← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 211

Sashe 23

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da Noor ke faman hawaye da murmushi lokaci guda idanun ta kan Jasmin 'din hannun ta kuwa na gefen fuskar ta.

Ta 'dayan gefen bed 'din Deen ya koma ya ri'ke hannun ta yace " Jas 'din Daddy kin tashi?"

Jasmine sai ta 'dage kanta sama a hankali tana kallon shi daga kwancen.

" ina ke miki ciwo yanzu ?"
Ya sake tambayar ta da kulawa cikin sassanyar murya.

Shiru Jas tayi tana kallon fuskar shi batare da ta bashi amsar tambayar tasa ba.
A hankali ta maida idanun ta kan Safwan inda nan take ta 'dan tura baki a hankali ta bu'di tace " Daddy kaga Uncle Safwan yayi min allura ba? kuma ni ai lafiya na 'kalau Sani ne yace bashi da lafiya 'dazu".
Tana maganar cikin shagwa6ar ta da ta saba yi masa.

Murmushi Deen yayi inda ya da'da ran'kwafowa ha'di da kai hannun sa 'daya yana shafo kanta yace " kar ki damu kinji mamana, shima ai Sanin an yi mishi alluran har guda uku ma, yanzu ina ke miki ciwo?" Deen ya 'karasa maganar tasa da tambaya yana me cigaba da shafa kanta.

Jas sai tace
" Ciwo?"
Ta sake mai maita abinda ya fa'da 'din.

Shima sai yace " uhmm fa'da min inji ko mamana, kanki na ciwo ne?"

Jijjiga kai Jas tayi a hankali alamar ah ah
" cikin ki fa ?"
Ya sake tambayar ta.

Sai kuma tayi shiru tana 'kara turo baki.

Noor kam tagumi tayi tana binta da kallon jin da'di jin har tana yi musu hira, ashe da gaske ne da Yah Deen yace " nata ciwon da sau'ki ba kamar na Sani ba......hamdala kawai take ta zubawa mahallici.

Jas ne taci gaba da fa'din " ai 'kafana na min ciwo da 'dan 'dina..."
Tayi masa nuni da bandages 'din dake kanta.

" Ayyah....sorry baby kinji, soon zai warke insha Allahu".

Sake 6ata rai Jas tayi sosai sannan tace " Daddy!"

Deen ma sai yace " Na'am 'yar gidan Daddy ina jinki akayi ?"

" Ba sani bane ya cinye min bakina a mota ba kuma ya rufe min bakin da 'karfi har ina jin zafi....., banyi pupu ba a school kuma ko fitsari ma banyi ba amma ya min tsarki mai zafi......ni kam Daddy kace mishi bana so.......".

Wani dumm dukkan su suka ji tamkar sau'kan wani abu mai nawi a tsakar kawunan su, yayin da idanuwan Noor duk suka firfito waje ta zuba su akan Jasmine tana kallon ta.

Deen ma kansa tsura mata idanu yayi yana faman harha'da bayanan nata wuri guda domin so yake ya fahimci ma'anar su.

Inda karon farko tunanin sa ya basa a kan zancen nata da inda ya dosa gaba 'daya sai yaji wani bambabara'kwai kamar ba hakan bane........'dan jijjiga kansa yayi tare da fa'din " no ths can't be".
Still yana ri'ke da hannun Jasmine cikin nasa.

'Dagowa yayi ya kalli Noor da bakin ta ke faman 6ari tana son furta magana amma ta rasa me zata ce ma kwata-kwata, domin ita tashin farko batare da wani dogon nazari ba ta fahimci inda maganar ta dosa.

Mayafin da ke rufe
da jikin Jas ta kai hannu da sauri ta yaye shi sai taga gaban ta a kumbure ka'dan.

