← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 211

Sashe 98

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin Mummyn Husnah ta 'dau zafi ne ya sanya shi fa'din" To Fateemah sai ki gaya min abinda ya dace inyi tunda ni banda hankalin kaina kinji?"
Sai tace
" Ai ba batun haka bane Alhaji, amma ai ya kamata ka duba lamarin kai da kanka, ko binciken kirki fa ba ka yi ba kawai ka 'dauki auren yarinya ka bayar bacin bakasan ko su 'din wasu irin mutane ba ne haka akeyi ne saboda Allah...?"

Shareta kawai yayi yayi kwanciyar sa yayi baccin yayin da Mummyn Husnah kuwa saboda tashin hankali ma kasa rintsawa tayi, zugum ta rafka uban tagumi, daren ranar ka'dai sai da ta tuna mahaifin Husnah yafi sau 'dari, cuz tasan shi din da wuya yayi mata hakan, koda yayi hakan ma to zai bita da kalamai masu da'di da kwantar da zuciya ne.

Gari na wayewa ta 'dauki wayar ta ta 'kira Husnah tace mata ko me takeyi maza ta bari ta zo gida aranar ba sai an kwana ba.

Jin yanayin da  Mummyn ta tayi maganar sai ya sa hankalin ta ya tashi sosai, kuka ta fara tana tambayar ta abinda ya faru, sai tace" Sai dai kin zo kawai..Allah ya tsare hanya".
Tana fa'din haka ta yanke 'kiran tare da zabga uban tagumi, wannan wace iriyar rayuwa ce fisabilillahi?"
Ta fa'di cikin ranta.

Alhaji na bayi tayi wayar lokacin da ya fito ya ganta da tagumi sai ya kauda kansa ya cigaba da abinda yake yi, dan yasan silar hakan.

Batare da ya dube ta ba yace" Wai ke Fateema kina tunanin kin fini son Husnah ne ko me? Ko kuwa ke aganin ki dan bana son ta ne yasa na yanke wannan hukuncin?"

Ko 'kala bata ce dashi ba dan takaici, kawai sai ma ta tashi tayi ficewar ta ta barshi a 'dakin..tana mitar" Wannan wace iryar tambaya ce haka..sai ana shirin cutar da rayuwar ka sannan za'a wani fake maka da soyayyar 'karya, bayaga haka ta yaya ma zai iya ha'da soyayyar da takewa Husnah da wadda yake mata, 'kilan ya manta cewa ita ka'dai ta sha wahalar na'kudar ta ta haifi abinta da taimakon ubangiji, shikuwa ganin ta yayi tar idanun ta a bude batare da yasha wahalar komai ba". sai ya ta6e bakin sa gefe.

Har kuwa ya gama shirin sa ya bar gidan kulashi ba..da yake ma ba kullum yake yin breakfast a gida ba shiyasa shima bai ko nema ba yayi ficewar sa.

Haka Mummyn Husnah ta yini ranar zuciyar ta cike da damuwa da tunani..har Husnah ta iso wajajen 'karfe biyu na ranar Mummyn ta bata warware ta saki ranta ba, gani take an dauko hanyar lalata rayuwar Husnah...ai gwamma ma Hisham 'din tunda shi duk lalaci tushen su 'daya kuma zai ga darajar ta matsayin kanwar shi koda kuwa sadakar ta aka bashi, akan wani can da bata san lungun da ya fito ba balle tasan halayen sa...ta ji bata son tarayyar Husnah da Hisham ne kawai dan taga Husnah na nuna kin amincewar ta ba wai dan ta tsane shi ba, yaro mai hankali da sanin ya kamata sam bai 'dauko ko 'kwara 'daya daga cikin halayen mahaifin sa ba..yaro nagartacce bata ma san me yasa Husnah 'kin amince masa ba.

Hankalin Husnah  a tashe ta iso gidan burin ta kawai taga ya mahaifiyar ta take ta kuma ji abinda ya same ta, sai data yi ido hu'du da ita kafin taji hankalin ta ya 'dan kwanta ganin garau cikin 'koshin lafiya tsaye bisa 'kafafun ta.

Amma duk da haka sai da ta saki kuka ta tafi da gudu ta rungume ta kamar wacce cewa tayi zata tafi ta barta.

Da 'kyar ta lallashe ta tayi shiru har ta je ta watsa ruwa taci abinci ta huta...zuciyar ta cike fal da tunanin dalilin da yasa mahaifiyar tan tayi kiran ta.

*****
'Bangaren Yah Deen kuwa har lokacin bai gama yanke hukuncin da yaka ta ya yanke kan rayuwar sun ba, ya dai sanar da ita cewa 'kanin mahaifin sa ne ta gansu tare sannan yana shakkan ranar da akace ya sake dawowa dan kawo masa ziyara musamman ta bazata irin wannan.

Ita kanta Husnah sai taji ta damu sosai har ta fara tunanin komawa cikin Hostel cuz da wani tozarci da abin kunyan ya faru gareka gwamma tun farko ka 'kuntatawa zuciyar ka kayi abinda ya dace kawai koda kuwa hakan zai saka ka cikin damuwa ne to yafi maka indai tsakanin ka da zuciya da gangan jikin ka ne.

Sannan tasan da kunya a ganta ace ta bi saurayi ta tare gidan sa dan tsananin son da take yi masa..shiyasa tuntuni ta fara tunanin mafita da zauna ta kwashi kunya abanza bacin bata ga ribar rayuwar da suke yi shi ba cuz har yau bai ta6a furta mata kalmar so ba, hira da itama sai lokacin da yayi ra'ayi yake mata, haka zasu kwana tare su tashi amma babu wata kalma mai da'di da take samu daga gare shi sai ranar da yayi niyyar sake mata fuska, in kinji ya kwantar da murya to yazo mata da bu'katar sa ne ita kanta tasani...amma duk da haka 'digo daga cikin son da take yi masa bai agu ba.

