← Book details Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 211

Sashe 49

Noorul Haske Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido Ammi ta lumshe gami da girgiza kanta gefe da gefe a hankali ta furta " _MU'EEN_ ".

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce* 😍

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *26*

Hannu na ta kama da alamar rarrashi take fa'din " sorry daina kukan i ll slap him too...zan rama miki marin ki bar ni da shi kinji?"

Kaina na 'daga sama alamar " to" sai ta sake fa'din " yauwa Hudah ta...."

Juyawa nayi na kama hanyar barin kitchen 'din da fa'din " zan je in yi shirin makaranta Ammi".

" To adawo lafiya" tace min gami da juyawa ta cigaba da aikin ta.

       Ranar ma ko gaida Alhaji Baba ban tuna nayi ba kawai na nufi hanyar da zata sada ni da barin parlourn batare da na sake kallon koda  inda suke ba daga shi har Zaid 'din gaba 'daya.

Bayan fitata ne Ammi ta zo ta 'karasa shishshirya musu abincin, inda anan take yiwa Mu'een da har a lokacin yake kishingi'de a wurin fa'dan mari na da yayi.

Murmushi yayi mata kana batare da damuwar komai ba yace mata" wai dan Allah Ammi ina kika samo wannan yarinyar da sassafe haka?"
" Ina ruwan ka".
Ammi tace da shi  sannan ta sake fa'din " ni dai kar ka kuskura ka sake dukan min 'ya bana so"!...sassafe yarinya bata karya da komai ba sai ta karya da mari....idan kai aka yiwa hakan zaka ji da'di ne?....shiyasa nake son 'yan biyu na wallahi cuz duk iya wasan da zasuyi agidan nan bazaka ta6a jin sunyi duka ba......"

      Rausayar da kansa yayi gefe ganin da gaske Ammi ke masifar an ta6a yarinyar da be san ta bai kuma san me take yi agidan da wannan safiyar ba.

         Taran masifar tata yayi da fa'din " kai Ammi na sorry...ni dai abani abinci inci....yunwa nake ji".
Ya 'karashe da yamutsa fuskar sa.

" Je yiwa Alhaji magana to...".
Cewar Ammi

Sai yace " na shiga gaida shi ma na tarar baya nan...ina ya tafi da wannan safiyar haka?".
Ya 'karashe mahanar tasa da tambaya.

           Kai Ammi ta dafe gami da fa'din " ups na manta ai, yaje wurin ta'aziya ne amma bazai da'de ba zai dawo".

Bai damu ba sai ma yasake fa'din
" Ni dai abani breakfast please Ammi"!

Murmushi Ammi tayi tare da jan kujera tana shirin zama tace da shi......" sai yarana sunzo tukunna"

       Mu'een sai ya 'dan ha'de fuska gami da fa'din " haba Ammi...ni 'din bare ne ba 'danki ba?, Allah zanyi fushi fa....".
" Zama ka sa'k'ko ai..."
Tace tare da juyawa ta kallo 6angaren da Zaid yake zaune  daga can tsakiyar parlour tace da shi....." Zaid 'kira 'dan uwan ka kuzo kuyi break.... time is running".

Mintina uku basu cika ba sai gasu sun fito atare, Saif already har yayi shirin sa yayin da Zaid bai shirya ba har yanzun.

     Da kallo Mu'een ya bisu dukkan su inda ya sau'ke idanun sa kan Zaid dake shirin zama yace da shi " me yasa baka yi shiri ba kai har yanzu".

Kallon sa Zaid yayi sannan ya bashi amsa da fa'din " Assignment nake yi ne Yayah shiyasa".
" Assignment kake yi ko kuma wasan banza, ba kaine na ganka kuna guje-guje ba 'dazun?"
Zaid cewa yayi
" Takkadda ta ta 'dauka min fa shine nabita in kar6a ba guje-guje muke yi ba".
'Dan neman sai ya sake fa'din
" me yasa kuma sai yanzu zakayi Assignment 'din...tun jiya me kake yi?"
"Mantawa nayi sai yau da asuba na tuna".

" Yayi maka kyau ai Zaidu dama ai kai bakajin....."
Ammi ce dake gefen sa ta take mai 'kafa wanda yasa shi dakatar da maganar yayi shiru tare da juyawa ya kalle ta da sauri.

Ammi kam tsaye ta mi'ke tana fa'din " ni ya isa haka masifar...ka barmin yara suyi abinda ke gaban su su wuce school...kai akwai wanda ya fika rashin ji ne?"
'Dan 6ata rai yayi yace
" Ammi ni kuma?"...da alamar tabbatarwa Ammi ta jinjina kai gami da fa'din " Ehh mana waye kuwa banda kai"....Ciki take murmushi dan tasan he may be angry.

Ai kuwa sai ya ha'de gira, sosai ya 6ata rai shi adole Ammi ta yarfa shi gaban 'kannan sa.
   Dalilin hakan ya ja baki yayi shiru...murmushi Ammi tayi a fili, haka ma Saif da tun 'dazun yake binsu da idanu, sai a lokacin kuma ya bu'di baki ya gaida shi.
A takaice ya amsa masa...batare da ya kalle shi ba...sai ma ya 'kara shan kunu. Saif be gaida Ammi ba a lokacin ga dukkan alamu ya riga ya gaida ta tun 'dazun.