Sake shi tayi da sauri tare da zubewa da gwiwowin ta 'kasa ta 'kasa furta komai wani mahaukacin jiri ke 'diban ta yayin da maganganun Jas 'din ke sake yi mata yawo aka " ........banyi pupu ba kuma banyi fitsari ba amma ya min tsarki mai zafi....".
Kanta tayi saurin dafewa da dukka hannayen ta biyu, yayin da hawayen ta ge turereniya wurin ganin sau'ka, sosai jikin Dr. Safwan yayi sanyi amma babu yanda zai yi dole ne zai tabbatar musu da asalin gaskiya.

Bin ta Deen yayi da kallo sannan ya sake bin jikin Jasmine 'din ma gaba 'daya da idanun sa da suka gama dawowa jajazur.....shi kam 'kwa'kwalwar sa ma dum yake jin ta ya kasa koda yin nazari ne tsabar confusion.

'Daga kai yayi ya kalli Safwan dake tsaye tun 'dazun bai furta komai ba.

A 'dan rikice yace " Safwan me ke faruwa wai?"
Nuna Jas yayi da hannun sa yace " kasan me maganan Baby ke nufi Safwan?"

Kai ya Safwan ya jinjina masa alamar " ehh".

Deen sai ya sake fa'din " kenan dagaske Sani......."
Bai 'karasa ba Dr. Safwan ya amshe da fa'din ".......he try to rape her but Allah bai bashi nasara ba sai dai duk da haka ya ji mata ciwo ka'dan......ni kaina lokacin da aka ciro shi a motar nayi mamaki sosai domin belt 'din wandon sa a kunce sai dai banyi zargin wani abu ba a lokacin gaskiya duk da kuwa abin ya kulle min kaina.....duba Jasmine da nayi sai naga abinda akayi mata wanda sai a lokacin na tuno da bu'da'd'den belt 'din Sani da na gani......ha'ki'ka wani mummunan lamari ne ya so faruwa sai Allah ya takaita shi......
Na gama tabbatar wa ne lokacin da Jasmine ta farfa'do.....ita ce ta sanar dani duk abinda ya faru wanda take da masaniya akai........".

Noor bata kai ga jin 'karshen maganar tasa ba ta sanya aka ta kurma uban ihu kamar zautacciya tare da zama dirshan 'kasan tiles tana kuka, wanda cikin kukan take fa'din " ta tabbata kenan an lalata min rayuwar 'yata....Sani ka cuce ni Sani, Sani Allah ya isa tsakani na da kai.....ubangiji sai ya saka wa Baby zalincin nan da kayi mata....insha Allahu sai kaga sakayyar ka tun anan ba sai an mutu ba.....Allah ba zai barka ba Sani".

Deen kam na gama jin abinda Safwan ya fa'di sai ya sake waigawa yana kallon Jas dake tsiyayar da hawaye ganin mahaifiyar ta na kuka.....kallon sa ya mayar kan Noor dake ihun kuka Sannan ya 'dago ya kalli Safwan dake tsaye kusa da shi sai ya jijjiga kansa......suna ha'da idanu sai Safwan yace " kar ka 'daga hankali dan Allah Mu'een abin ba mai tsanani bane, inajin yatsa ya tura mata da karfi amma bai kai ga mummunan ku'durin nasa ba.....kaga Allah ya takaita....kuma da iznin sa komai zai zo da sau'ki".

Tsaye Deen ya mi'ke sai Safwan yace " Zo da Allah ka bawa Noor ha'kuri tayi shiru ko kuma ka 'dauke ta ku koma gida ku huta zanji da Jasmine karka damu please".

Deen bai ko waigo ba yaci gaba da tafiyar sa inda yake 'daga kafafun da 'kyar tamkar ana ri'ke masa 'kar'kashin takalmin da gum.

'Kirjin sa yake ji tamkar na aro ne aka bashi ba nasa ba, a hankali yake tafiyar kamar bazai yi ba dan sosai lamarin ya karya masa ga6a6o6in jiki gaba 'daya, ba'ki'kirin yake ganin gaban sa....sam baya ma fahimtar meke gaban sa dan tsananin ka'duwa amma a hakan ya cigaba da tafiyar dan gani yake tamkar haske zai baiyana masa a gaban sa...tamkar zaiji cewa wannan abin dayajin ba gaskiya ba ne....ba Jasmine 'din sa Sani yayiwa haka ba".

