Sashe 65
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da safe bayan gama breakfast, Alhaji Baba ya zaunar dashi ya ringa yi mai nasiha cikin natsuwa game da rayuwa, ha'kuri da kuma yadda da 'kaddara, sosai yayi 'ko'karin jawo hankalin sa akan hakan, ya 'kara da ro'kon sa akan ya maida hankali ya kula da karatun sa da kyau...Uncle Ja'afar ne ya sanar da shi cewa nextweek zasu fara registration dan haka ya bada himma ya kuma ri'ke Allah cikin Allah al'amuran sa.
Da yake Alhaji Baba yayi masa nasihan ne da sau'kak'kiyar harshe dan haka sosai Yah Deen ya fahimce shi ya kuma ji sau'ki cikin ransa...har ma sai yaji kamar bai kyautawa iyayen nasa ba da ya 'daga hankalin sa game da mutuwar.
Alhaji Baba bai bar shi ya tafi ba sai da ya tabbatar ya 'dauka masa al'kawari akan ba zai bar kowacce damuwa ta 'kara illata masa rayuwar sa ba zai fuskanci rayuwar sa da dukkan farin ciki...zai kuma rin'ka gode wa Mahallici bisa ga dukkan 'kaddarar da ta same shi.
Ku'di masu 'dan nauyi Alhaji Baba ya ciro ya bashi tare da tsaraba masu yawa duk kuwa da cewa tafiyar tasa ta bazata ce amma hakan bai hana Alhaji Baba tanadar masa da abinda ya kamata ba.
Jikin sa sanyi 'kalau ya 'karasa shirin sa, haka ya bar gidan da misalin 'karfe tara na safiya, ya tafi zuciyar sa cike da kewar ahalin sa.
Mu kam lokacin muna makaranta sai da muka dawo muka tarar ya wuce.
Ko da ya koma kuwa Uncle Ja'afar kansa sai da yayi mamakin dawowar tasa ganin kwanan sa biyu ne kacal da tafiya amma ya dawo, shi da yace zai yi a'kalla 2weeks acan me ya faru to ya tambaye shi...koda yace zasu fara registration ba wai ya fa'di hakan dan ya dawo bane cuz yasan akwai sauran lokaci kafin ma afara 'din.
Deen sai yace da shi ai Alhaji Baba ne yace ya dawo kawai ya fara shirye-shiryen registration.
Bayyananniyar murmushi Uncle Ja'afar yayi sannan ya 'kara da fa'din
" Har shiri akewa registration 'din kenan?"
Anty Zainab kuwa cewa tayi " Amma na ganka wani iri ba kamar yadda ka tafi da farin ciki ba Mu'een fatan dai ba wata matsala ba ce?" tayi maganar tana kallon sa.
Murmushi ya 'ka'kalo ya sanyawa fuskar sa sannan yace " Anty ba dole ki ganni haka ba..ni da zama ya gagareni acan, kema ai kinsan ba yanzu nayi niyyan dawowa ba".
Ajiyan zuciya ta sau'ke gami da fa'din " Allah ya kyauta"
Uncle Ja'afar kam bai yadda sam cewa babu abinda ya faru ba dan haka sai da ya 'kira Alhaji Baba ya sake tambayar shi sannan ya tabbatar da gaskiyar Mu'een 'din na cewa babu abinda ke damun sa, da yake Alhaji Baba ya 6oye masa batun bai sanar dashi gaskiyan lamari ba.
Hakan yasa bai 'kara bi ta kan damuwar Yah Deen 'din ba kawai ya 'kyale shi.
Yayin da shi kuma ya cigaba da ya'ki da zuciyar sa shi ka'dai ya san me yake ji, amma yana shan magungunan sa akan tsari baya wasa da shi ko bari su 'kare ma beyi idan yaga ya kusan 'karewa sai yaje ya 'karo wasu...haka kuma ya yi 'ko'kari sosai wajen 'daukan shawarwari da nasihohin da iyayen sa sukayi masa, gaba 'daya ya dogara ga Allah ya mi'ka lamuran sa kaf agare shi, yana kuma Addu'ah kamar yadda Ammi tace da shi yana mata yana kuma yiwa kansa, da haka har suka fara registration.
Kana ganin sa zaka san akwai abinda ke damun sa ko dan saboda 'yar ramar da yayi ma ga kuma shiru-shirun da ya 'kara zama musamman idan kayi masa sani na gaske...a hakan ma wai ba'karamin 'ko'kari yayi wajen kawar da damuwar ba.
Anty Zainab ma abin na damun ta ko da ta yiwa Uncle Uncle Ja'far magana akan hakan kuma sai yace ta bar shi damuwar makaranta ce kawai a ransa.
Tun washe garin tafiyar sa Alhaji Baba ma ya tafi Plateau state, inda yaje duba aikin da ake yi masa acan din na bu'de sabon gidan gona amma na zallar kaji.
Kusan satin sa guda acan kafin ya dawo, lokacin da ya dawo kuwa ni ina gidan mu wurin Ummah ta, su Addah ta Maryam da yaran ta ne suka zo shine naje gidan...kwana na biyu agidan Ammi tazo muka koma tare.
Anan naje na tarar da uban tsarabar kaya da Alhaji Baba yayo min harda kayan wasa set masu kyan gaske, murna kamar baki na zai yage Saif ma na taya ni farin ciki haka ma Ammi.
