Sashe 191
Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wata majalisa ya wuce ta samari wanda tun lokacin da ya doso su yaji sunyi tsit amma bai san dalili ba...da shigewar sa sai yaji sun fara musu a tsakanin su, dayake kowa na son a saurari nashi ne sai abin ya zame musu tamkar hayaniya, daga inda yake tafiyan ma har yana iya jiyo wasu daga cikin maganganun nasu.
Abinda kunnuwan sa suka fara jiyowa shine"... _Dallah can kai idan baka san abu ba kawai ka yiwa mutane shiru..."_
Wani yace" _Ya zaka ce haka bacin ni farin sani nayi masa, ai ko lokacin da cikin Ma'u ya bayyana ma kowa yasan shine ya aikata..._ "
" _Da wannan fa suke tafiya Imrana wanda kwanaki 'yan drugs suka kama innan..'yan iska ne na gaske...shima wannan in sa'a yaci da hadda shi za'a kama, yanzu ma haka ance 'yar wani babba yaje ya ta6o shine kuka ga ya dawo gida gudun kar a ka mashi_ ".
Wani daga cikin su yace" _Munafiki ai ni wallahi da nasan ko waye sai naje na tona masa asiri...banzaye 'yan iska marasa tsoron Allah kawai..kuma duk iyayen su ke 'daure musu gindi..._ ."
Daga haka ya rage jin abinda suke fa'di dan sun koma yi 'kasa-kasa ne.
Idanu ya rintse yana jin babu da'di cikin zuciyar sa, ko da ya bude idanun nasa ma dishi-dishi yake gani,fat-fat zuciyar sa ke bugawa da sauri, Allah wadai yake da rayuwar sa ta baya, ashe kowa yasan halin sa babu kyau, har ma gashi anan neman juya masa abin ta yadda ba haka bane, har mahaifan sa basu tsira kan harshen jama'a ba, da kansa da hankalin sa ya aikata abinda ya jawa iyayen sa zagi a gari, haushin kansa sosai yake ji yanzu, koma menene za'a fa'da yasan basu da laifi... yanayin fahimtar su suke bayyanawa...kuma da be bi mata ba da babu wanda ya isa ya dangana shi da hakan balle har a shigar da iyayen sa ciki...ji yake kamar ya koma ga samarin nan amma ya san zuwan nasa ba zai haifar da Alkhairi ba...Allah ka kaji 'kaina ka yafe min laifuka na."
Abinda yace ka'dai kenan yana me cigaba da tafiya har ya 'karasa lambu.
Ko daya tashi dawowa ranar kuwa bai dawo da wuri ba har Alhaji Baba ya baro shi a can, sai da ya yayi maghrib acan wurin sauran ma'aikatan kafin ya dawo gida gudun kar wasu su 'kara ganin sa su ma suyi maganar sa.
Tun daga ranar bai sake komawa lambu ba...haka kuma bai sanar da ko Ammi abinda ya faru ba.
Sai dai ya fita can harabar gidan ta baya wajen garden yayi zaman sa nan yana tunanin rayuwar sa, bai kwanta jinya ba kam amma a kullum rama ce ke saka shiga jikin sa saboda damuwa, idan yafar jin kirjin sa na ciwo sai ya dukufa shan magungunan sa har yaji dama-dama.
Sukan yi waya da su Ishaq Safwan da sauran su, Jiddah ce ka'dai baya 'daukan wayar ta, yayin da a kullun baya gajiya da 'kiran Uncle Ja'afar Anty Zainab da kuma Noorul Hudan sa, rashin ji daga garesun a kullum 'karamar jinya yake haifar masa mai shiga jiki.
Da kansa yasan ya yiwa rayuwar sa babbar illar da kowa zai ta ganin sa da shi.
Uncle J tuni ya sa numbern sa a divert yayin da Anty zainab kuma 'kiran ke shiga amma ko a kuskure bata ta6a 'dagawa ba...layin Noor kuwa kullum akashe yake samu abin na bashi haushi sosai...text marasa adadi yake tura musu Noor da Anty Zainab, duk da kullum layin Noor akashe amma baya gajiya da tura mata sa'ko...wani bin sai yaga kamar ko dagaske ne da Ammi tace da shi ta mutu kwanaki da kansa kuma sai ya girgiza kansa ya 'karyata batun sa sai ma ya 6ige da tunanin ai da ace ta mutu dagasken da bazasu sake 'daga batun saki tsakanin sa da ita ba, kuma ma yanda yasan Ammi ke ji da ita baiga alamar rasuwar ta tattare da ita ba...hakan yasan shima baya gajiya da tura mata sa'konni da tunanin ai wataran in da rai zata gani.
Tun bayan sakin da yayi mata Uncle Ja'afar ya tura su Malesia ita da Anty Zainab inda Noor zatayi karatun ta acan 2yrs programme ne dan haka babu batun dawowa, shine dai da kansa yake zuwa duba su idan ya samu lokaci.
Duk kuwa abin nan da ke faruwa Yah Deen bai ma san Noor bata Nigeria ba, ya dai san Anty Zainab na waje amma bai san cewa da Noor in sa suka tafi ba.
Anty Zainab kam 'kiran ne ka'dai bata 'dagawa amma ita ka'dai tasan yanda take jin tausayin sa a zuciyar ta, da ya 'kira ta sai ta tsaya har 'kaguwa take yi taga text in sa ya shigo cuz tasan a kullum bai gajiya da turawa.
