Sashe 162
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A labarin da Noor ta bata ta fahimci Nanne ce ka'dai wacce ya so ta so na gaskiya, so mai tsananin gaske, domin ya so ta ne da dukkan zuciyar sa da tunanin zai aure ta watarana dalilin ta ya tafi karatun likitanci, amma da yake Allah baya barin wani dan wani sai bai barta da ranta ba ya kar6i abin sa tun kafin Mu'een ya kai ga cika burikan sa akanta...daga ita bai 'kara jin soyayyar wata cikin ransa ba sai Noor da a yanzu take kyautata zaton yana yi mata soyayya mai masifar zafi, ga dukkan alamu yana tsananin so da 'kaunar ta a yanzun, domin sosai yake respecting feelings 'din sa ta 6angaren ta, duk wanda yake tare da shi dole sai ya fahimci game da shi kuma ma ko shi da kansa baya 6oyewa.
Amma idan tayi tunanin sai taga kamar gaskiyan Noor ne da tace Mu'een ba zai ta6a son ta ita ka'dai ba, cuz ko ni na kasa fahimtar dalilin da yasa ya kasa bibiyan wasu matan ya kasa barin mummunan halin sa duk da yake yana ikirarin Noor ka'dai ta ishe shi rayuwa, ako'ina baya 6oye tsananin soyayyar da yake yi mata?...
A hankali Hafsat ta 'dago kanta ta dube ta cike da tausayawa da sanyin murya tace" Kiyi ha'kuri Noor, dan Allah ki fawwalawa Allah komai, nasan babu da'di, dole akwai ciwo sosai, faruwar irin hakan yana da mugun 'kuna amma tawakkali shi zamu sanya cikin rayukan mu saboda Allah na ganin komai.
Ha'ki'ka Dr. bai kyauta ba, bai kyautawa ahalin sa dake 'kar'kashin inuwar sa ba, ya za6i son zuciyar sa ya manta da girman darajar da yake da ita, ya manta girman nasabar ba, ya manta cewa babban zunubi yake aikatawa 'karshe ya cutar da zuciyar ki mafi tsananin cutar wa...kiyi ha'kuri, kiyi ha'kuri Noor duk nima nasani ba'a kyuata miki ba amma kisani wannan ba shine cikakkiyar hujjar da ya kamata mu ri'ke bisa faruwar hakan ba balle har kice zaki tuhume shi da shi matsayin sa na uba mahaifi ga Jasmine, baki kyauta masa ba Noor, shi da kansa kinsan bazai ta6a son ganin faruwar hakan ga Baby ba.
Idan kinji cikin zuciyar ki cewa an miki ba dai-dai ba fine zaki iya barwa Allah ki jira ha'duwar mu a madaka ta ki 'kara ninka ha'kurin ki akan na baya wanda kika da'de kina aikatawa, da kaina ma na baki lambar yabo kan ha'kurin ki Noor, amma a yanzun har ga Allah bazan 6oye miki ba kin tsawwala masa da yawa, 'karamin misali ma ki duba kiga halin da ya shiga wallahi sosai Dr. ya bani tausayi yau ka'dai, da wanne kike so yaji? shima fa abinda ya faru ga Baby yaji ciwon sa sosai musamman idan kika yi duba da yanayin da aka fita da shi daga 'dakin nan, da kanki kinsan shima 'din abin ya ta6a shi ba sai an gaya miki ba..tunda kinsan Jasmine 'yar sa ce 'ya kuma mafi soyuwa cikin zuciyar sa...
Numfashi Hafsat taja dan ita kanta dauriya kawai take yi take neman kwantar da zuciyan Nuree ba wai dan tana goyon bayan Yah Deen ba, tana yin.hakan ne kawai dan sau'ke hakkin zamantakewa bai kamata ace ta bada nata gudunmawan wajen rushe musu farin cikin su ba...a hankali ta 'karasa maganar tata da fa'din" kuma kar ki manta fa Noor ko wani bawa yana da tashi 'kaddarar a zane, so me ze hana wannan in ma ki 'dauke shi a matsayin taki 'kaddarar?"
Wani kallo Noor ta jefe mata sannan ta kawar da kanta gefe" Hafsat kar kiyi tunanin zaki tursasa ni in yafewa Yah Deen koka'dan banji zan iya yafe masa ba, kuma batun yanda aka fita da shi wannan duk ba damuwa ta bace matsalar sa ce, inyaso daga yanzu ya ha'diyi zuciayr sa ya ha'kura da numfashin ma ba ta yanda hakan zai shafe ni, inda yasan hakan ai da ya jima da tuba ya daina abubuwan da yake aikatawa da har kike ni zan 'dauke alhakin zunuban sa matsayin 'kaddara, hakkin wa na shiga a rayuwa ta? In ma akwai akwai wata 'kaddara da zan 'dauka ai babu wacce ta wuce na auren Yah Deen da nayi a duniyan nan? In ma akwai ni banganta ba sam, kuma har abada bazan ta6a daina danganta abinda ya faru da baby da shi ba domin shine sanadi".
Tana fa'din hakan ta mi'ke cikin sanyin jiki ta nufi inda Baby take kwance...har a lokacin baccin ta take yi cikin kwanciyar hankali, yayin da Noor ke jin kanta tamkar zai zage biyu dauriya kawai take yi dayake tasan musabbabin sa a yanzu, burin ta bai wuce taga ta 'dauke 'yar ta daga garin Bauchi ba...wannan kawai shine Burin ta, taga ta nesanta Jasmine da Mu'een da duk wani abinda ya shafe shi.
