Sashe 157
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin lokaci 'kan'kani kuwa na koya dan ban wani sha wahala wajen fahimtar komai ba, hutun 3weeks yayi sannan ya koma bakin aikin sa, kafin hakan kuwa sai da ya tabbatar ya nemawa Jasmine Special Nanny wacce ke kula da ita a makarantar ita ka'dai yana biyan ta.
Da sun yi break kuwa zata 'kira shi suyi hira da baby yaji muryan ta yayi ta jan ta da hira har sai yaji tana dariya kafin yake hanging 'kiran, aikin ta kenan kulawa da Jamsine har a tashi a school sannan ta wuce bayan ta sada ta da wanda yazo 'daukan ta.
A lokacin kuwa asbiti har biyu Yah Deen ke aiki da su abin sai ya zame masa ba hutu sam, wani sa'in har tausaya masa nake yi, dan duk yadda ya so ya ringa samun isashshen lokaci yana zama da iyalin sa hakan ya kasa samuwa, Baby kanta sosai take damuwa da rashin sa kusa dan ta sha'ku da shi ba laifi...motsin ta ka'dan zakiji ta ambaci sunan sa, ko wasa ta ke yi" Daddy ta fiye ambato.
Da farko shi ya cigaba da sau'ke Baby a school amma daga baya da abubuwa suka yi masa yawa sai na nemi ya bar Baby Jas in rin ka kaita makarantar amma ya'ki amincewa sam.
Da 'kyar na samu ya amince ya bani ragamar kaita makarantar da 'dayan motar sa wanda sanadin hakan yasa ya 'dan samu natsuwa ya rage fita sassafe, yakan yi shirin sa cikin tsanaki ya gama komin sa a nutse sannan ya fita office.
Banfi 2months da fara jigilar makarantar Baby ba nima na fara tawa makarantar.
Lokacin fitar mu da Baby ba 'daya ba haka ma lokacin tashin mu amma duk da haka sosai nake 'ko'kartawa wajen ganin kowa ya isa tasa makarantar akan lokaci.
*****
Bazan manta ba ranar wata talata Yah Deen yazo min da batun wai ya ha'du da wani matashi dake son yin aiki kuma wai ya iya tu'ki ba laifi, yace sunyi magana da shi kuma ya fahimci yaron na da natsuwa dan haka zai ringa sau'ke ni da Baby a school yana 'dauko ta in yaso nima idan na futa a lectures sai ya koma ya 'dauko ni cuz shi har yanzu ransa bai kwanta da nawa tu'kin ba.
Wallahi tun lokacin ban ji da'din 6ulluwar yaron nan ba, haka sam banji batun Yah Deen in ya kwanta min arai ba haka kawai sai na tsinci kaina cikin rashin natsuwa.
Sai ma na tsaya da mamaki ina duban sa, domin da bakin sa ya furta wannan maganar kamar yanda ya ta6a furta min garga'di abaya akan shiga mota da wani, baki na ta6e cikin raina nake ayyana ina kuma kishin ya tafi oho? Ko da yake yace ya yaba da natsuwar yaron 'kila shiyasa ma bai damu 'din ba.
" Baki ce komai ba" Ya sake fa'di yana duba na.
Kaina na kawar gefe sannan nace" Toh ni Yayah me zance?"
" Akwai mana ai naga kamar ranki bai so hakan ba".
" A a ba haka bane kawai nayi mamaki ne...dan Allah Yah Deen yanzu miye abin sai ka 'dauki driver bacin ba shiga hakkin karatun kowa cikin mu akayi ba..".
" Shi ai namiji ne Nuree kuma sosai na yaba da hankalin sa, nima 'din zanfi samun natsuwa idan ya kasance na 'dora wani a bayan ku in ba haka ina office amma kullum hankali na a rarrabe, tunanin halin da kuke ciki nake koda yaushe tunda nasan ba wai sosai kike 'kware a tu'kin ba".
" Ni dai please a barshi Yaya, ka nema masa wani aikin".
" Haba Nuree..zaki fara ko?"
Yayi maganar yana janyo ni jikin sa.
'Dan 6ata rai nayi nace" ni bana san damuwa ne kawai Yayah..."
Bai bari na idasa maganar ba ya rufe min baki da nashi wanda hakan ya tilasta min yin shirun dole.
Duk da hakan daga baya sai da na so nuna masa 'kin amincewa ta dan sam lamarin bai min ba har cikin raina amma ya dakatar da ni ta hanyar fa'da min cewa" Hakan zai fi mana gaba 'daya saboda babu wanda zai shiga hakkin wani...ya kuma ce dan Allah baya son musu...taurin kanki kullum 'kara hauhawa yake yi Nuree".
Ya 'karasa maganar da 'dan alamun 6acin rai akan fuskar sa.
Dole na watsar da zancen musamman ma saboda yanda naga Yah Deen ya fara 6ata ransa kan batun yasa kawai na zuba idanu na ba wai dan raina ya so ba.
Haka driver mai suna Sani ya fara aikin sa wanda cikin gidan yake kwana tare da maigadi.
Idan ya fara sau'ke Baby nima sai ya ajiye ni a tawa makarantar, tun farkon zuwan sa maganar kirki bata ha'da ni da shi, daga gaisuwa shikenan musamman ma da na lura yaron surutacce ne hakan yasa na ke kama kaina dan kar ya samu fuskan cika ni da surutu.