Ita kam ba fushi take yi da shi ba dan tuntuni ta watsar da komai balle da taji labarin sakin da yayiwa Noor sai tausayin sa ya nunku mata a zuci, ko cikin text in da yake tura mata da kansa ya sanar da ita cewa ya saki Noor, tun yana yi mata text 'din ban ha'kuri har ya dawo gaya mata halin da yake ciki game da rashin matar sa, shi ne da kansa yake bata labarin komai idan ya faru da shi a ata'kaice...wani sa'in har kuka take 6uya tayi saboda tausayin Mu'een idan ya cika ta, abu 'daya ke hana ta 'daga 'kiran sa a yanzu dan gudun sa6awa Alhaji Baba maganar sa da kuma warning in Uncle Ja'afar, ta sani matu'kar kunnuwan ta suka yi arba da muryar Mu'een bazata juri ja masa rai akan Noor ba, da kanta zata fallasa komai saboda tausayin sa...kuma bata san me ze biyo bayana hakan ba shiyasa take tsoro.
Shima ya sani tana ganin text in sa dan haka sai yake tura mata da. Ya'kinin tana karantawa.
Wanda hakan ne kuwa, duk lokacin daya tura text in sai ta rufe layukanta ta rubuta masa reply dai-dai da abinda ya rubuta amma baya tafiya da yake layukan ta akashe sai ta ta tabbatar yayi error kafin take bu'de layin ta.
Duk wani text nasa dayake yi mata suna da reply awayar ta batare da ya sani ba.
Sosai Anty Zainab ke tausayin sa tana jin babu da'di da rashin sa.
Ko da wasa bata bari zancen sa ya shiga tsakanin ta Noor mai tsayi domin bazata juri gani da jin 'kiyayyar sa daga gareta ba.
Taka tsantsan take yi sosai akan hakan wani sa'in takan jajanta batun da Ammi idan ya dameta...yayin da Ammi ke ce da ita ta barshi kawai wannan ka'dan kenan daga sharrin aikata son zuciya.."
*****
Yah Deen duk ya zama wani abu daban, ya fita hayyacin sa, shiru-shiru ya zama na gaske.
Ko iyayen sa ma ba wani maganar kirki dake shiga tsakanin su daga gaisuwa shikenan.
In kinga wani uban gashi da ya tara akansa da fuskar sa abin har zai baki tsoro...yayi fayau ya rame siririn 'karfi da yaji ya zama...gashi duk Ammi ta san halin da yake ciki amma bata nuna damuwar ta akan sa.
Ko waya zatayi da Noor bata yi inda ta tabbatar zaiji..shi dai kawai bai ta6a ganin alamun kewar Noor tattare da ita ba.
Har su Saif sukayi hutu suka dawo gida, a lokacin dukkan su jikin su sanyi 'kalau yayi da ganin sa hakan da suka yi.
Saif sosai yaji tausayin 'dan uwan sa fiye da zaton mai karatu, Noor kuwa na can ta saki ranta bata da damuwar komai yanzu.
'Karfi da yaji ta yi 'ko'karin cire shi cikin zuciyar ta ta fuskanci sabuwar rayuwar ta da ke gaban ta gami da karatun da ta sa agaba...ta murje tayi 6ul-6ul da ita, kewar Ummah da Ammi kawai ke damun ta.
Comment
Vote
Share
*_Salmerh ce_* 😍
💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)
By
*Salmerh MD*
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *86*
Tun kafin zuwa su Saif akwai watarana ya shigo parlour sai ya ci karo da wayar Ammi na haske alamun shigowan 'kira while Ammi na kitchen bama ta sani ba.
ko daya ya 'dago wayar bai gane wanda yayi 'kiran *ba...Jewel* yaga an rubuta..yana ri'ke da wayar har 'kiran ya yanke yana tunanin inda Ammi ta sami me irin wannan sunan, wani 'kiran yaga ya sake shigowa, sai ya zauna yana duban wayar da tunanin waye haka...kuma bai yi tunanin mi'ka ma Ammi wayar ba sam.
Bai san meyasa ba kuma sai yaji zuciyar sa na bashi shawaran amsa 'kiran...haka kawai sai yaji yanan so yasan wace Jewel 'din kuma Ammi ta samo.
Kunnan sa yakai wayar yayi shiru yayin da daga 'dayan 6angaren ta sake dubanbwayar ganin.yau Ammi ta 'dauki 'kiran da tayi mata...bata bari ta 'kira ta kamar yadda ta saba mata ba.
Murmushi tayi ta ha'da wayar da kunnan ta, kamar a mafarki yajiyo muryar ta na fa'din" Ammi na har na fara tsoro tun 'dazun nake 'kira baki 'daga ba....".
Baya ya jingine bayan sa da jikin kujerar yana sake manne wayar da kunnan sa tare da folding hannun sa 'dayan bisa 'kirjin sa...shin da gaske itan ce ko kuwa kama ce ta muryoyi?.
Jin shiru Ammi batayi magana ba yasa ta fara cewa" Hello!..Hello Ammi!.."
Kamar zatayi kuka ta sake fa'din" Ammi baki ji na ne?"
Saurin gyara zaman yayi bayan tabbatar da cewa itan ce da yayi, da rawar murya ya furta" Nu..ree..!"
Goshi tayi saurin tattarewa jin wata murya ba ta Ammi ba...wayar ta cire ta duba waiko ba Ammin ta 'kira bane? ganin sunan Ammi yasa ta sake maida wayar kunnan ta...dai dai yana fa'din"...Ina kika shiga a duniyan nan Nuree?...kin san..."
Bata bari ta kai ga jin 'karshen maganar ta sa ba tayi saurin datse wayar ta ma kashe ta gaba 'daya.