Da yake Ammi ta riga ta san ra'ayin 'yan biyun ta sai tayi serving nasu ta tura musu gaban su gami da fa'din " oyah hurry up kar ayi late..."
Duk abinda take yi Deen na binta da idanu a kishingi'den da yake amma bazaka ta6a lura da hakan tashin farko ba.

        Tana gama sallaman su Saif sai  ta dawo da kallon ta kan Mu'een tace da shi " me zaka ci?"

Kunun da yaga ta zubawa Saif ya nuna mata da hannu sai ta zuba masa shima...." sai kuma me?"
Ta sake tambayar sa.
A hankali yace " ya ishe ni ma wannan 'din".
" owk tace gami da tura mai roban sugar gaban sa.

Sosai yaji da'din kunun ya kuwa shanye duk wanda Ammi ta saka masa, 'dan fushin da yayi ne ya hana shi bu'dan baki ya yaba mata a zahiri.....amma 100% yaji yayi masa.

         Daga shi kuwa be 'kara cin komai ba ya tashi ya bar table 'din.
                 Suma su Saif na kammala break fast 'din sai suka hanzarta 'karasa shirin su suka wuce makaranta.

   Koda Alhaji Baba ya dawo bai same su agida ba da yake sai kusan 'karfe tara ya dawo gidan so a lokaci, sun da'de ma a makaranta.

      A harabar gida ya ha'du da Mu'een sai suka dawo ciki tare suna 'dan ta6a hira.

       Anan Alhaji Baba ke fa'din " ai da har zan tashe ka muje ta'aziyar tare amma danaga kamar baccin gajiya kake yi kawai shiyasa na barka nai tafiya ta".

Mu'een kam cikin ransa yace " ai gara hakan ma".
Afili kuwa murmushi yayiwa Alhajin sannan yace " Ai kuwa gara ma da baka tashe nin ba...mafarki nake yi ina gaban ka'abah, daka tashe ni da har sai nayi kuka".

" Lalle yau ka kai babbar ziyara".
Fa'din Alhaji Baba yana dariya.
Mu'een sai yace " wallahi kuwa, dan ma naji haushi hannu na bai 'karasa ta6awa ba na farka".

" Allah ya sa mu dace to".

" Amin Amin"
Ya amsawa Alhajin da shi.
Haka suka cigaba da 'dan hira har lokacin da Ammi ta gabatar masa da abin karin sa, batare da 6ata lokaci ba ya karya sannan yayi shirin tafiya gidan gonar sa.
Har ya kama hanya zai fita sai kuma ya juyo ga Mu'een yace da shi" ko zamu tafi tare ne, naga gidan shiru kar kuma ka gaji da zama kai ka'dai 'din babu da'di".

" ah ah Alhaji...ni kam ba yau ba sai dai gobe in Allah ya kaimu".

" to shikenan Allah ya nuna mana goben ni kam na wuce".
Fa'din Alhaji Baba tare da juyawa ya fara tafiya
" Allah ya bada sa'a " Ammi tace yayin da Mu'een yace da shi " adawo lafiya".

Ko bayan fitar Alhaji Baban ma bai bar parlourn ba zama yayi suka cigaba da hirar su da Ammi.
   Ya kanji farin ciki sosai a duk lokacin da yaga yanda rayuwar ahalin sa ya kasance a yanzun gaskiya sai dai Alhamdulillah kawai za'ace, domin bai ga alamun suna tare da damuwar komai ba...gashi Allah ya 'kara bu'da musu gidan gona sai ha66aka takeyi.

   Shima 'din ya kanji farin ciki ta 6angaren sa marar misaltuwa, domin kuwa har mantawa yake da damuwar dake cikin ransa.

Kwanan sa 'daya ne tak amma Alhamdulillah cuz bai samu lokaci ya zauna dan tunani kan abinda ke damun sa abaya ba, hakan kuwa yayi masa da'di sosai, shiyasa 'karfi da yaji yake 'ko'karin maida kansa surutacce na dole ba wai dan hakan ra'ayin sa bane, face dan kawai ya ringa 'dauke hankalin zuciyar sa daga damuwar data ke 'kunshe da shi.
     Wannan kenan.

*****
     " Ummah kinga Hudah ta'ki tayi da sauri ko?"
Cewar Nanne dake ta faman ha'de fuska tamkar zatayi kuka.

" me ya faru ne Nanne me Hudahn tayi miki?"
Ummah ta tambaye ta tana mai tattaro dukkan hankalin ta gareta.
Nanne sai tace
" Tun 'dazu fa nake ta cewa tayi sauri tayi wanka ta shirya amma ta 'ki kuma fa tun 'dazu akayi azahar har an kusa yin la'asar ma,malamin mu kuma bulala zai mana idan mukayi latti".

Kafin Ummah tayi magana sai nayi saurin le'kowa nace " Nifa Ummah yau bazani ba gaskiya, tayi tafiyar ta kawai".
Ummah 6angaren da nake ta maida idanun ta sannan tace dani " me yasa bazaki ba Hudah ba fa na san shiririta ni"
Ummah tayi maganar da 'dan masifa harda da nuno ni da yatsa.

Ni kuwa baki na na  turo gaba sannan nayi komawa ta ciki batare da na 'kara fa'din komai ba.

Daga wajen Ummah ta sassauta murya gami da fa'din " kinga uwata yi tafiyar ki, wannan ja'irar ba zuwa zatayi ba nasani tunda har ta fadi da bakinta kuma ma ai kinga bata shirya ba har yanzu...tafi abinki Allah ya bada sa'a, banda wasan banza kinj uwata?"
Chapter 49 · 0% Book details