← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 192 OF 211

Sashe 192

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar yinin kuka tayi domin ya fama mata tsohon ciwon ta, bata yadda ta sake kunna wayar ba har sai da ta tabbatar ta musanya layin ta da na 'kasar tukunna.
Dama tun farko itace taki amincewa ta canza amma tuni Anty Zainab ta canza nata ta fara amfani da na can.

Yah Deen kam komawa yayi ya jingina da kujerar dake kusa dashi yana jin kansa na sarawa da 'karfi..dafe kan yayi yana lumshe idanu lokacin da ya sake 'kira yaji wayar akashe...

Gudun kar Ammi ta fito ta tarar da shine ya sanya shi saurin 'dago wayar ya sake dubawa.

Kallon sakanni 'kalilan yayiwa numbern take ya haddace su.

Fita yayi daga wajen 'kiran ya ijiyewa Ammi wayar ta sannan ya tashi ya koma 6angaren sa.

Da shigan sa 'dakin sa ya nufivwayar sa, sunan Ishaq ya nema ya turawa numbern sannan ya 'kira shi daga baya ya bashi bayanin abinda zai yi masa.

Ishaq bai wani 6ata lokaci ba ya fito cikin gari ya nemi inda ake tracing number ya bada wanda Deen ya tura mai da tunanin ko ta waye oho dan bai masa dogon bayani ba shi dai ro'kon sa kawai yayi akan yabi masa diddigin layin ya ga location 'din da yake.

Kafin sau'kar rana kuwa Ishaq ya 'kira shi ya sanar da shi cewa ba'a 'kasannan ma ake amfani da layin ba.

Deen shiru yayi kawai ya rintse idanu, koka'dan bai yi tunanin cewa Noor nada ala'ka da Anty Zainab ba, illah ru'din da ya shiga na damuwar abinda ya fitar da ita wata 'kasa.

Ko daga baya ma bai yiwa Ishaq bayanin ba duk kuwa tambayar da yayi ta jera masa amma sai cewa yayi da shi bakomai.
Cikin lokacin har akayi bikin Imam amma bai samu ya je ba saboda damuwar da yake ciki.

Cigaba yayi da gwada 'kiran layin nata a koda wani lokaci amma cikin rashin sa'a a kullum baya samun ta.
Abin sosai yake 'daure masa kai, zuwa yanzun a fili ya fahimci cewa ba 'karamin tsana Noor tayi masa ba.

In har zata iya kashe wayar ta na tsawon lokaci ko kuma canza layin ta saboda shi ka'dai to kuwa yasan abin ya girmama sosai.

Sai dai hakan ba dame shi sosai ba fiye da rashin sanin takamamme me ya fitar da ita waje da be yi ba..kenan tunda auren sa akanta tayi tafiyar ko kuwa? me ma ya kaita wajen 'kasar nan sam ya kasa haskowa.

Bai sake yiwa kowa maganar ba kawai ya bari cikin zuciyar sa akullum kuma baya gajiya da sake gwada 'kiran sabuwar layin nata da ya samu hoping that zai same ta watarana, bai sani ba ashe ta canza wani layin.

Safwan ma har Shuwarin yazo ya duba shi ya kuma tausaya masa matu'ka, ace mutum kamar Mu'een amma kullum zaune cikin gida sai kwanciya sai zama a 'daki duk rayuwa ta canza shi ya koma wani abu daban kamar bashi ba.

Da kansa yaje ya sake bawa su Ammi ha'kuri domin ya fahimci ayanzun damuwar Mu'een abu 'dayane kawai, amma sai suka nuna masa cewa su babu ruwan su indai akan Noor ne, tana da 'yan cinta a yanzu babu wanda zai takura ta, ko ada in ma ita da kanta ta nemi rabuwa da shi indai hakane kuwa su basu da dalilin takura ta dole ta zauna da shi, tawakkali kawai zai yi ya koma rayuwar sa ya daidaita ta, in yayi sa'a yayi dacen samun wata matar kuma shikenan su basu da matsala da shi.

Safwan bai yi mamaki ba domin kuwa yasan _sakayyar Allah_ idan ta tashi fa'dawa kanka fiye da hakan ma zaka iya gani.

Shawara ya bashi akan ya daure ya koma bakin aikin sa zai fi samun natsuwa wala Allah ma damuwar ta sa ta 'dan ragu.

Baya son wata damuwa balle batun wani aiki a yanzu, shi aganin sa wa zai yiwa aikin yanzun, wa zai nemawa farin cikin rayuwa tunda bashi da kowa, babu Jasmine babu Noor aikin me ze yi kuma.. amma ta wani 6angaren kuma da kansa sai yaga dacewan komawa aikin cus zama gu 'dayan nan sosai yake illata shi...da kansa ya fara jin babu da'di, koda wani lokaci inba tunani ba baya aikin komai.

Gashi da alamu ciwon sa na son motsa shi a 'yan kwanakin, 'kirjin sa na yawan yi masa zafi da nawi..ga wani masifaffen ciwon kai dake yawan addaban sa ko motsin kirki wani sa'in be isa yayi ba.

Haka suka rabu da Safwan da al'kawarin zai yi tunani akan batun tukunna.

Be gama yanke shawarar bane har su Saif suka zo gida.

*****
Tun dawowar su Saif sai abin 'dan uwan sa ya dame sa sosai, sai yaje ya samu Ammi kan batun domin shi harga Allah tausayin sa yake ji matu'ka, mutum tun safe idan ka ganshi waje to gaida su Ammi ya fito yi bayan haka kuma bazaka sake ganin sa ba, ko abinci ma 'dakin nasa aka koma kaima masa wanda shima 'din sau tari yanda aka shigar haka ake fitar da shi.

