← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 211

Sashe 85

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yah Deen kam ha'kuri ya dinga bashi cikin kwantar da murya tare da shirga masa 'karyar baida lafiya ne shiyasa, burin sa kawai yaji ko Uncle Ja'afar na da masaniya akan abinda ya farun tare da son sanin ko yasan 6oyayyen shirin Alhaji akan sa....yayin da a masifance Uncle Ja'afar yace da shi " Da baka da lafiyan kuma ka sanar da ni ne?"
" So sorry bazan sake ba Uncle".
'Karamin tsaki yaja tare da fa'din ya jikin to?"
" Ai ina jin muryar ka na warke kamar ba ni ba".
Cewar Yah Deen yana 'dan smilling da bai wuce kan fuskar sa ba.
" 'Karyar banza sai kace ban san halin ka ba Mu'een".
Yah Deen 'yar dariya kawai yayi batare da ya 'kara fa'din komai ba.
Uncle Ja'afar ne ya sake fa'din"...ya batun school kuma, hutu ya 'kare ko?"

" Erh mun kusa komawa Insha Allahu 'karshen week 'din nan ma...ina Aunty na?"
Ya 'karashe da tambayar sa Anty Zainab.
Ja'afar kam yana shirin yanke 'kiran yace" Hala manta sunan da kayi saving number 'din ta a wayar kayi".
Bai sake sauraran jin komai daga gareshi ba kawai ya yanke 'kiran yayin da Mu'een ya bi wayar da kallo da mamakin rashin jin wani abu daga bakin sa da ya danganci damuwar da ke damun sa.

Ga dukkan alamu Uncle J bai san komai kan lamarin ba tunda baiga alamun hakan ko cikin kalaman sa ba.

Murmushi ya saki na jin da'din rashin sanar da Uncle J da Alhaji bai yi ba, nan take yana murmushin ya 'kira layin Antyn sa Zainab inda suka gaisa cikin sakin fuska da walwala itama tana mai mitan rashin samun wayar sa cikin kwanakin.

      'Karyar da yayiwa Uncle Ja'afar itama shi yai mata sai dai ita kam cewa tayi" Ya Ammi bata sanar da ni batun rashin lafiyar ba kuma?"
Ai da sauri ya bata amsa da fa'din" May be mantawa tayi Anty".
" Ammin ce zata manta da batun jinyar ka Mu'een?"
Anty Zainab ta tambaya mamaki bayyane cikin kalaman ta haka ma kan fuskar ta.
Sai yace
" Gashi kuwa, Anty ai babu mamaki...kinsan Ammi tunda ta samu wannan yarinyar ta daina so na, kullum masifa take min ban isa ko aikan yarinyar nayi ba sai ta tsigale ni".

Dariya Anty Zainab tayi tace" k'ilan kana muzguna mata ne shiyasa Ammi take yima haka amma ai yarinyar bata da matsala a yadda na fahimce ta".
Yace
" Ke de Anty kiyi shiru kawai amma ni da nake tare da su ni zan bada labari...".
Taran sa tayi da fa'din
"....Ai gaskiya ne Mu'een...ni dama nake cewa zan ro'ki Ammi ta bamu aron yarinyar danni fa tayi min gaskiya ina son ta sai mu zauna tare dukkan mu idan mun dawo Bauchi".
'Dan 6ata rai yayi yace " Anty ni kuma fa?"
" Har da kai ai sai kazama yayanta inda rabo kuma watarana da iznin Allah sai ka zamo mijin ta na har abada".
Da wuri ya furta " God forbid...Allah ya sawwa'ka Anty ina zan kai ta ni kuma?"
Zaro idanu Anty Zainab tayi tace masa" Inda ya dace da ita mana, jimin yaro da shiririta, har haka zaka ce Mu'een an gaya ma ana gayawa Allah yadda zaiyi ne?"
" Ni dai please Anty ki bar zancen nan...shima Allah zai kiyaye bazai bar hakan ya faru ba".
Anty cewa tayi " Ni dai da za'a ban za6i Allah ita zan za6a ka maka dan nasan ba 'karamin sa'a zakayi ba da samun ta".
" Hasara dai".
Ya fa'di 'kasan ma'koshi amma Anty sai da ta jiyo shi.
"...Hmm...Fatana ni dai a kullum inga ranar da za'a ce wannan yaron nawa na fama da zuciyar sa akanta..."