Tana nan ne dai tana tare da shi da tsammanin wataran zatayi nasara ya so har ya aure ta.

Koda ta ta sanar da shi zata je gida mahaifiyar ta ta'ki ra ta ma bai wani damu ba da yake dama tun tafiyar Uncle J maganar kirki bata shiga tsakanin su ba..kowa nada tashi damuwar 'kunshe cikin ransa.

Duk da yaga hankalin ta a tashe amma bai wani damu ba sai yayi tunanin ko family issues ne da yake cewa tayi zata je gida mahaifiyar tayi 'kiran ta, dan haka bai nemi jin dalilin tafiyar tata ba illah 5k da ya 'dauko ya bata da sunan ku'din mota...bai san cewa an bashi auren ta ba sam nasan da ko sisin sa ba zai bata ba.

*****
  Sai bayan kwana biyu da dawowar su Alhaji daga Azare sannan Uncle J ya sanar da shi cewa sunje sun tambaya masa aure a Azare kuma an bashi...bai fa'di gidan da suka je 'din ba haka ma sunan yarinyar duk bai fa'da masa ba..duk da lokacin da suka je yaji Alhaji Baba ya fa'di sunan ta Asma'u wanda shima yaji ne abakin Yusha'u da ya tura yi masa bincike da sunan mahaifinta da yake ba 6oyayyen mutun bane, kuma ita ka'dai ya mallaka kafin ya bar duniya shiyasa ma Yusha'u bai sha wahalar binciken ba.

Hakan ma da Uncle J ya samu ya sanar dashi da 'kyar ya ro'ki Alhaji ya amince akan asanar masan, dan da farko cewa yayi ba za'a gaya ma kowa ba ciki kuwa harda Ammin sa, wai har sai bayan an tsaida ranar 'daurin auren kafin a sanar musu.

Ranar kam in akwai sahun tashin hankali na 'karshe to shi Mu'een ya shiga, musamman ma da yaji wai a Azare aka tambayo auren, bai nemi 'karin bayani ba cuz ya san ba Rahma bace, dan ita tuni tayi auren ta harda 'yar ta, shi kenan ta tabbata shine mijin Husnah.

Bazan iya misalta muku yanayin yanda ya shiga ba kudai ku misalta da kanku ku gwada girman 6acin ransa akan aure tsakanin sa da Husnah, nasan ku kanku kunsan abin sam bazai yi masa da'di ba.

Tun daga ranar da yayi jifa da wayar sa bayan jin bayanin Uncle J bai sake bi ta kan wayar ba...bai ko sake tunanin 'kiran kowa ba dan yasan duk babu wanda zai iya dakatar da auren tunda har takaiga anje anyi tambaya...to wama zai 'kira?
Dam Alhaji ne ko Ammi kuma suma 'din a yanzu rashin jin su yafiye masa.

Allah sarki Ammi kuwa Allah ne ka'dai ya san halin da shiga da ta daina samun wayar sa domin sam bata san abinda yake faruwa ba har tausayi take bani, kwata-kwata na rasa wani irin so take yiwa wannan gagaren 'dan nata.

*To ina labarin Husnah?*
       mahaifiyar ta bata sanar da ita komai ba har sai da ta tabbatar da natsuwar ta that's washegarin zuwan ta, shima 'din sai bayan da suka idar da sallar Zuhr kafin ta sanar da ita cewa wan mahaifinta ya bada auren ta ga wasu mutane da suka zo daga Shuwarin...sai ta kasa tantancewa, shin Mu'een ne ko kuwa wani daban, dan ita sam bai ta6a nuna mata alamun a shirye yake da auren ta ba...ya akayi haka kuma?...duk da haka sai take jin 6oyayyen farin ciki cikin zuciyar ta gefe guda kuwa fargabar kar yakasance ba shi bane.

Taso ta same shi awaya ko zata damu jin asalin labarin daga bakin sa, amma layin baya tafiya ta gaza samun sa, duk yadda taso su gana abin ya faskara.

Haka ta yini neman layin sa amma bata samun sa hankalin ta duk sai ya tashi cuz tasan ba'a fiye rasa shi a waya ba, his phone is always on baya ta6a kashe wayar sa" To yau din meke faruwa kuma?
Ta tambayi kanta while tana sake dialling numbern but still is switch off.

Damuwar Husnah bai wani yi tsayi kan batun auren ba fiye da rashin samun sa da bata yi ba, dan hankalin ta gida biyu ya kasu, idan Mu'een aka bawa auren ta tasan zata dawwama ne cikin farin ciki musamman ma saboda irin dumbin soyayyar da take yi masa shiyasa ma ba ta damun ba, gefe guda kuma tana tunanin inba shi 'din aka bawa auren kuma fa?"
Wannan duk bai dame ta sosai ba kamar yadda ta bawa neman layin sa muhimmanci cuz tasan da ta same shi zata ji komai in yaso daga baya sai ta san me ya dace tayi kan batun.

Duk abinda take yi  mahaifiyar ta na lura da ita musamman da taga bata wani damu sosai da jin labarin ba sai tayi matu'kar mamaki, bata san haka Husnah zata 'dauki abin da sanyi ba, she thought zata 'daga hankalin ta ne idan taji labarin amma ga mamakin ta sai taga akasin haka.
Chapter 98 · 0% Book details