← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 211

Sashe 44

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiru yayi mata bai furta komai ba dan abinda yake ji cikin jikin sa ne yake sake hauhawa tsawon da'ki'ka uku yana fama da bugun zuciya sannan a hankali cikin 'karfin hali yace da ita " ta shi Rahma...mu fita waje zafi na damu na anan sosai".

'Kin kula shi tayi sai ma ta sake yin luf tamkar bata ji abinda yace da ita ba, ganin hakan ne ya sanya shi sakin tsaki cikin zuciyar sa dan yau 'din sosai yake jin sa wani iri bai san me yasa ba haka kawai yake jin kansa a tsarge.

" Rahma please 'dagani mana...je ki saka ko hijab ne mu koma waje......"

Taran shi tayi da fa'din " ni fa banson wajen yau dan Allah mu zauna anan kawai ?"

Ganin da gaske take yi bazata 'daga shi ba ya sanya shi janye 'kafar sa daga
kar'kashin kanta da 'karfi yana shirin mi'kewa sai ta kamo hannun sa gami da rutsa shi da idanun tace " wai yau meke damun ka ne dan Allah ko ni 'din ce baka son gani...?

Sai ga hawaye shar ya gangaro mata wanda ganin hakan ya sanya shi fasa mi'kewan ya koma ya zauna gami da kallon ta da mamaki, yayin da ta cigaba da fa'din.."...ni bansan me kake so inyi maka ba da zai sa ka soni, kullun ni ka'dai ke damuwa da kai ni ka'dai ke son ka...ban isa nayi tambaya ka bani amsa directly ba kullum ina lura da kai, gashi yanzu ma abu na damun ka amma bazaka sanar dani ba so kake yi sai zuciyata ta buga tukunna ko?"
Tana gama fa'din hakan sai ta cigaba da kukan ta.

Jikin sa sanyi yayi shi kansa ya san baya kyauta mata amma ai yau 'din shi damuwar sa daban ce kuma baya tunanin zata fahimce shi, taya ma zai iya bayyana mata halin da ya tsinci kansa a yau 'din wanda shi kansa ba zai iya fasalta shi ba...a hankali ya kai hannun sa 'daya ya kamo nata hannun sai tayi saurin ri'kewa gami da tasowa ta fa'do jikin sa kamar dama jira take yi sai ta rungume shi.

Shima 'din hannu yasa ya 'kara ha'de ta da jikin sa sosai.....sau 'daya ya furta " sorry dear don't cry...owk"
A hankali cikin ra'da yayi maganar daga nan shiru ne ya biyu baya illah sautin sheshshe'kan ta dake cigaba da tashi a parlourn.

Tsawon kusan mintina uku sannan ya sake fa'din " sorry!"
Yana bubbuga bayan ta.

Ganin bata da niyyan barin kukan ne yasa shi saurin cireta daga jikin sa tare da fa'din " wai kukan duk na menene haka ba nace ya isa ba?"
A 'dan hassale yayi maganar idanun su cikin na juna take kuwa sai wani hawayen ya 'kara sau'ko mata wanda yasa Mu'een saurin rintse idanu ya kuma bu'de su nan take.

" Ai dama batun yau ba na fahimci kai baka sona".
Ta fa'da hawaye na sau'ko mata.

Sai yayi saurin tambayar ta " me kike so Rahma in miki...please ki daina wannan abin ban son kukan nan ni".

Bata kula shi ba sai ma sabon sheshe'kan da ta fara wanda ya matu'kar bawa Mu'een haushi da ya rasa yanda zai yi da ita kawai sai toshe mata baki da nashi.

Cak kukan nata ya tsaya shima da farko tsayawa yayi cuz bai san me zeyi bayan hakan ba.
Amma sabon yanayin da ya fara tsintan kansa a ciki sai ya sanya shi jin tamkar bashi bane da Rahma a wurin, gaba 'daya ya manta a ina yake ya manta matsayin Rahma a wurin sa.

Ji yake tamkar ana ingiza shi....a hankali ya maida idanun sa ya lumshe tare da kamo lips 'din ta na 'kasa ya fara 'daura mata sabon darasi.
Yana jin yanda ta 'kan'kame masa hannu da jin salon darasin nasa wanda hakan ya 'kara bashi 'kwarin gwiwa wurin kamo harshen ta ya cigaba da abinda yake yi.
Shi kansa ji yayi take komai ya kwance masa, fiye da yanayin da ya tsinci kansa 'dazu yake sake ji cikin jikin sa.....wannan dalilin ne ya sanya hannun sa ya kasa tsayuwa wuri guda a jikin ta yana sake wargaza mata matashiyar yanayin ta.

Rahama bata hana shi ba sai ma tayi luf a jikin sa tana kar6an darasin da bu'da'dden brain 'din ta yayin da ta tattaro hankalin ta da 'kananun kukan banzan da take yi gaba 'daya ta dun'kula su wuri guda suka koma zuciyar ta.
Lokacin da ya tsinci hannun sa cikin 'yar shimin dake jikin ta sosai hakan ya ta6a zuciyar sa sai dai duk da halin da yake ciki hakan bai sa ya gaza fahimtar nata yanayin ba a lokacin, dan wani sassanyar ajiyan zuciya ta saki mai matu'kar shiga jiki.

