yana kanta,  yanayin yanda take tafiya kawai ne ya birge shi, yana matu'kar son mutum mai natsuwa a rayuwar sa musamman ma mace, bai fiya son mace mai hayaniya sosai ba.

     Koda ya gama wayar kuwa tattaro dukkan natsuwae sa yayi ya mayar kanta tashin farko kawai yaji yarinyar ta birge shi jiki da zuciyar sa, bai ta6a jin irin hakan farat 'daya game da mace ba sau 'din, yarinyace 'karama mai cike da natsuwa da haiba.... da kansa ya 'kiyasta shekarun ta a ransa, gani yayi kamar bazata wuce 14-15 yrs ba.
   Cigaba yayi da kallon ta yana sake yabawa da kyau da tsarin ta  har 'kaguwa yayi ta iso kusa da shi dan ya ganta da kyau da idanun sa.

  Baifi taku ashirin ya rage tazo ta gifta shi ba kawai wata dake can bayan ta itama sanye da kaya irin nata ta 'kwalla 'kiran sunan ta, ga dukkan alamu makaranta 'daya zasu je.

Juyawa tayi batare da ta amsa ba dan ganin mai 'kiran nata.
   'Bangaren sa kuwa hakan da tayin sai ya sake birge shi har zuciyar sa, sunan da yaji an 'kirata da shi ya cigaba da maimaitawa cikin ransa yana sake binta da idanu..ya maimaita _Nanne_ ya kai sau uku, bai san ma'anar sunan ba amma a hakan yaji sunan ya mai da'di.

" d'an jirani mu tafi dan Allah".
   Wacce ta 'kira tan ta sake fa'di tare da 'kara saurin tafiyar da takeyi dan tayi saurin cimmata.

Bata ce komai ba har 'dayar ta 'karaso kusa da ita suka fara tafiyar tare a hankali tamkar basu don yin tafiyar....'mita Nanne ta fara yi mata k'asa-'kasa da fa'din " Ke dan Allah kullum sai ki rin'ka 'kiran sunan mutun da ihu Allah..nifa bana so".
   " yi ha'kuri to na daina yanzun ma ai naga kin min nisa ne shiyasa...ina Hudah kuma yau 'din na ganki ke ka'dai?".

  Duk baiji wannan hirar da sukayi ba illah amsar da ta bayar na cewa " Hudah ta'ki zuwa cewa tayi wai bazata je ba yau 'din".
Wannan 'din ma yaji ne kasancewar daf dashi suke a lokacin.

Bayan su yabi da kallo yayin da sassanyar muryar ta ya ratsa mai dodon kunne har cikin zuciyar sa bai bari ba, idanu ya lumshe a hankali yana jin wani nisha'di na ratsashi, haka kawai sai ya tsinci kansa da binsu da idanu har suka 6acewa ganin sa.

                Wannan shine ya kasance rana ta farko da Deen ya ta6a tsintan zuciyar sa cikin shaukin so da 'kauna na gaskiya....wanda babu algus acikin sa...bai ta6a sanin da'din da ake ji idan an kamu da soyayya ba sai a wannan lokacin.

         Yana daina hangosu sai ya sau'ke ajiyar numfashi yana murmushi ya juya ya wuce cikin gida, inda bai jima a gidan ba ya fito bayan ya 'dauro alwalar sallar la'asar, masallacin da yafi kusa da gidan nasu ya nufa dan bin jam'i.

Ana idar da sallah bai zauna ba sai ya koma gida, 'dakin sa ya wuce ya mi'ke kan kujera...tun lokacin da idanun sa yayi arba da yarinyar murmushi bai bar kan fuskar sa har yanzun, kallon 'daya zakayi masa ka fahimci cewa yana tare da nisha'di marar misaltuwa.

      Sam Mu'een bai hana zuciyar sa tunanin yarinyar ba dan ko yace zai yi hakan ma ba iyawa zai yi ba, bai gushe ba yana tunanin ta har sai da ya tabbatar da cewa da gaske son yarinyar ne ya kamashi so kuma matsananci, he can feel his heart beat yanda ya canza gaba 'daya....bai kuma 'kalubalanci hakan ba, domin 'dari bisa 'dari zuciyar sa tayi na'am da ita, tashin farko zuciyar sa ya bata tambarin masoyiya agare shi kuma sanyin ransa,  damuwar sa kawai a yanzun shine ya san bayaga Nanne menene asalin sunan ta.

      Ko lokacin da aka tashi daga islamiyar ma dawowa yayi ya tsaya da ya saiti 'karfe biyar tayi yasan duk tsiya bazasu wuce hakan ba.

  Yana tsaye a wurin 'yan biyun Ammi suka dawo suka shige gida...ba'a 'dau lokaci ba sai ga su nan itama da 'kawayen ta sun taho, sauran nata hira amma ban da ita, dan sam ita ba gwanar hakan bace tun asali, ko ta kansa ma babu wanda yabi balle su san da tsayuwar sa a wurin abinka da 'yan yara dake ji da yarinta....Duk da 'kura mata idanun da yayi amma sam baiga alamar ta san da tsayuwar sa a wurin ba.... amma ga mamakin sa suna gifta shi sai yaga ta waigo ta kalle shi suna ha'da ido sai tayi 'kasa da kanta gami da juya ta cigaba da tafiyar ta.

