← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 211

Sashe 24

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Noor kuwa 'kan'kance idanu tayi tace da Safwan
" Miji na kace Yah Safwan?, kuma kace na sassauta masa?
Haka kace da gaske.....?
Gashi nan ka tambaye shi Yah Safwan na san ya sani.......a yau 'din nan kafin yazo me budurwar sa ta turo min....Yah Safwan ga shi ka tambaye shi".

Ta fa'da tare da kamo hannun Deen amma ko motsi bai yi ba daga inda yake tsayen.

Dawo da kallon ta tayi gare shi tace " wallahi tunda nake Yah Deen ban ta6a dana sanin kasancewa da kai ba irin ta yau kuma hakkin 'yata sai ya biku bazai ta6a barin ku ba.......mazinatan banza kawai".
Tana gama fa'din hakan ta wuce wurin Jas da tun 'dazun take faman kuka a kwancen da take.

Deen bai iya cewa da ita komai ba, illah binta da idanu da yake 'karayi, shi ka'dai ya san me yake ji zuciya da gangan jikin sa.

Shi kansa Safwan jikin sa yayi sanyi sosai, har ma bai san lokacin da Deen ya bar 'dakin ba.

Komawa yayi gurin Noor yana bata baki akan tayi ha'kuri amma ko sauraran sa batayi sai surutu take yiwa Jas tana kuka tamkar ta zauce bata hankalin ta, ganin hakan ne yasa shi niyyar barin office 'din domin bata lokaci ta 'dan nutsu.

Juyawan da yayi ne yaga Deen baya 'dakin sai dai taku uku mai kyau bai yi ba yaji muryar Noor na fa'din " Yah Safwan yaushe za'a sallami Jasmine?"
Inda tayi maganar ba tare da ta waigo ta kalle shi ba.

Shi 'din ne dai ya sake waigowa gami da bata amsar " sai nan da sati 'daya idan ta warke"

" ba gaskiya ka fa'da ba Yah Safwan?"
Ta sake fa'di cikin dakiya sannan ta tashi ta juyo ta fuskance shi " ka gaya min gaskiya dan Allah, ina so ne inje in kula da tarbiyar yarinya ta guri guda in da bazata ha'da ala'ka da duk wani munafuki ba bana son zaman asbitin nan bani son zaman Baby anan".

Safwan kam zuwa yanzun mamakin ta ma yake yi yanda duk ta juye masa zuwa wata abu daban tamkar zakanya, har ji yake kamar wannan ba Nureen Deen ba ce, yarinya mai matu'kar sanyin hali, ha'kuri, kunya da kawaici ga girmama duk wani wanda ya girme ta, sa6anin wannnan da take kallon cikin idanun mijin ta take zagin shi, ta dubi tsabar idon mutun ta 'karya tashi.

Cikin rawar murya ya bata amsa da fa'din " ki bari dai sai ta warware....first idan ma zaki..tafi da itan ".

Noor bata sake tanka shi ba sai ta koma ga Jasmine ta kwanta gefen ta tare da kwantar da kai gefen ta tana shafa cikin ta tace "Allah zai saka miki Mamana, baki da hakkin kowa akanki kuma da iznin Allah duk wanda ya cutar da ke sai Allah ya saka miki...zai bi miki ha'k'kin ki".

Safwan jijjiga kai yayi kawai sai ya sa kai ya fice daga 'dakin.

*****
'Bangaren Sani kuwa.........

Comment
Vote
Share

*Salmerh ce*😍

[11/30/2019, 10:34 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *13*

'Bangaren Sani kuwa.....tunda aka kawo shi asbitin bai farka ba iya tsawon zaman sa bai san meke faruwa da shi ba sai yanzun da yake dai-dai da 'karfe hu'du da mintina hamsin da uku na yammacin ranar.

'Kafafun sa ne suka fara motsawa a hankali kana ya bu'de idanun sa da yake jin sun matu'kar yi masa nauyi saboda buguwan da kansa yayi.

Kasa-kasa bu'de idanun nasa yayi saboda wani suka da yake jin kansa nayi masa ga jikinsa ko'ina yayi masa nawi, takamamme ba zai ga inda ke yi masa ciwo ba.

Allah ma yasa dai-dai lokacin farkawar ta shi likita mai kula dashi yana nan cikin ward 'din wato Dr. Felix.
Matsowa yayi cikin saurin sa zuwa gaban gadon da Sani yake kai 'din ganin ya 'dan motsi da 'kafafuwan sa, wanda ganin hakan ne ya tabbatar masa da cewar ya farka.

Jin motsi kusa da shine yasa shi 'karfin halin bu'de idanu da 'kyar, bama ya gani sosai dishi-dishi yake gani, amma a hankali da ya cigaba da 'kif-'kif da idanun sai suka 'dan washe ya fara gani da kyau.
Bai wani sha wahalar gano inda yake ba a halin yanzun, musamman da yake yaga likita akansa cikin kayan aikin sa na likitoci.

Idanun sa ya mayar ya rufe su sai tar hawaye ya gangaro ta gefe da gefen idanun nasa, yana so ya 'dan jijjiga kansa amma ya kasa, yayi 'ko'karin 'daga hannun sa da yaji yayi nawi sosai amma hakan ma ya gagare shi, banda ciwon da ga6o6in sa ke masa baya jin komai.

'Ko'karin tuno sanadin faruwar hakan yayi inda ya fara tunani tun daga farko, lokacin da ya 'dauko Jasmine daga makaranta, feelings 'din da ya kama shi sanadin kallon abinda bai dace ba cikin wayar sa, amfani da yayi da sanyin da tace tanaji, kissing, har zuwa fingering nata da yayi and most of all yun'kurin kusan ta kansa da ita da yayi wanda bai kai ga aikatawa ba yayi musu sanadin accident saboda firigici da ya kamashi.