'Bangaren Yah Deen kuwa a wannan yanayin yayi shiri ya wuce Jigawa State duk da kuwa zuwa yanzun sam makarantar ta fice a ransa haka ma course 'din da yake dama ba ra'ayin sa bane saboda soyayyar sa ne yasa shi tilastawa kansa son course 'din, yanzun.kuwa da ya rasa soyayyar sai yake jin baya son course 'din ma tsohon nashi burin yake so, tsoron yanda Uncle Ja'afar zai 'dauki maganar ne kawai ya sanya shi jan bakin sa yayi shiru, amma ba wai dan ransa ya so ba.
Haka ya bar abin cikin ransa ya shirya ya tafi makarantar, inda anan ne ya ha'du da Husnah wurin wani signing suka ha'du bayan fahimtar cewa daga gari 'daya suka zo.
Husnah taji da'din ha'duwa da shi..da yake dama ba ta san kowa anan 'din ba, tun daga ranar suka zama abokai, bata samun sakin fuskar sa sosai amma a hakan bata ta6a nuna damuwa kan hakan ba, cuz Husna irin yaran nan ne masu nacin tsiya, duk inda zai je yin signing sai ta raka shi, haka tayi ta biye masa har ya kammala nashi sannan ta 'karasa nata ita ma.
Baya mata hira dan sai suyi zaman 2hrs da shi amma kalaman sa basu fi biyar zuwa shida ba, ita kuwa gwana ce wurin surutu inda anan ma zaka samu amsar sa be wuce eh, a a ko kuma kawai idanu ba, in kuwa abin dariya me sai dai kawai yayi murmushi, ita hakan bai ta6a damun ta ba dan a fa'dar ta ita mutun miskili na birge ta, she thought miskilanci kawai ke damun Mu'een bata san damuwar sa daban ba shi.
Har ta fara karatu a AMINU SALEH COLLEGE OF EDUCATION dake can garin Azare inda take karantar PHYSICAL AND HEALTH EDUCATION, amma shekarar ta 'daya acan ta bari da yake ba wai ra'ayin ta bane mahaifiyar ta ce ta sata, wani Yayan ta ta yiwa complaint shiyasa wannan shekarar aka nema mata gurbi a anan Dutse shine ha'duwar su da Yah Deen.
Husna kusan sa'ar Mu'een ce dan kuwa ko ya girme ma ta ma bai fi da shekara 'daya ba, a haka da shariyar tasa amma kafin su rabu sai da suka sha'ku da juna cuz har suka kammala registration tare suke har suka koma gida.
Ko ranar da zasu dawo ma tare suka taho da ita sai da suka shigo cikin gari ne kafin kowa yayi hanyar sa.
Da komawar sa gida ne yace da Uncle Ja'afar shi ba zai zauna Campus ba cuz sun cika hayaniya shi kuma bai so, duk yadda Uncle Ja'afar ya so fahimtar da shi amfanin zaman sa cikin 'yan uwan sa 'dalibai Yah Deen 'kin amincewa yayi daga 'karshe dole Uncle Ja'afar yayi magana da wani abokin sa akan anema masa gida 'dan madaidaici na haya...wanda bai da tazara sosai da makarantar.
Yah Deen ne ya sanar da Alhaji Baba cewa shi baya son zama cikin makaranta, take Alhaji Baba sai ya 'kira Uncle Ja'far sukayi magana sai yayi masa transfern ku'di yace a siya masa gidan zai fi akan haya.
Wannan dalilin ne ya sanya akalar neman gidan ta sauya daga na haya zuwa na siya.
An kuwa yi sa'a an sami gidan sai dai yanada 'dan nisa ka'dan da makarantar amma ahakan yace shi ya masa...dan ba laifi gidan na da kyau da tsari gwanin birgewa.
Uncle Ja'far da kansa yayi masa siyayyan sauran kayan amfani da za'a saka a gidan hatta kujeru sai da ya zuba masa masu kyau amma ba manya ba da katifar sa babba da sauran abubuwan amfani.
A waya Alhaji Baba yayi ta masa fa'da akan tara abokan banza, yace kar ya ga ya ke6e gefe babu idon manyan sa.
Yace " Karka manta duk abinda zaka aikata Allah na ganin ka domin shi ba sai angaya masa ba, dan haka ka san da wa'yan da zaka ringa hul'da wa'danda bazasu ta6a maka daidaituwar imanin ka ba...sannan daga 'karshe karka manta da al'kawarin da ka 'daukar min..and please ka dinga kulawa da lafiyar ka kaji Babana? ".
Alhaji Baba ya 'karashe da lallashi.
Dama bashi da yawan tara abokai hakan yasa nasihar Alhajin saurin kar6uwa a zuciyar sa...daga 'karshe godiya yayi masa sannan ya yanke 'kiran ba tare da damuwar komai ba.
.....Husnah Campus take ita cikin sabbin 'kawayen ta, gashi kuma ba course 'daya suke da Yah Deen ba, hakan sai ya rage kaso mafi yawa na ha'duwar su, duk dama ita bata ta6a yadda rana guda ta wuce batare da ta ganshi ba.
'Bangaren sa kuwa abin ba haka yake ba, dan shi bai damu ba da su ha'du ko kar su ha'du sam bai damu da ganin ta ba, illah iyaka idan ta 'kira shi ta tambayi inda yake sai ya gaya mata ita kuwa tazo ta same shi...sau tari ma yakan ui mata 'karyar yana da lecture a time 'din ita kuwa sai tace to tana jiran sa idan ya fito.
Amma da kansa bai ta6a zuwa neman ta ba...bai ta6a 'kiran ta kuma dan wai su ha'du ba.