← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 211

Sashe 58

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
Ni kuwa rayuwa ta wurin Ammi sai godiyan Allah, domin Ammi bata nemi akawo min ko kayana ba dan bata so in tmringa yawan tunawa da gidan, tayi tunanin ko duk kayan mu iri 'daya ne da marigayiyan tsoron ta kar inzo yin amfani dasu kuma in dinga cigaba da tunawa shiyasa ma bata nemi abata ba.

Washegarin zuwa na Ammi ta bayar da 'dinki cikin ajiyayyun zannuwan da take dasu aka ciccire min rabi rabi kusan kala biyar ta bayar aka 'dinka min.

Ammi ta kula dani sosai, ta kula da rayuwata da tarbiyyata tamkar ita ta haife ni, Ammi bata ta6a barina in zauna shiru, da dare ita kanta take min wanka ta sani in kwanta kan tsakiyar gadon 'dakin ta sani inyi addu'ah sannan tayi ta karanta min story har inyi bacci sannan sai ta koma other room.

Da safe ita zata tadani inyi sallah da wanka sannan ta bamu abincin breakfast ni da su Saif bayan munci sai mu wuce makaranta, idan mun dawo bana yi mata aikin komai haka zata sani kallon cartoon a T.v har lokacin sallah tayi daga nan idan nayi sallah sai kuma mu shirya mu wuce islamiya.

  Ranar da babu islamiya kuwa...ta ware min lokacin da ya dace nayi baccin rana ragowar lokutan ma duk bata barina in zauna haka kurun Ammi occupied them da abubuwan 'dauke hankali.

Musamman ta sa aka siyo min game dan in ringa yi lokacin da babu wutan Nepa...gidan mu kuwa sai dana yi sati hu'du cif ban le'ka ba....ko nace zanje sai tace bani da lafiya in bari sai na samu sau'ki tukun.

Shagwa6ewa nakeyi ince " Ammi nifa lafiya ta 'kalau".
" Ke de ki bari when u recover da kaina zan kaiki".
Ban sani ba ashe Ammi in taso zuwa gidan namu sulalewa take yi tatafi abinta lokacin da ta tabbatar ina tare da dasu Saif muna game, wani sa'in har zataje ta dawo ma bansani ba.

Ummah ta tun tana saka ran dawowata har ta ha'kura gashi Ammi bata ta6a ce mata ga ranar da zan dawo ba haka kuma bata sanar da ita son zama da ni take yi ba.

Dalilina Ammi ta nemi 'yar aiki saboda ta ringa samun isasshen lokacin da zata zauna dani agidan, in kuwa kitchen zata shiga tare muke zuwa Ammi bata barina idan tana girki kuma bata gajiya da nuna min idan anyi kaza anyi kaza kaza zai zama..ta kan gaya min...idan muna kitchen.

Alhaji Baba ma ta 6angaren sa abin sai Alhamdulillahi domin tamkar mahaifi haka ya 'dauke ni, lokaci 'kan'kani na dawo 'yar gatan gidan gaba 'daya, har 'yar ramata ta 6oye.

Sha'kuwata da 'yan biyun Ammi kuwa sai abinda yayi gaba musamman ma Saif, dan shi tare muke cin abinci cikin plate 'daya da shi...idan wasa zamuyi ma team 'din mu 'daya dashi...sai dai duk da haka Ammi bata ta6a bari na in shiga 'dakin su haka kawai sai dai in da wani dalili.

   Zakiyi mamaki Hafsat yanda kwata-kwata na manta da duk damuwa ta ta baya har mantawa nakeyi da cewa ni ba 'yar gidan ba ce....natsuwa ce ta shige ni ta ban mamaki, yanzu sam na daina rashin ji kamar bani ba...dan ko a gidan idan Zaid ya min mugun ta ban kula shi haka kuma ban kai 'karar sa.