Lumshe idanu yayi yana tuno Nannen sa, masoyiyar sa, sahibar zuciyar sa, baya jin zai 'kara yiwa wata 'ya mace kwatankwacin son da ya yiwa Nanne har abada balle har tasa ciwon sa tashi, ko ita Nannen ma bata tada masa ciwon ba balle wata daban can da ya san bazata kai Nanne daraja a wurin sa ba.

Idanun sa a rufen cikin sanyin murya yace
" Babu ita Anty...ba ma za'a haifeta har abada".

'Yar dariya Anty tayi daga can 6angaren tace"...Zamu gani ai...in da rai kamar yau ne, ko angaya maka abin ana gudun sa cikin sau'ki ne tamkar yadda kake gudun abokai?"

Shiru yayi bai amsata ta ba sai ta cigaba da fa'din" Gara ka bari in mana kamun 'kafa wurin Ammi tun kafin wani ya riga mu".

'Kit!.. yayi saurin datse 'kiran cike da jin haushin maganar ta...cikin ransa yake ayyana" ina zan kai wannan abin da jiki ko'ina flat sam babu mamora, da'din me zata jiyar dani banda aikin kuka da ta iya da kayan takaici, yana ji cewa irin Noor ko a 'kafa aka 'daura masa Allah sai ya kunce ta ya tafi ya barta da gudu ma kuwa...har gara 'dayan yarinyar ma wato Ma'u, babu laifi ita tana da abin kallo ajikin ta...."

Take salo da tsarin tunanin sa ya canza, wuri guda ya 'kurawa idanu yana tariyo ranar da ya ha'da jiki da ita (Ma'u) yanda ya jima yana jin tudun 'yan matasan boobs 'din ta a jikin sa, tun ranar yake so ya samu damar ganin su da idanu amma sam ya rasa ta yadda hakan zai faru.

Tsaki ya saki a fili yana lumshe idanu tare da kishingi'da, a hankali tunanin sa ya koma kan Husnah, tuno yanayin surar jikin ta take sai ya saki ajiyar numfashi mai 'dumi, gani yake yi kamar ni har abada har in 'kare kaf 'din rayuwa ta bazan ta6a kamo Husnah 6angaren halitta ba, a fa'dar sa bai ma ga alama ba da har Anty ke yi masa fatan kasancewa da ni.

Wannan 'dan tuno Husnah da yayi sai yasa take yaji shi on, wani irin shau'kin son kasancewa da ita ne ya kama shi.

Aikin kenan dama indai tsakanin Yah Deen da Husnah ne ta 6angaren sa babu komai cikin zuciyar sa daya danganci so ko 'kauna illah son kasancewa da ita da yake yi koda wani lokaci, ya kuma rataya hakan akanta ya maida ta abar jin da'din sa kawai a mori rayuwa.

Yayin da Husnah ke yi masa so, so irin na asali mai ninkuwa a duk lokacin da take tare da shi, soyayya take masa wanda babu gauraye ko algus acikin sa, da tunanin yiyuwar aure tsakanin su watarana.

Akwai wani cousin 'din ta mai suna Hisham dake tsananin 'kaunar ta da aure amma ta'ki sake mai fuska ta 'kwallafa ranta akan Yah Deen bata san shi a 6angaren sa abin ba haka yake ba sam....(ni kuwa nace stop deceiving ur self am mata).