Ammi yaje ya samu da maganar tace to ni ya zan yi da shi Saif? Shi fa ya saka kansa duk abinda kaga ya same shi ba wanine ya sashi ba.
" Duk da hakan Ammi ya kamata ai zuwan yanzun a tausaya masa..kuyi ha'kuri Ammi ku duba lamarin nan..kuma cikin wannan yanayin bai kamata ace itama Noor tayi nisa da shi ba, na rasa ma me yake damun ta yanzu duk ta canza wallahi....tausayin ta yayi 'karanci..na tabbata damuwar sa harda ta guje masa da tayi a ciki...mtheww".
Ya 'karashe da jan tsaki cike da jin haushi.

" Kai de kasa ni, kai kaga me 'dan uwa ko?
Ni dai abar min yarinya ta huta yanzu dan babu wani ala'ka tsakanin ta da shi, da jimawa ya rubuta mata takadda..".
" Takddar me kuma Ammi?"
Yayi saurin tare da tambaya tun kafin ta 'karasa.
Sai ta bashi amsa da fa'din
" Saki mana...he divorced her tun ba yau ba yanzu haka ma karatu take yi abinta...gaka ba wada ala'ka yanzu".
Wani banbara'kwai yaji abin har ma bai san lokacin da ya mi'ke tsaye ba ransa a matu'kar 6ace yace" haba Ammi..me yasa zaki jagoranci abinda kinsn illah zai yiwa 6angare 'daya, na tabbata bakomai ke barazana ga rayuwar Yayah ba illah rashin matar sa kusa da shi, Ammi koma wace iriyar nadama ake bu'kata ai duba 'daya zaki masa kisan itace tare da shi, me yasa kuma za'a raba shi da matar sa bacin kunsan yana son ta har zuciyar sa Ammi..harga Allah ni ban ji da'din hakan ba".

Ammi kawar da kanta tayi gefe bata ce da shi komai ba.
Zai sake magana tayi saurin dakatar da shi da fa'din" Wai Saif so kake ka nuna min kai me 'kaunar 'dan uwan ka ne ko me? har zaka zo kaina ka tsaya nagging at me for what?...uban ka ne shi? Ko kuwa da shawarar ka yayi rayuwar sa?"

Sau'kar da murya Saif yayi jin ranta ya fara 6aci yace" ba haka bane Ammi...ki tausaya masa please..ki duba... "
Waje tayi saurin nuna masa fuskar ta a sha'ke.
Yi yayi jamar be fahimta ba zai sake magana ta daka masa tsawan" Kayi min waje".
Da yaren su tayi maganar cikin tsananin 6acin rai.

Saif kai ya girgiza kawai yayi waje...zuciyar sa babu da'di.
Abin sosai ya tsaya masa arai..gani yake kamar ba ayiwa 'dan uwan sa adalci ba.

*****
'Bangaren Jiddah kuwa hankalin ta sosai ya tashi da wannan shariyar da Mu'een yayi da ita tsawon watanni, tun da jimawa tayi dana sanin abinda ta aikata domin aganin ta dalilin kenan.

Gashi yanzu yana ganin 'kiran ta amma baya 'dagawa, whatsapp ma ko tayi masa magana baya dubawa, taje asbitin da yake aiki yafi sau goma amma duk babu labarin sa.

Gidan su kuwa dake Abujan kusan kullum sai taje amman duk matsalar iri 'daya, dan ko alamun an ta6a rayuwa a wurin ma bata gani kullum gidan datse yake da padlock babba, abin na 'daure mata kai sosai.

Tun tana damuwar ita ka'dai a 'daki har ta fara bayyanawa, kowa dake gidan su sai da yasan abinda ke damun ta, tana son Mu'een ra yadda take tunanin bazata ta6a iya rayuwa babu shi ba.

Abban ta kam shi yafi kowa shiga tashin hankali sam ya rasa ta ina zai fara, gashi gunsa tafi zuwa tayi masa kuka ganin cewa bashi da niyyan cika mata al'kawarin da ya 'daukam mata kwanaki, sam bataga alamun zai cika mata burin ta ba.

Mummyn ta ma bata barin sa, domin hankalin ta tashi yake a duk lokacin da ci karo da tilon 'yar ta a gaban ta tana kuka kan wani dalili wai shi soyayya, tasan mahaifin ta nada ku'din da ko a wata 'kasar ne zai iya siya mata soyayya da ku'din sa in bu'katar hakan ta taso, me yasa yanzun kuma da abin ma yake kusa da shi zai yi watsi da ita.

Shi kam har ga Allah abin ya masa wani iri ne, bai kamata ace shi mai 'ya mace shi zai kai batun auren 'yar sa gidan maza ba amma yanda Jiddahn ta matsa dole ya sanyawa zuciyar sa amincewa.

Da kansa ya sanya rana shi da P.A 'din sa sai kuma drivern sa suka tafi, dan a ganin sa wannan abin kamar sirri ne, bai kamata wasu suji labari ba hakan yasa bai gayyaci kowa ba..saboda gudun zubewar mutuncin sa, ace mutum kamar shi amma yake nemawa 'yar sa soyayya matsayin ta na 'ya mace mutum mai daraja cikin al'umma

Tun kafin ya tafi ya sa ta tura masa pic 'din gayen da numbern sa in case ko bai same shi a waya ba sai su nuna pic in tunda 'karamin gari ne babu mamaki asan shi ko baya garin zaiyi magana da iyayen sa inyaso kawai su san matsaya.

Tun a hanya ya fara gwada 'kiran sa domin yaji ko yana ina.
Chapter 192 · 0% Book details