← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 211

Sashe 11

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Deen 'dakin sa na da dake gidan ya wuce, sai da ya shiga bathroom ya watso ruwa inda ya ya 'dauki tsawon lokaci kafin ya fito sai yayi kwanciyar sa a kan gado daya ke yanzu ma ya 'dan rage jin abinda yake ji 'din sai 'dan abinda ba'a rasa ba..... ba dai kamar 'dazun ba, amma duk da haka zuciyar shi bata hana shi lalu6o wayar sa yayi dialling wata number ba tare da lafewa sosai kan gadon.
(Kuyi ha'kuri fa dan nima banga sunan ba ballantana in fa'da muku).

Ammee sosai ta so 'daga hankalin ta da jin cewar 'kirjin Deen na ciwo, tsoro take yi kar ciwon zuciyar sa ne ke shirin motsawa.
Haka ta zauna ta dafe kanta, gaba 'daya ta nemi natsuwar ranta ta rasa shi.

Alhaji Baba ke kwantar mata da hankali akan kar ta damu ba abu mai tsanani bane tunda ma gashi ai da kansa ya shigo gidan.
Taso ta je ta sake duba shi bayan shigar tasa amma sai Alhaji ya hana ta da cewar " koma meke damun sa ai a yanzu ba zai so a dame sa ba ta bar shi kawai zuwa safiya in da rai komai zai dai-dai ta".

Haka Ammee ta ta ha'kura ba dan taso ba ta tafi ta kwanta.

Alhaji Baba kam anan ta bar shi yana zaune tsawon lokaci yana tunani, shi kansa fa abin ya dame sa kawai ya danne ne a zuciyar sa.
Sai daya kusan raba dare a nan palourn sannan ya tashi ya 'karasa 'dakin Deen 'din, a hankali ya tura 'kofar inda ya same shi kwance jikin sa ba ko riga sai dai dogon wando kawai na bacci da ya sanya.
Hannun sa duka biyu dafe da cikin sa yana kwance rigingine.
Duk kuwa da cewa bacci yake yi amma zaka ga goshin sa a tattare, kallo 'daya zaka masa ka fahimci cewa ba'a yanayi mai da'di yayi baccin ba.

Alhaji Baba kai ya jijjiga ganin yanayin Deen 'din, domin a fili yanayin sa ya fallasa asirin zuciyar sa, Alhaji Baba bai sha wani wahalar gane 'karyar da Deen ya sharara ba na cewa 'kirjin sa ne ke ciwo, amma dubi yanda ya dafe cikin sa.
Godiya ya jerowa mahallici Alhamdulillah har sau uku, da kuma fatan Allah yasa ba zuciyar bace da gaske, idan ya kasance hakan kuwa zai matu'kar jin da'di.

Jijjiga kai Alhaji Baba yayi tare da fa'din " Allah ya shirya min kai Mu'een Allah ya yafe mana kura-kuran mu gaba 'daya".(AMEEEN).

*****
" Daddy ina Mummy na?"

Jasmine dake tsaye daga bakin gadon da yake kwance ta tambaye sa hannun ta kan sa tana wasa da suman kansa, fuskar sa na 'daya gefen daya ke yana cikin baccin yaji hannun nata a kansa wanda sanadin hakan ne ma yasa shi farkawa.

A hankali ya juyo ya tsura mata idanu yana kallon ta cikin kyakkyawan shirin ta da yasan aikin Ammee ne a yau 'din, sosai yake son 'yar tasa da dukkan zuciyar sa, ba'kin cikin ta sam baya fatan gani har 'karshen rayuwar sa, buri, 'kauna da soyayyar sa kaf a kanta suka 'kare, zaka ga walwalar sa koda kuwa waye kai matu'kar ka sanya Jasmine cikin farin ciki.
Juyi yayi tare da 'dan yin mi'ka ka'dan, hannun sa ya kai yaja hancin ta yana murmushi yace " baki gaida ni ba kike tambayar mummyn ki ko?"

