Sashe 10
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *6*
A hankali Deen ke tafiya da motar tamkar bai san yin tu'kin haka yake yi, sam baiji da'din abinda Noor tayi masa ba duk da yayi 'ko'karin ba'kin cikin sa amma sam ransa ya kasa sakewa da hakan.
Tsaban yanda yaji haushi 'kirjin sa har nauyi yake yi masa na takaici, ban dama marar sa data ri'ke sa.
Bai tashi sanin abin sosai bane har sai da yazo shiga gida, da yake babu gate man dake kula da 'kofar gidan so dole sai shine da kansa zai fito ya bu'de kafin ya shiga.
Yun'kurin da yayi da niyyan fita daga cikin motar ne ya sanya shi jin tamkar an sar'ke shine gaba 'daya, sosai yake jin feelings na damunsa, tsigar jikin sa duk ta mi'ke, ga cikin sa ma ba'a barshi a baya ba.
Koma wa yayi ya kwantar da kansa kan sitiyarin motar tare da lumshe idanun sa, Jiddah ce abu na farko da ta fara zuwa cikin ransa a lokacin amma sai yayi saurin girgiza kan sa a 'ko'karin sa na ganin ya gujewa tunanin ta.
Bai gama fitar da Jiddah a ransa ba yaji wayar sa dake cikin aljihun gaban rigar sa na vibration.
Share wayar yayi batare da ya duba mai 'kiran ba har ya tsinke take kuwa wani ya sake biyo baya.
'Dan 'karamin tsaki yaja jin yanda wayar ke 'kara shiga rayuwar sa bayan halin da yake ciki a lokacin.
Hannu ya kai ya lalu6o wayar wanda sunan *NOOREE* ya bayyana akai da manyan haruffa.
Kamar ba zai 'daga ba kuma sai ya yaja yayi receive tare da sada wayar da kunnan sa yayi shiru.
" Yah Deen"!
Ta 'kira sunan shi cike da damuwa.
Shiru yayi mata bai amsa ba.
Sai ta sake fa'din " Yah Deen kana jina.......ka isa gida lafiya ko?"
" miye matsalar ki da hakan?"
Yayi maganar cikin 'karfin hali.
Take idanun ta suka fara tara hawaye tace da shi
" Haba Yah Deen...laifi ne dan na tambaye ka hakan dan Allah?".
" To ni kaina ban sani ba tukunna, may be lafiyar na iso".
Ya bata amsa da da kewa.
Sai tace " Yah Deen bakace min shikenan ka ha'kura ba miye hakan kuma please kake min, kasan bazan juri fushin ka har hakan ba ko?"
Bai yi mata magana kawai sai dafe 'kirjin sa da yaji yayi masa wani suka mai azaba da ya ratsa har brain 'din sa, hatta wayar da ke hannun sa ma bai san lokacin da ta zame ta fa'di ba, take kuwa ta mutu a inda ta fa'din, 'kirjin sa ya dafe da hannun sa 'daya a hankali yake jero bayyananniyar salati cikin azaban ciwon da ya ha'de masa guda biyu.
Noor kam nata" hello!, hello!!!, Yah Deen....."
Taji shiru, bin wayar tayi da kallon mamaki, cikin ranta ta ayyana kar dai Yah Deen kashe wayar sa yayi.
Koda ta sake gwadawa kuwa ga mamakin ta switch off aka ce mata.
Sosai hakan ya ta6a ta bai tsaya iya zuciyar ta ba har sai da ya nuna a gangan jikin ta.
Dawowa tayi 'dakin da ta baro Ummah a ciki tana tafiya a hankali tamkar wacce 'kwai ya fashewa a ciki, inda ta sami Ummah nata a kishingi'de, yayin da Ummie ke kwance a gefen ta kan katifa tuni tayi bacci abinta.
Ummah na ganin ta ta mi'ke tare da gyara zaman ta da kyau tana kallon ta cike da murmushi.
Yanzu ta bar 'dakin jikin ta ko kayan kirki babu cuz fitowan ta daga bayi kenan ta watso ruwa shine ta 'dauki wayar ta fita 'kiran sa.
Inda dama manufar yin 'kiran shine dan taji ya ya isa gida ta kuma 'kara jin yanayin da yake ciki, dan ita kanta ta kasa samun natsuwa tun rabuwar su.
Rashin samun gamsasshiyar amsa daga gareshi da kuma tukuicin datse wayar da yayi ne ya sanya ta dawowa 'dakin cikin sanyin jiki.
" Menene haka 'yar nan? naga kin wani dawo wata iri meya faru?".
Ummah ta jefa mata tambaya tana kallon ta tuni kuma murmushi dake kan fuskar Ummah ya riki'da ya dawo damuwa.
Sai da ta sami bakin gadon dake 'dakin Ummah ta zauna kafin tace " bakomai Ummah, kawai na 'kira shi ne naji ko ya isa lafiya sai kuma yace min har yanzu bai kai ba".
Tana maganar ne tare da lalu6an abin shafa daga cikin jakar da suka zo da ita.
" Shine kuma kika dawo haka dan har yanzu bai 'karasa gidan ba? Miye abin damuwa a ciki? Mu'inuddeen ai ba ba'ko ko kuma yaro, 'dan gari ne fa .....kuma kin san shi da sabgogi...... ni fa har kin firgita ni wallahi da na ganki"
Ummah ta 'karasa maganar tata da 'dan sakin fuska.
Tunowa da tayi cewar man sha fan baya cikin jakar ne ya sanya ta sakin 'dan 'karamin tsaki a hankali.