Noor dake ihun kuka tana sumbatu cak ta tsaya da kukan da take yi kamar wanda aka 'dauke mata wuta, tashi tayi da sauri ta tafi ta tari gaban sa ta tsaya tare da kama kunkumi da dukka hannayen ta biyu tamkar ba ita ce mai kukan yanzun ba, amma kallo 'daya zakayi mata ka fahimci tsananin 6acin rai dake tattare da ita.

Gaba 'daya idanun ta run rufe da 6acin rai...... abinda bata ta6a yi masa ba tsawon rayuwar ta amma ayau tana jin zata iya aikata masa fiye da zaton duk mai zato akan yarinyar ta.

Cike da 'karfin hali dakiya da kuma masifa tace " kagani ko?
Yah Deen Kaga result 'din mugun halin ka ko?"

Nuna Jas tayi da hannu tace " ai kaji da kunnan ka abinda tace Sani babban amintaccen ka yayi mata ko?
Me kuma zaka ce yanzun?
wani dama ce ta rage maka......wace dama ce ta rage maka ka bu'di baki ka bani amsa Yah Deen?"
Ta 'karashe cikin daka masa tsawa tamkar itace gaba da shi.

Rage sautin muryar ta tayi tace " Miye ban gaya maka ba Yah Deen?, miye ban sanar da kai game da Sani ba amma 'kememe ka'ki ka saurare ni, sai ma kake ganin tamkar kawai 'kiyayya ce nake yi masa, ban sani ba ashe bakin ku 'daya ne da shi, yanzu daya 'kwa'kule min yarinya kuma me zaka ce dani....miye laifin Jasmine...me ta tare muku a rayuwa dan Allah.....?
Kuka ne yaci 'karfin ta sai da ta 'dan yi kuka kafin na taja numfashi sannan taci gaba da fa'din
" wallahi har abada Yah Deen bazan ta6a yafe maka ba kai da Sani, kun cutar min da 'yata kun cuci yarinya ta kun cuci rayuwar ta....ha'k'kin ta ba zai ta6a barin ku ku sami farin ciki ba da izini Allah..".

Da yatsa ta sake nuna shi sannan ta cigaba da fa'din " kuma ka sani wallahi duk abinda ya sami yarinya ta kaine sila kuma sai na 'dau ka mata fansa a kanka.... ba zan yafe ma ba sai inda 'karfi na ya 'kare.....banza munafukai marasa tsoran Allah masu lalata 'ya'yan mutane babu gaira babu dalili........".

" Noor.......
Da Safwan ya fa'di ne ya sanya ta waigo wa ta kalle shi inda a masifance tace da shi " miye...?"
Cikin 'dacin rai.

Sam Safwan bai yi mamakin abinda take furtawa ba dan kuwa ya san fiye da hakan ma ba laifi ba ne matsayin ta ta uwa ga Jasmine da aka cutar, amma miye na 'dora lafin kacokam akan Mu'een kuma bayan shine mahaifin yarinyar, ai koma miye ne tasan shi ba zai ta6a bada gudummuwa wurin ganin an cutar da Jas 'din cuta mafi muni irin haka ba.

Saurin matsowa yayi kusa da ita cikin salon kwantar mata da hankali yace " haba Noor relax mana....mijinki ne fa kuma mahaifin Jasmine, ki sassauta mana......".

Deen kam tsaye yake tun 'dazun tamkar mutun mutumi, tun farkon fara maganar tata ya tsurawa bakin ta idanu, gani yake kawai bakin na motsi yayin da sautin muryar tata ke ratsa dukkan wani ga6o6i dake jone cikin jikin sa, har bibbiyu yake ganin ta amma sam bai da niyyan tanka ta.
Chapter 23 · 0% Book details