Ranar da muka fita gidan mu tare da Ammi kuwa...karki ga farin cikin da Ummah ta tayi da gani na...." Alhamdulilah kawai take fa'di cikin ranta...a fili kuwa godiya tai ta zubawa Ammi.
Har muka bar gidan ha'koran Ummah na basu daina bayyana kansu a fili ba cike da fara'a.

*****
Alhaji Baba kam damuwar sa kullum Yah Deen ce dan har yau bai iya ya sanar da shi halin da ake ciki ba, ko ya tambaye shi amanar sa kuwa sai dai yace masa " Allah zai yi maka jagora Mu'een....."
Fargabar yanda Mu'een zai kar6i lamarin yake yi, kullum tunanin bai wuce hakan.

Da abin ya dame shi ne sai lokacin ya sanar da Ammi komai da suka yi da Mu'een kafin tafiyar sa, itama Ammi tayi mamaki sosai amma tasan koma miye ne dole idan yaji ai zai ha'kura tunda bamu ke da mutuwar ba, Allah ne ka'dai mafi sani akan hakan.

〰〰〰
*BAYAN WATA UKU DA RASUWAR NANNE.*
      Sai lokacin Yah Deen yazo gida cike da murnar zaiga ahalin sa da sahibar sa, ga kuma 'dumbin farin cikin da ya cika shi na samun gurbin karatu a FEDERAL UNIVERSITY DUTSE.... course 'din da yafi k'auna a rayuwar sa wato Pharmacy.....yana kammala wannan programme 'din da yake yi zai tattara ya koma jigawa dan cika burin sa.

👇🏼
*Toh fah readers ina son jin ra'ayoyin ku game da dawowar* *_MU'INUDDEEN......._*
*Sai naga ruwan comments sannan zan cigaba da typing, sa6anin hakan kuma ina jin sai kun jini nan da 1 week ko kuma 29 january idan muna cikin rayayyu.....dan harga Allah na raina comments 'din ku*

*Labarin dai har yanzu da saura....amma in akayi ha'kurin bina duk zamu ji koma menene....sannan dan girman Rabbi👏🏻 ku ringa sharing ni 'din abubuwa kan min yawa ne shiyasa*

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Ina son ku masoyana_ 😍 _...Allah ubangiji ya haskaka rayuwar ku da mafi alkhairi daga cikin alkhairai_ 👏🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *30*

........'Bangaren Alhaji Baba kuwa...a yau 'din duk ya kasa sukuni, damuwar sa ta yawaita sosa...tunanin sa ta yanda Mu'een zai kar6i zancen ne, tun ranar da Yah Deen ya bashi amanar ta ya fahimci tsantsan son da yake yi mata cikin idanun sa da kalaman sa ya fahimci hakan, babban abinda yasa ya 'kara gaskata soyayyar tasa ma shine da har Yah Deen ya iya manta dangantakar da ke tsakanin su matsayin sa na mahaifi agare shi, ya iya duban tsaban idanun sa ya ha'da shi da amanar kula masa da ita, ha'ki'ka hakan ka'dai ya wadaci koma waye fahimtar tsantsan son da Mu'een ke wa marigayiya AMINA...musamman idan kasan halin sa cewa bashi da rashin kunya sam a rayuwar sa.

      Alhaji Baba lambun sa ya tafi yaje ya ke6e kansa guri guda yana tunani, sai dai daga 'karshe dole ya watsar da batun ya cigaba da harkokin sa.

        Shigan yamma Mu'een yayi dan kuwa 'karfe biyar da 'yan mintina ya shigo garin...fuskar sa cike fal da fara'a tamkar bashi ba, ya 'kara kyau da girma, dama gashi dogo ne shi ba laifi sai gaba 'daya ya juya ya koma tamkar 'dan shekara talatin da haihuwa.

   Ni kaina lokacin da na gansa tsaye a 'kofar shigowa parlourn bangane shi ba, saboda kwaftareren ba'kin gilashin dake manne a idon sa, shima kuma bai yi min magana ba tunda yayi sallama ya dire jakar sa a wurin sai ya yaja ya tsaya yayi shiru.