Zipping jakar tayi sannan ta mi'ka hannu ta 'dauko mai 'din kuma sai a lokacin ne ta bawa Ummah amsar ta da fa'din " sabgogin mene da shi Ummah yanzu bacin duk abokan hul'dar tasa basa nan".
" kede ki bi a hankali uwata, ki daina sanya damuwa a ranki bisa wasu dalilai na daban marasa amfani da ma'ana, idan kince haka zaki cigaba da yi wallahi zaki sha wahala arayuwar nan.... hmm Allah kiyaye dai".
Ummah ta 'karasa da fa'din hakan tare da komawa ta kishingi'da abinta kamar 'dazun.
Noor kuwa har ta kammala da shafa mai 'din ta 'dauko kayan baccin ta sanya bata furta komai ga Ummah ba.
Mi'kewa tayi a gadon batare da ta 'kara fa'din komai ba cuz abinda Ummah take tunani daban yake da abinda ke tsakanin ta da Deen, ita kuwa tana ganin ba abin sanar wa haka ga kowa bane shiyasa kawai tayi shiru duk da kuwa ta fahimci Ummah kamar na ganin kishi take yi, duk da kuwa a yanda tasan halin sa ko da ace kishin ne a ranta to ba laifi ne amma ma bata sanyawa ranta faruwar wani abu daban ba a wannan lokacin, sam babu hakan cikin ranta a, dana sanin rashin 'kin amince masa ma takeyi duk da kuwa har a lokacin tana nan a kan bakan ta na farko, amma yanayin da taji yake magana ka'dai ma ya fi sanyata damuwa dan tasan babu mamaki fama yake da kansa akan 'kin amince masa da tayi.
Shiru ne ya 'dan biyo baya na wasu 'yan lokuta kowa da abinda yake sa'kwa cikin ransa, Ummah ce ta sake fa'din " ni kuwa ya jikin mijin naki fatan dai yanzu ciwon yayi sau'ki ?"
Sai da ta 'dan mi'kar da hannayan ta ta kuma lumshe idanu kafin tace " da sau'ki sosai sai godiya gaskiya, dan har ma na manta rabon da ya tashi masa....ina jin dai an dace ciwon ya tafi".
Ummah cewa tayi
" masha Allah, Allah ya 'kara lafiya da nisan kwana".
Da "Ameen Ameen " Noor ta amsa mata daga nan bata 'kara magana ba har bacci yayi gaba da ita.
*****
'Bangaren Deen kuwa da 'kyar ya samu zafin 'kirjin ya ragu masa inda ya lalla6a a 'dan ran'kwafe ya samu ya fita daga motar yaje ya bu'de gate 'din tare da jan motar ya shigar ciki.
Yanayin yanda yake tafiya idan ka ganshi har zakayi zaton cikin halin maye yake tsaban yanda yake tafiyar cikin rangaji shi ciwon da cikin sa keyi ne kawai ya dame sa.
Koda ya isa 'kofar parlourn ma sai da yayi 'ko'kari ya seta komai nasa, tafiyar sa da muryar sa ya daidaita ta yanda iyayen nasa ba zasu fahimci yanayin da yake ciki da wuri ba, amma a zahiri kallo 'daya zaka yi masa ka fahimci ba dai-dai yake ba musamman idan kayi duba da cikin idanun sa yanda suka riki'de zuwa ja suka kuma 'kan'kance, shi kansa ya san hakan amma bai damu ba saboda dare ne yasan gane hakan zai matu'kar yi musu wahalan gaske
Ciki-ciki yayi sallama yana daga wajen, jin an amsa shi ne yasa shi 'dago 'kafar sa ya shigo.
"Ka dawo ?"
Alhaji Baba ya tambaye sa sai ya amsa da " umm na dawo Alhaji"
A takaice.
Hanyar 'dakin sa ya nufa tare da furta "sai da safe Alhaji...."bai jira yaji nashi amsar ba ya 'kara fa'din" Ammee mu kwana lafiya".
"Zonan Deeni meke damun ka ne wai?"
Alhaji ne yayi wannan tambayar dan tun a muryar da yayi sallama Alhaji Baba ya gane ba lafiya ba.
Cak Deen ya tsaya da jin muryar Alhajin tare da 'dan juya idanu ya lumshe su ya kuma bu'dewa ba tare da yayi niyyan fa'din komai ba.
Alhaji ne ya sake fa'din" da kai nake magana ko?"
" Baba 'kirji na ke min zafi amma ba wata matsala bace, zan sha magani yanzu idan na shiga".
Ya bashi amsa da fa'din hakan dan hakan ka'dai zai iya furtawa ya kare kanshi batare da sun 'dago damuwar sa ba.
"Subhanallah"
Ammee ta ce cikin damuwa tare da tasowa ta nufo inda yake" me yaja hakan ?
Me yafaru bayan fitan naka ko dama haka yake yima kullum?"
Ammee ce ke jero masa wa'dan nan tambayoyin cikin tashin hankali.
Girgiza mata kai yayi a hankali tare da fa'din" Kar ki 'daga hankalin ki please Ammee, ba abin damuwa bane zai daina ne, bari inje insha magani yanzu".
"Wani irin kar in damu Mu'een ka ga idanun ka kuwa....?"
Bata gama kai aya ba ya tare ta da fa'din" idanu na bacci nake ji sosai ne shiyasa.......let me go nd take mu drugs.....okay".
Yayi maganar tare da 'ko'karin wucewa 'dakin sa.
" To Allah ya sawwa'ka" Alhaji ya fa'di yana daga inda yake zaunen cuz shi bai taso ba daman, batare da ya sake yun'kurin jefa masa wata tambayar ba ya barshi ya wuce 'din kamar yanda ya bu'kata.