       Tsabar yanda Deen yaji da'din hakan har dafe 'kirjin sa yayi...yana sau'ke sassanyar murmushi.....saman la66an sa ya furta " wannan tawa ce ni ka'dai insha Allahu ke zan aura ko dan in cikata gurbin farin cikina".

*****
      'Bangare na kuwa.....washe gari da safe da nazo gidan a 'kofar gida na samu Alhaji Baba zaune a kan farar kujerar roba yana hutawa.

   Ganin sa wurin ne ya sanya ni gaida shi sannan na shiga cikin gida.

     Yau kam parlourn babu kowa sai TV dake aiki shi ka'dai, ba gwanar zama inyi kallo ba ce ni shiyasa ma sam ko hankali na ban kai wurin TVn ba, kitchen na wuce wurin Ammi dan nasan tana can a dai-dai wannan lokacin.

  Gaida ta nayi sannan na sanar da ita cewa na ajiye a dinning kamar yanda naji suke 'kiran abin da shi.

Banko bi takan su Saif dake can 'dakunan su ba kawai nai wucewa ta waje.

Gurin Alhaji Baba na koma na zauna daga gefen sa, dama shi babu ruwan sa matu'kar na ha'du dashi to sai na tsaya surutu da yake shima biye ni yake yi.

  " Har kin fito ne?"
yace da ni yana kallo na.
Ina shirin zama kan wata kujerar nace masa " ehh na fito gidan shiru sai Ammi".
Sai yace
  " Ina jin suna can 'dakunan su basu fito ba tukunna, shiyasa ma ashe naga kin fito da wuri dan nasan idan da kin ha'du dasu Saifuddeen da ba yanzu zanga fitowar ki ba".

Dan 6ata rai nayi nace
" Ai nayi fa'da dasu ma kuma babu ruwana da Zaid "
Nayi maganar ina dama fuska tamkar yanzu ne abin ya faru.
" laifin me yayi har haka?"
Alhaji Baba ya tambaye ni yana kallona da fara'ar sa sai nace " ai shine jiya ya hana ni in taya shi zane".
Alhaji Baba murmushi yayi tare da fa'din
" Lallai Zaidu bai kyauta ba, amma ki barshi watarana ai da kansa ma zai ce miki ki taya shi idan yaga kin fishi iyawa dan nasan 'yar tawa gwana ce ko ba haka ba?"

" Hakane"
na bashi amsa ina washe ha'kora na jin dadin an yabe ni.
Shima murmushi yayi Alhaji Baban sai ya sake fa'din " to maza kije ki shirya zuwa makaranta karki makara kinji..bana son ana dukan yata kullum a makaranta"
Kai na juya na kalli hanya sannan nace masa
  " ni sai na huta zan tafi...ai na gaji da tafiyar".
A fili Alhaji Baba yayi murmushi mai sauti sannan yace " to 'yata ki huta amma ka'dan sai ki wuce ....".

Bai gama rufe bakin sa ba sai mukaji sallama daga bayan mu.
Alhaji ne ya amsa sannan muka kalle shi dukkan mu.
Sanye yake da wando 3quarter na rubber jeans da wata armless riga ja, wuyan sa rataye da headphone babba sai tsiyayar gumi yake yi.
Baki na ta6e gami da kawar da kaina gefe.
" barka da hutawa Alhaji"
Yace bayan ya iso ta gaban mu.
Fara'ar dake kan fuskar Alhaji naga ta karu fiye da na dazu wanda cikin hakan yace.
" Yauwa Muhammad gudun ya isa kenan?"
yayi mafanar yana kallon fuskar sa.

    Da murmushi kawai ya amsa Alhajin sannan batare da ya furta komai ba ya tunkari mashigar gidan nasu a hankali.

Ni kam 'kasa-'kasa nak hararar sa dan sau 'daya kawai ya kalle ni daga haka bai sake bi ta kaina ba.
Alhaji ne ya juyo ya kalle ni sai yace " Baki gaida yayan ki ba..."
Tun kafin ya dasa aya na bu'di baki na da 'dan 'karfi nace " ina kwana"
Ko kula ni.ma bai yi ba k'ilan bai ma san cewa da shi nake ba...ni kuwa ban kara ba sai ma na kawar da kaina.

Alhaji Baba murmushi yayi shi kam.
Daf da zai shige gidan Alhaji Baba ya 'kira sunan shi
" ammm Muhammad!"

Cak ya tsaya gami da waigowa cikin raina nace " ashe gaisuwar tawa ma yaji da gangan ya ki amsa min tunda gashi ya ji sunan shi da Alhaji Baba ya k'ira...ban koyi la'a kari da cewa yanayin amon muryar mu ba 'daya bane dashi.
..... Alhaji Baba ne ya ce dashi" sai kayi sauri ka shirya mu wuce da wuri ko....dan yau akwai sa'kon da nake so zan bayar".
Chapter 50 · 0% Book details