" saif!...Saif!!...Zaidu!!!"
Na fa'da da 'karfi cike da firgici ina 'dan jan baya dan harga Allah tsoro ya bani, ban kuma kawo akaina shi bane saboda nasan shi baya murmushi haka siddan sai da dalili 'kwak'kwara.

Ammi da Saif duk lokaci guda suka bayyana suna tambaya ta saboda jin 'karan 'kiran sunayen da nayi kuma nayi da 'karfi, sannan da tsoro nayi.
" Wai me ya faru ne?"
Saif yace yana kallo na, yayin da Ammi ta ce dani " Hudah Lafiya kike faman ihu?"

Ban bawa kowa cikin su amsa ba illa hanyar 'kofa da na nuna musu da hannu na wanda sai a lokacin suka lura da shi.
    Still yana nan tsaye with smile on his face yake duban mu da karkataccen wuya.

Saif murmushi yayi yayin da Ammi tace da shi " 'kaniyar ka Muhammad!"

Cikin marairaita yace " haba Ammi daga isowa ta ?"

" me yasa zaka yi tsaye acan to har kana firgita min yarinya?"
Murmushin sa ya 'kara fa'da'dawa sannan yace " Ni fa Ammi ke kawai nake jira ki taroni".

Ido Ammi ta 'dan zaro tare da fa'din " daga zuwan na ka zaka fara ko?"

Ganin bata da niyyan zuwa ne ya sanya shi tahowa inda take yana kwa6a fuska.

Ni kam da kallo kawai nake bin sa ina mamakin sa ayau 'din gaba 'daya ya canza min.

Saif ne ya girgiza kansa shima cike da jin dadin ganin 'dan uwan sa tare da wucewa inda jakar sa take ya 'dauka ya wuce da shi cikin 'dakin sa.

Ammi kuwa hannun sa ta kama kamar 'dan goye ta jashi zuwa kan kujera mai zaman mutun biyu ta zaunar da shi kan kujera....da yaran su na Igbo tace da shi " Sakalcin yau ya motsa kenan?...baka ganin 'kannen ka na kallon ka ne?"

Kai ya 'dan sosa gami da satan kallon 'bangaren da nake tsaye...dai-dai fitowar Saif sai ya maida kallon sa gare shi.

   Suna ha'da idanu sai yace " Yayah Welcome...hope an iso lafiya?"
Da " Alhamdulillah" ya amsa shi daga haka ya ja ya kishingi'da gami da sakin numfashi.

Ammi ya kalla yace da ita " barka da gida Ammi".

" Yauwa...ya su Auntyn ka?"
" Lafiyan su"
" karatun fa?"
" Shima normal Ammi saura na tafiya Jigawa yanzu".
" To Allah ya taimaka ya bada sa'a".

'Kasa-'kasa ya amsa mata da " Amin Ammi na".

Ni kam har lokacin ina tsaye a inda nake sai ma raku6uwa da nayi jikin labile ina kallon su.
   Ammi ce tace dani " 'karaso mana kika wani tsaya acan, koma gaida yayan ki baki yi ba".
Da jin haka sai nayi saurin tahowa kusa da ita kamar dama jira nake a kira ni na zauna nima a hankali cikin sanyin jiki " wai har kin manta waye shi ne?"
Ammi ta sake tambaya ta.
Sai na girgiza mata kai alamar "a a"
Sai tace" to oya..."
ta karasa maganar da nuna min shi da kanta.
Sai da na 'dago na kalle shi kafin nace " Ina yini".
Bai amsa ba sai kawai ya 'dago idanun sa ya kalle ni sannan naga ya kalli yanayin yanda na ra6u da jikin Ammi.

Kai ya 'daga ya maida kallon sa ga Ammi gami da 'dage gira 'daya.
Chapter 58 · 0% Book details