Safwan dake tsaye bakin 'kofa ne yayi gyaran murya gami da yin sallama ya 'karaso ciki, shima 'din wajen Baby ya nufa kansa 'kasa yake sake maimaita kalaman da yaji Noor na furtawa da zuwan sa kenan yaji tana tana magana shine ya 'dan tsaya yaji.
Sosai yaji da'di da bai tarar da matar sa na zuga da sake aibanta Muceen a gaban ta ba, wanda ya tabbatar da ace wasu matan ne da sai sun fita za'kewa akan nuna rashin jin da'din su game da faruwar wannan lamarin.
Erh yasan cewa tana da daman da zata aikata duk yadda taga dama ko dan ta samu sassauci ma a zuciyar ta saboda an cutar da ita an ci zarafin ta a zahiri, amma kai da kake tare da ita bai kamata ace ka 'kara hura mata wutar abin ba koda kuwa kasan cewa itace da gaskiya a lamarin in bazaka taushe ta ba kawai yi shiru yafi.
Sam babu halacci cikin abinda akayi mata amma ya zama dole ka taushi zuciyar ta ko dan sau'ke hakkin zaman takewa ma.
Ganin ya nufi wurin Baby ne ya sa Hafsat ma tayi saurin tasowa, duba ta yayi sannan ya waigo gare su wanda har alokacin babu wanda yace uffan tsakanin su, sai da ya juyo garesun ne kafin yayi magana Hafsat ta riga shi da jefa masa tambayar" Ya jikin nata?"
Yace" Alhamdulillah ba laifi gaskiya".
Yayi maganar yana sake juyawa ya Kalli Baby.
Noor kam kallon sa kawai take yi tana so taji yace Babyn ta warke amma bata ji ya furta hakan ba.
Idanun sa kan Hafsat yace" Har yanzu baku rintsa ba dare yayi sosai fa".
Inda ya 'karasa maganar yana duba agogon dake 'daure a tsintsiyar
hannun sa.
Babu wanda yace da shi uffan a cikin su, sai ya 'dago ya maida kallon sa ga Noor cikin natsuwa yace" Madam kiyi ha'kuri fa dan Allah, ki sawa ranki cewar komai da ya faru ga bawa daga Allah ne, ki daina ganin kamar wai ko Mu'een shine sanadin hakan ta dalilin halayyar sa, ko kuma dalilin aminta da kuma yadda da yayi da drivern sa ne hakan ya faru duk ba wannan bane, duk mumini da kika gani idan mummunan abu ya faru da shi Allah ka'dai yake fara kawowa cikin ransa sanadin haka sai kiga ya samu damar furta kalmar _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ , dukkanin mu bayin Allah ne, ababen halitta ne mu, kuma bauta muka zo yi a duniyan nan, so kinga bamu fi 'karfin Allah ya jarrabe mu da duk abinda yayi niyya ba, ya kan iya 'daukan rai ma kuma dole a zauna ayi ha'kuri, Noor yanzu ina mahaifin ki?
kin isa kice me yasa Allah ya kar6i ransa ne?
Kin isa ki 'daurawa wani laifin barin sa duniya ne ko kuwa kin kasa rayuwa bayan bashi?
Me yasa?
Saboda ba ki da ikon yin hakan domin mutuwa da rayuwa duk daga Allah ne, lafiya da rashin sa ma duk nasa ne, amma me yasa kuma da ya gwada imanin ki ya jarrabe ki ta hanyar Baby sai kike jayayya kina nuna kamar imanin ki ya samu rauni Noor...yanzu inda ace Jasmine mutuwa tayi ta barki ya zakiyi? shima zaki ce Mu'een ne sanadi kenan?
Na sani cewa akwai abubuwa da dama da muke aikatawa marasa kyau kuma Allah ya 'kyale mu ya dube mu da su har 'karshen rayuwar mu, amma Noor kisani bayin Allah masu sa'a ne ka'dai Allah kan waiwaye su ya fahimtar da su laifikan su tun anan duniya yayi musu hukunci in anyi dace sai kiga mutun ya nutsu ya gyara rayuwar sa ya koma ga Allah kafin wa'adin rayuwa ta tsaya musu...wannan masu sa'a kenan, wasun koda wasa basa samun damar yin hakan, Allah baya basu daman shiriya har wa'adin su ya tsaya 'karshe suyi mummunan 'karshe abin Allah shi kyauta.
Dan haka ki gode Allah kawai Noor domin da rahamar sa ya dube ki ya dubi ahalin ki, kiyi tawassuli, ki kai kukan ki ga mahalicci, ki ro'ke shi da dukkan zuciyar ki inaga hakan ka'dai shine mafita, wanda 'kilan sanadin yadda da zakiyi da 'kaddarar da ta same kin sai kiga Allah ya sada ki da rahamar sa, amma yawan 'dorawa Mu'een laifin da kike yi sai kiga har ya jijjiga zaman imanin ki cikin rashin sani, domin zai zamane tamkar baki yadda cewa Allah buwayi bane kuma yanda yaso yake aikatawa ga bayin sa.
Dan Allah Noor kiyi ha'kuri, nasan da ciwo, da zafi da 'kuna kuma wallahi dukkan mu mun jishi cikin jikin mu, duk da nasan bazai kai naki ba matsayin ki na uwa dole ne ki fimu nuna damuwar ki amma ya zamuyi?
Fatan mu kawai shine Ubangiji Allah ya kiyaye mana gaba abinda ya faru kuma ya zame mana izna a gaba...akwai darasi babba da Allah ya 6oye kan hakan dan haka kiyi ha'kuri kinji? Ki kwantar da hankalin ki insha Allahu Baby zata samu sau'ki zata warke ta koma kamar baya ta rayu cikin farin ciki kamar kowacce yarinya".