Hawaye yake sau'karwa masu matu'kar zafi da ciwo a zuci, tambayar kansa yake yi shin anya shine kuwa, Jasmine fa, da 'din kenan kusantar ta zanyi ko me?
Sani da hankalin ka kuwa?
Anya kaine Muhammad Sani na da 'din nan?
me ya ru'deni har haka?
Me ma zan samu a jikin ta?
Ashe kissing 'din ta da da nake yi ma bai isheni sanin haukar da nakeyi ba?
Yanzu yarinyar Oga Deeni nayi wa haka?
Waiyo Allah na.....wallahi shai'dan ka cuce ni, baka min adalci ba,
yanzu fisabilillahi wani kallo Oga Deeni zai yi min...?
Nasan ba zai ta6a yafemin ba...."

Dr. Felix kam bai bi ta kan hawayen da yaga Sani keyi ba, dan zaton sa duk akan zafin ciwo ne, dan haka kawai sai yaci gaba da aikin sa inda ya 'kara duba lafiyar sa da sauran wasu abubuwa, tambayan sa Dr. Felix yayi kan cewa baya ga ciwukan sa na zahiri akwai inda ke yi masa ciwo ne?

Sani ko kulasa ma bai yi ba yaci gaba da kukan sa yana tariyo ta'asar da ya aikata cike da tarin nadama.

*****
Tunda ya baro 'dakin da aka kwantar da Jasmine yake tafiya tamkar mutun mutumi, tunani yake cikin ransa wai dagaske Babyn sa aka lalatawa rayuwa, dagaske ne Sani ya lalata masa rayuwar 'yar sa?, da gaske ne kamar yanda Nuree ta fa'da wannan abin ya faru ne sanadin halin sa?
Kai ah ah me ze sa hakan to?
Abu 'daya ne yafi tsaya masa a rai shine lalata masa 'ya da Sani yayi.

Sam Deen bai san inda yake jefa 'kafafun sa ba, bai san inda yake nufa ba balle yasan wa'danda ke wuce wa ta gefen sa ko suke masa magana, domin bajin su yi ba ba fahimtar su wanene yake yi ba.

Ga6o6i, zuciya da gangan jikin sa duk sun saki, tuno irin yadda da aminta da yayi da Sani fiye da ma mai gadin gidan sa, tuno irin yanda Jasmine ke yawan kawo masa 'karan Sani ne ya 'dan bashi 'karfin gwiwa ajikin sa.

Sani!
Ya sake maimaita sunan cikin zuciyar sa......lumshe idanu yayi ya kuma bu'de su a take sai hawaye ya gangaro masa.
'Daci yake jin na taso masa daga zuciyar sa ga harbi da takeyi da 'karfi gami da nawi da yake jin 'kirjin sa na yi masa, amma duk hakan basu dame shi ba kamar idan ya tuno wai Sani drivern gidan sa ne ya lalata masa rayuwar 'yar sa da bata 'karasa ma ciki 5years ba har yanzun.

Saurin goge hawayen nasa yayi cikin bawa kansa 'karfin gwiwa gami da juyawa ya koma baya zuwa male surgical ward tunowa da yayi cewa Sani na can....." i ll kill today Sani.....sai na kashe ka ta yadda bazaka sake samun daman illata 'ya'yan mutane ba".

Cikin zuciyar sa yake wannan maganar yana tafiya cikin hanzari.

Dr. Felix na 'ko'karin sake jefa ma Sani wata tambayar ne sai Sani ya dakatar da shi da fa'din " dan girman Allah likita ka cire min wannan abin....ina so inga Jas inga halin da take ciki....ban kyautawa....rayuwar ta da ta iyayen... ta ba".

Da 'kyar Sani yayi maganar cuz in ba ka kawo kunnan ta kusa da dashi ba bajin abinda ya fa'di zakayi ba.

Dr. Felix ma bai ji abinda ya fa'di ba.....kawai sai shi da kansa yaga dacewar cire masa abin zu'ko numfashi dake manne saman fuskar sa.

Kallo 'daya zaka yiwa Sani ka fahimci cewa cikin tsananin damuwa yake......har a lokacin kuwa bai daina hawaye ba, ana cire masa abin ya furta " Likita ina Jasmine take? Wani hali take ciki?
Allah yasa yarinyar mutane bata mutu ba sanadin abinda nayi mata?

Wannan karon Dr. Felix ya 'dan ji abinda Sani ya fa'di dan haka sanin da yayi cewa tare da 'yar Dr. Mu'een suka yi accident 'din ya sashi takaita tunanin sa kan cewa ita Sani ke tambaya.....cikin salon kwantar da hankali yace da shi " don't worry...tana lafiya, Dr. Safwan ya bata kulawa".

Rintse idanu Sani yayi hawaye na sake bin gefen fuskar sa.

Dr. Felix na sake shirin jefawa Sani tambaya akan nasa jikin ne sai idanun sa suka sau'ka kan Dr. Mu'een da ya bayyana daga bakin ward 'din tsaye cikin hali mai wuyan fassaruwa.

Idanun sa ka'dai zaka kalla kasan cewa ba a dai-dai yake ba.

Kallon Sani yake yi cikin tsananin tsana da haushin sa while Sani kam bai ma san yanayi ba domin idanun sa a rufe suke.

Dr. Felix da bai san asalin abinda ke faruwa ba lokacin da ya gansa yaga halin da yake ciki sai yayi saurin nufo inda yake tsayen domin shi zaton sa damuwar sa nada nasaba ne da jinyar su Sani, dan haka cikin tausaya wa halin da ya gansa a ciki ya nufo inda yake da nufin calming 'din sa.
Chapter 24 · 0% Book details