Kafin ma ya rufe bakin sa tayi gaggawan fa'din
"Ina kwana Daddy...." batare da ta jira amsa ba ta 'kara da fa'din" ai na gaida Baba Alhaji ma da Ammee, Baba Alhaji ya bani dabino da zam-zam".

"Iyeh Baby na ta dawo 'yar gatan su Alhaji kenan.....wato dan haka ne yasa har kika manta ki gaida ni ko?"

Jas jijjiga kanta tayi tare da fa'din " ah ah ai jan gaishe ka har da Mummy na ma".

" Mummyn naki ai bata nan itama taje wajen maman ta".
Cewar Deen yana kallon ta.

" To Daddy ka kaini wurin ta ".
Jas ta fa'di cike da shagwa6a kamar ba itace me surutu yanzun ba.

Shiru Deen yayi kawai ya kauda idanun sa a kanta ya mayar gefe yana tunanin yanda zaiyi da ita.
D'ayan wayar sa da ya kalla ne a gefen gadon yasa shi mi'ka hannu ya 'dauko ta, dialling numbern Noor yayi tare da 'kurawa wayar idanu, sai yanzu ma ya tuno abinda ya faru jiya, sam bai ga laifin ta ba domin ya san laifin sa ne gaba d'aya, amma me yasa itan bazata iya yi masa uzuri na rana 'daya ba?"

Noor kuwa fitowan ta kenan daga wanka daya ke tasan yau zasu koma kuma da wuri zasu tafi cuz idan sun koma Deen ma zai wuce Abuja duk a yau 'din, so shiyasa take 'ko'karin shiryawa da wuri dan kar su rigata shiri.

'Karan wayar ta da taji ne yasa hankalin ta ya koma can, tana ganin sunan Deen sai tayi saurin danna receive don dama tun jiya ta kwana da shi a cikin ranta.

Sassanyan muryar ta da yaji tana sallama cikin wayar ne yasa shi lumshe idanu " Barka da safiya Yah Deen".
Ta 'kara fa'di bayan sallamar daga 'dayan 6angaren.

Bai amsa mata ba sai yayi saurin mi'kawa Jas wayar shi kuma ya tashi ya shige bayi kamar an tsikare shi.

" Mummy".
Jas tace tana turo baki.

Ajiyan zuciya Noor ta sau'ke tare da fa'din
" Na'am Mamana ke ce?"

" Umm "
Jas ma tace a takaice.
Sai Noor ta sake fa'din " Ya a kayi baby kina lafiya ko? ina Daddy?"

"Yana bathroom".
Jas ta bata amsar 'daya daga cikin tambayoyin nata wanda taga zata iya badawa.

Noor murmushi ta saki a 'dayan 6angaren, tasan ba mamaki Deen fushi yake yi da ita, shiyasa ya shige bayi bayan ya ha'da Jasmine da wayar tunda ai tasan Jas ba iya 'kira zatayi da kanta ba dole sai an mata.

" Mummy ni zan zo gurin ki.....".
Da taji Jasmine na fa'di ne ya sanya ta yanke tunanin da take yi da kulawa tace da ita.
" me kika ce Baby ban jiki da kyau ba".

" Ni gurin ki nake so Mummy".
Jas ta sake maimaitawa a sakalce.

Murmushi Noor tayi tace
" Ai baki ko gaishe ni ba dan haka babu gurina da zaki zo nima ba ruwana".

" sorry Mummy, good morning".

" Yauwa my princess....ko ke fa, hope kowa na lafiya?"

"Ehh har da nima Mummy, Ammee ta min wanka ta samin turare a jikina".

"Ahh masha Allah ashe yarinya ta tayi kyau sosai ko?"

Jas washe 'yan ha'kwaran ta tayi na jin da'din maganar.