Shi kam sam ya manta da cewar lallashi yake yi dan gaba 'daya tsintan kansa yayi a wata duniya ta daban, ganin kamar shimin nata na hana shi sakewa ne ya sanya shi janye shi zuwa sama gami da bin ilahirin jikin ta da sumba, yana niyyan kaiwa kaiwa 'kirjin ta farmaki da bakin sa ne sai yaji tashin sallama daga 'kofar parlour wanda kafin ma yayi wani yun'kuri har an shi go ciki batare da an jira amsar sallamar ba.

Caka ya tsaya da abinda yake yi yayin da zuciyar sa ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, salati yake so yayi a zuciyar sa amma ya kasa tsaban ru'danin da ya shiga ganin tun a rana na farko da ya fara ta6a mace Allah ya kamashi.....

Bai 6ata lokacin sa wajen yin wani nazari ba ya fahimci muryar waye dan ba yau ya san amon muryar Hayatu ba a rayuwar sa.....yau gashi ga Hayat ga kuma Rahma sannan ga uban kunya da ta lulla6e shi.

Bai amsa sallamar ba kamar yanda bai ko motsa daga yanda yake ba sai ya bi jikin nata kawai da kallo sannan a hankali ya rintse idanun sa take ya sake bu'desu ya sau'ke su ajikin ta, batare da yayi kyakkyan motsi ba yaja mata shimin 'kasa ya maida shi yanda yake tun farko sannan cikin 'karfin hali yayi 'ko'karin bawa kansa 'karfin 'karfin gwiwa, take ya danne kunyar da ta kamashi ya juya ya kallo inda yake da tabbacin Hayat na tsaye.

Itama Rahma jin ya tsaya da abinda yake yi ne ya sanya ta bu'de idanu a hankali tana duban sa har a lokacin bata ji cewa ba dai-dai suke aikata wa ba haka kuma bata san da zuwan Hayat cikin parlourn ba.

Hayat da tun shigowar sa ya tsaya turus yana duban bayan sa da mamaki cuz bai gane waye bane kamar yanda bai san me yake yi agidan ba bayan ance Kaka bata nan, toh ma daga ina yake?"
Hayat sam bai yi tunanin tare yake da Rahma ba dayake koda ya shigo ma bai ganta ba dan Deen ya tare gaban sa juyawan da Deen yayi ne ya sanya shi bu'de baki cike da mamaki biyu zuwa uku yake nuna shi da yatsa, magana yake son yi amma ya kasa sai la66an sa dake cin karo kamar zasuyi dambe....a fili zaka fahimci meke shirin faruwa musamnan idan kayi duba da yanayin kusancin dake tsakanin su.

Mamakin sa bai wuce na ganin Mu'een cikin gidan kakar su ba, sannan kuma da ganin sa tare Rahma da kuma abinda yake shirin faruwa tsakanin su.....me kenan nake gani?
ya tambayi kansa cikin 'kin gaskata abinda idanun sa suka gane masa.

Da rawan jiki yake nuno Mu'een da already ya mi'ke tsaye yana gyara hannun longslip shirt 'din dake jikin sa cikin nuna halin ko in kula tamkar bai san me ya aikata ba...
" _MU'INUDDEEN_ !"
Hayat ya furta cikin ka'duwa.
Deen kuwa sai yayi murmushi gami da 'dage masa gira 'daya 'kasan ma'ko shi batare da ya bu'di baki ba ya amsa masa da " Ummn".

Hayat kallon sa yayi sannan ya juya ya kalli Rahma da tuni ta mi'ke zaune ta ha'de kai da gwiwa tana kuka a rikice da ganin sa.

Rintse ido Hayat yayi yana mai Addu'ar Allah yasa mafarki yake yi ba gaskiya ba ne.

Ganin hakan ya sanya Mu'een takawa zuwa gaban sa sai ji yayi an dafa kafa'dar sa tare da fa'din " ai bazaka farka daga baccin ba malam Hayat dan kuwa zahiri kake gani ba a mafarki ba".

Hayat na jin haka sai yayi saurin cukumo wuyan rigar Mu'een cike da 6acin rai yana jijjiga shi yace " me kayi mata Mu'een, mecece ala'kar ka da 'kanwata menene tsakanin ku?"
Hankalin kwance yace dashi
" Ka tambaye ta mana babban Yaya ai gata nan zaune ko"
Ko yun'kurin dakatar da Hayat bai yi balle yayi niyyan kare kansa sai ma wani murmushin sa na mugunta da ya aro ya sanyawa fuskar sa yake kuma cigaba da zubawa yana duban Hayatu.

Da 'karfi Hayat ya jijjiga shi da zararren idanu yace " tambayar ka nake yi ka bani amsa...me ya kawo ka gidan nan?"
ya fa'di a tsawace.
Chapter 44 · 0% Book details