Imrana baya nan ya tafi Kano yanzu shiyasa gidan ya kasance shi ka'dai ke rayuwar sa babu mai takurasa....wa'dannan shai'danun tunanin da yayi ta biyewa zuciyar sa akai ne ya sanya shi jin muguwar sha'awa na taso masa.

Sai yanzun yaji babu dadi da rashin Imrana a kusa, ya so da yana nan da sun kammala maganar waccan yarinyar da ya'ki bashi ha'din kai akanta kwanaki, amma sai akayi rashin sa'a baya gari a ranar....fatan shi dai kawai shine Allah yasa dagaske Imrana yake yi cewa da yayi yarinyar itace waccan me zuwa gidan shi da 'yar gidan Ammin nan...cuz waccen tafi tsaye masa a ransa, ita yake so ya mora yanda take da 'danyen 'kuruciyar nan yasan zai kwashi gara.
(Hmm....Allah ya shiryi wannan 'dan gidan Ammin gaskiya).

Yanda abin ya gama ratsa shi ya kashe mai jiki nan take ya sanya shi mantawa da 6acin ran da Alhaji Baba yayi da shi kwata-kwata, neman hanyar da zai kawar da abinda ke damun sa kawai yake yi.

Bashi da mafita game da abinda yake ji wanda tasa dole ba dan yaso ba ya dannawa Husnah 'kira tare da sake yin luf kan kujerar da yake kwance..idanun sa duk sun 'kan'kance sun yi wani iri da su...yasan Husnah ka'dai yake da shi da zata taimake shi cikin wannan yanayin batare da yasha wahala ba.

Yanajin wayar tafara ringing sai ya lumshe idanu ya kifa wayar kan kunnen sa na dama yayin da hannun sa 'daya ke yawo saman cikin sa zuwa marar sa a hankali.

Har sai da wayar ta kusan tsinkewa kafin Husnah ta 'dauka tana yatsina fuska cike da jin haushin korar da yayi mata, bayan haka kuma bai ko 'kira ta ba tun ranar, haka ma sa'k'konin ban ha'kuri da tai ta tura masa ko reply 'din guda bata gani ba, da wannan tunanin ta daure a yatsine ta furta" Hello!"

Shiru yayi yana murmushin mugunta, tuno irin cin mutuncin da yayi mata rannan da tazo.
" Helloo!!
Ta sake fa'di kamar dole aka sanya ta.

Yah Deen bai amsa ba illah numfashi da ya furzar mai 'dumi wanda hatta Husnah sai da ta jiyo shi take kuwa jikin ta ya amshi sa'kon kamar wawuya, cikin sanyin murya da dauriya ta sake fa'din" Hello!!!... wai waye ne?"

Sai yanzun ya bu'di baki yace
" Husnah!"
Cikin mayaudariyar muryar sa mai narkar da zuciya.

Husnah na jin yanda 'kira sunan ta ta wani lumshe idanu saboda jin wani irin abu da ya tsarga mata tun daga kanta ya ratsa mata har 'kafafu, wani sanyin da'di  da farin ciki taji ta ciki marar misaltuwa wanda ya sanya ta kasa amsa sunan tan daya 'kira.

Yayin da Yah Deen ya cigaba da fa'din ".....Husnah har kin manta da ni da wuri haka ko?..kenan goge layi na kika yi cikin wayar ki?"

'Kasan ma'koshi tayi dauriyar amsawa da " um-um".
" To me yasa kika share ni? Baki damu kiji halin da nake ciki ba dan baki sona ko?"
Muryar ta na 'dan rawa tace" Ka manta abinda kayi min ne Mu'een?"

Murmushi yayi daga inda yake cikin son kawar mata da wancen zancen yace" Ba 'karamin kewar ki nayi ba fa Husnah na damu sosai...yaushe zaki koma school please? "
" Sunday".
Ta bashi amsa a takaice.
Sai yace
" Fatan kin shirya ha'duwar mu dan ni gaskiya na matsu...dan Allah ki taho da wuri karki sani jiran ki kinji?"
Chapter 85 · 0% Book details