Noor sai tace " kin zama 'yar gatan Ammee kenan".

" Harda Baba Alhaji ma ai shima ya bani zuma da zam-zam da dabino na ci".

" iyeh....duka ke ka'dai mamana, gaskiya Alhaji ya kyauta, me kika ce masa to".
Noor ta 'karashe da tambaya sai Jas tayi saurin fa'din" nace masa nagode".

"Yauwa Babyn Mummy, May Allah's blessing be with you....hum".

Deen da fitowar sa kenan daga bathroom 'din kunnuwan sa suka jiyo addu'ar Noor, a saman la66an sa ya amsa da " Ameen summah Ameen".

Noor kuwa sai tace da Jas 'din" bari nima in shirya ko sai ki jirani zan zo kinji.... sai mu koma gidan mu ko ba kya so?"

A hankali Jas ta amsa da " inaso".

" Yauwa Baby bye"
Daga haka ta yanke 'kiran tare da cigaba da shirin ta.

*****
Lokacin da yaje 'dauko Noor a gida tare da Jasmine suka tafi, kuma ga mamakin Noor sai taga fuskar sa wasai a sake ba kamar yadda ta tsammaci ganin sa ba, cuz tayi tunanin zai yi fushi da ita ne tunda har ya kashe wayar sa jiya suna cikin magana.

Sosai taji da'din hakan da yayin har take jinjinawa wannan ranar mai tattare da sa'a a gareta, da har tayi masa laifi amma bai 6ata ransa ba.

Sallama yayi wa Ummah suka fito a tare dukkan su da Jas bayan Ummah ta cika su da tsaraba irin nasu, da tulin dabino, Ummie ce ta fito musu da shi aka sanya bayan mota.

Haka suka rabu da Ummah cikin farin ciki tana tsokanar Jasmine wai tsohuwa mai sunan flower, Jas kuwa tace ita ba mai sunan flower ba ce ita mai sunan maman Daddy ce".

Dariya suka 'dan yi kafin Ummah ta bisu da Addu'ahn sau'ka lafiya.

Ko cikin motan ma Noor shiru tayi fuskar ta cike da annuri, har kwantar da kanta tayi jikin kujera tana murmushi ita ka'dai.

Haka har suka isa gidan Alhaji Baba basuyi wani dogon magana ba tsakanin su, nan ma dukkan su suka shiga cikin gidan, Noor ta gaida in-laws 'din nata tare da yi musu sallamar tafiya.

Alhaji Baba bai bar su sun tafi ba har sai da ya 'kara jan hankalin su sosai a kan rayuwar duniya da kuma ha'kuri da juna cikin zamantakewar su.

Ammee ma sai da ta 'kara da nata kamar wasu sabbin aure su Alhaji basa gajiya da sake tunatar musu da muhimmancin kasancewar su a tare da junan su.

Daga 'karshe Ammee tace da Deen dan Allah ya daina wasa da shan maganin sa dan jiyan nan sosai ya so 'daga mata hankali dan ma Allah yasa ciwon bai yi tsanani ba.

Murmushi Deen yayi yace da ita " kar ki damu Ammee na insha Allahu ina nan araye har sai kingan ni cikin jikokina nima".

Murmushi sukayi dukkan su Ammee kuwa tace " ja'iri kakar ka ka mai dani ko?".

Basu 'kara 6ata wani dogon lokaci ba suka 'dauki hanyar Bauchi, Noor kam da'di take ji har cikin ranta, lokaci-lokaci ta kan tsura masa idanu sai kuma ta 'dauke, ba'a 'daukan lokaci kuma sai ta sake.
Sosai yake bata mamaki musamman da taji bai tado maganar jiya ba ya share tamkar babu abinda ya faru.

Deen kam kasa ha'kuri yayi da kallon har sai da ya tambayi dalili shima 'din fuskar sa a sake wasai yayi tambayar .
Chapter 11 · 0% Book details