A bakin Nannyn Jasmine yake jin wasu labarin rigimar da take yi farkon sata makarantar da yake idan yaje 'dauko Baby sukan 'dan yi hira da Nannyn dan Sani gwani ne ko baka yi ra'ayin magana ba sai ya saka yin magana na kan fahimci hakan ne idan suna tare da Yah Deen.
Kuma ma da yake watarana Nannyn ma shi ke sau'ke ta idan sun tashi, aikin ta kuma dama a iya school ne kawai da zarar su Baby sun tashi shikenan aikin ta ya 'kare sai kuma gobe...idan kinga su da Sani suna sururtu har zakiyi mamaki, za ma ki zaci cewa sun shekara biyar tare da yake duk irin su 'daya ne surutattu ne na masifa...ni kuwa a rayuwa ta na tsani mutun mai yawan magana.
Ai kuwa tunda Sani yaji labarin rigimar Baby a abkin Nanny shikenan sai yake yawan tsokanar ta akan hakan, yakan ce da ita cry-cry mai kukan Daddy...idan yaga ta 6ata ranta tana fushi sa kiga yana ta yi mata dariya yana sake maimaitawa while ita kuma tana tura baki tayi tamkar zata yi kuka, da yake yanzu ba laifi ta saba sosai da makarantar ta kuma saki jikin ta so sam bata so ace mata mai kuka a school.
A kullum idan ta dawo sai ta min 'karar Sani wai yana yi mata dariya wai tana kuka sai tace min kuma Mummy ai yanzu na daina"
Haka take ce min tana nuna alamun rashin jin da'din ta afili.
Tun ina bata lalla6a ta akan maganar har nazo na gaji na daina kula ta sai ta koma gayawa Daddyn ta wanda shima akwai ranar ta dawo yana gida ne yana ganin ta sai yayai turus yace" Maman Daddy ya da fushi haka?"
Sai ta nufe tana dama fuska tace" Ai Sani ne yake ce min wai cry-cry kuma fa Daddy yanzu bana kukan".
Dariya sosai ta bashi amma ya danne yana cire mata uniform yake ce mata rabu da Sani zane shi zanyi shima yayi kukan sai kiyi masa dariyar kema ko?"
Hakan da ya fa'da mata ne ya sata jin da''di shiyasa ta maida kaiwa 'karar wurin sa, a duk ranar da Sani ya takale ta to Yah Deen take sanar ma wa.
Shi ma da 'marar ta ishe shi ranar yana dariya ya 'kira Sani yace masa" Sani gaskiya kana takurawa Mama na da yawa, kai baka ganin yanzun ta girma ne? kuma ai ma bata kukan yanzu ko?"
Ya 'karasa yana duban ta
Saurin 'dage kanta tayi tana ta6o kunnen ta, sai yace" Sani to ka kiyaye ni...idan baka daina ba kaima zane ka zanyi kayi kuka Mama na ta rama dariyar ta..."
Sani na jin haka ya bushe da dariya dan yasan Deen wasa yake yi masa dan ya kwantar da hankalin Jasmine, yana cikin dariyar yake fa'din" Hajiya maman Daddy wato 'karata aka yi?"
" Ni dai na gaya maka".
Yah Deen ya fa'di tare da hanging call in.
Lalla6a ta yayi har ta saki ranta da taji cewa anjima zasu je yawo.
Daga lokacin kuwa sai Sani ya 'dan rage tsokanar ta 'din a hankali ma sai yazo ya daina gaba 'daya sai jifa-jifa.
A cikin wannan lokacin aka haifi Afrah, wanda tun zuwan gidan na farko da muka dawo Baby ta fara yi min rigimar ita ma wai asiyo mata Baby..Yah Deen kam dariyar ya ringa yi duk dama shi kansa yana so yaga ya tara iyali amma shiru har yau babu komai, babu abinda na sha ko muka yi amfani da shi amma tun haihuwar Jasmine har yau ban 'kara ko 6atan wata ba.
Lalla6a ta ya ringa yi yana taro mata Babys in wasa kala-kala sannan ta huce.
Ranar da shima zai je gidan Safwan in kuwa dukkan mu muka je har da ni muka gaishe su sannan muka dawo.
Kamar wasa sai abin ya fara damun sa, duk dama ya san ba yin kan mu bane amma shekara hu'du ya kamata ace ya sake ajiye wani Babyn.
Kwance muke hannayen sa dabaibaye cikin jiki na, yayin da ya kwantar da kansa bayan wuya na yana sau'ke min numfashin sa a hankali ya 'kira suna na ban amsa ba amma da yake yasan na jishi kawai sai ya cigaba da maganar sa" Nuree yaushe zan sake samun wani Babyn ne, ina son inga na tara yara da yawa".
Hannun sa ya 'daura saman hanci na yana ja a hankali tare da dawo da bakin sa saitin kunne na sannan ya cigaba da fa'din" Ina so in haifi mai irin hancin ki Nuree, da mai irin wannan bakin..."
Murmushi nayi masa dan sosai nake jin wani shock a jiki na ga kuma yanayin maganar tasa har cikin zuciya ta take ratsawa.
Jin bance komai ba sai yayi saurin birkito ni ya koma saman jiki na..." fuskar sa ya kai dai-dai da tawa ni kam tuni na lumshe idanu na ina sakin murmushin jin da'di.
A hankali ya kai bakin sa saman la66a na ya sumbace ni sannan ya 'daga kansa" Baki bani amsa ba Nuree..na ga alama ke babu ruwan ki ko..ni kam na koma bayan Baby..."